Ticker

6/recent/ticker-posts

Daudu

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Daudu

 

 G/ Waƙa: Na Audu,

: Kai ka aje gero da yawa,

: Ƙanen Basulluɓe Ila.

 

  Jagora: Na Audu,

: Kai ka aje gero da yawa,

: Ƙanen Basulluɓe Ila.

‘Y/Amshi: Na Audu,

: Kai ka aje gero da yawa,

: Ƙanen Basulluɓe Ila.

  Jagora: Mai zwarin wuri ƙanen Mugu,

 ‘Y/ Amshi: Tahi gonakka,

: Kar ka dawo said a duhu,

: Na Audu,

: Kai ka aje gero da yawa,

: Ƙanen Basulluɓe Ila.

 

Jagora: Abu ukku yab bani

 ‘Y/Amshi: Ba sauran magana,

 

Jagora: Abu ukku yab bani.

 ‘Y/Amshi: Yau ya kyauta kiɗi,

: Na Audu,

: Kai ka aje gero da yawa,

: Ƙanen Basulluɓe Ila.

 

  Jagora: Mai zwarin[1] wuri ƙanen Mugu,x2

‘Y/ Amshi: Tahi gonakka,

: Kar ka dawo sai da duhu,x2

: Ƙanen Basulluɓe Ila.

: Na Audu,

: Kai ka aje gero da yawa,

 

  Jagora: Ƙwairo ban zuwa gidan,

: Ƙan-ƙan-ƙan,

: Ƙwanƙiro[2] mai batun ƙwange hannu,x2

‘Y/Amshi: Ibak kwabonka sai an taka ƙaya,

: Ƙanen Basulluɓe Ila.

: Na Audu,

: Kai ka aje gero da yawa,x2

Jagora: Ga ni na shigo Damaga,

  ‘Y/Amshi: Ga goran batu ɗan yaɗa,

: Ɗanƙwairo na Audu,

: Mai kwana magana,

: Ƙanen Basulluɓe Ila.

: Na Audu,

: Kai ka aje gero da yawa,

 

 Jagora: Kura goma ga tareni goma,

: An aje inda babbassu,

‘Y/Amshi: Kura goma sunka zo baƙunci,

 

 Jagora: Kura goma sunka zo baƙunci,.

 ‘Y/ Amshi: Anka ba su tareni goma,

: Anka aje inda babbassu,

: ‘Yan yaya na raba daidai,

: Don kar a je a jawo man Magana.

: Ƙanen Basulluɓe Ila.

: Na Audu,

: Kai ka aje gero da yawa,

 

Jagora: Kura goma sunka zo baƙunci,

: Sai anka bas u tareni goma,

‘Y/ Amshi: An aje inda babbassu.

: ‘Yan yara sai ku koma dan nesa,

: Sai sunka koma daƙ ƙauye,

: Tak kirayi kura guda,

: Tab bat a tareni guda.

: Tac ce masu ku nawa kuke?x2

: Ta ce mata mu tara muke,x2

 

  Jagora: Yanzu ga tareni guda,

: Sun ce game da shi,

: Mu goma muke.

 ‘Y/Amshi: Ya ce noma na da lada.

 

  Jagora: Ta ce ga tareni[3] guda,

‘Y/Amshi: Sun ce game da shi, .

: Mu goma muke.

: Ƙanen Basulluɓe Ila.

: Na Audu,

: Kai ka aje gero da yawa,

 

  Jagora: Mai zwarin wuri ƙanen Mugu,x2

‘Y/ Amshi: Tahi gonakka,

: Kar ka dawo sai da duhu[4],x2

: Ƙanen Basulluɓe Ila.

: Na Audu,

: Kai ka aje gero da yawa,

 

  Jagora: Ga ni na shigo Damaga,

‘Y/Amshi: Ga goran batu ɗan yaɗa,

: Ɗanƙwairo na Audu,

: Mai kwana magana,

: Ƙanen Basulluɓe Ila.

: Na Audu,

: Kai ka aje gero da yawa,



[1]  Haɗama.

[2]  Marowaci/ wanda bai son ya rabu da abinsa/ mai ƙwange hannunsa.

[3]  Wata dabba wadda aka feɗe aka banƙare aka gashe musamman ragon layya ana kiransu da suna aSakkwato tareni.

[4]  Idan dare ya yi.

Post a Comment

0 Comments