Ticker

Fatan Alheri

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Fatan Alheri

Fatan alheri shi ne yi wa mutum kalamai masu ƙunshe da addu’ar samun biyan bukatocinsa da yake fatar samu tare da haɗawa da wasu muradan rayuwa da mutum ke son ya gani da saduwa da abubuwa masu kyawo da kowa ke son samu. Akwai irin wannan jigo a cikin waƙoƙin da mabarata ke rerawa a lokacin da suke yin bara. Suna yin haka ne domin daɗaɗa zuciyar waɗanda suke yi wa bara haka ya sa su ji daɗin ba su sadaka. Rubutattun waƙoƙin da ba don baran aka shirya su ba, sai dai don wata manufa ta daban ba a samun irin wannan a cikinsu. Duk da haka, mabarata kan ƙara fatan alherin a cikinsu idan suna bara da su. Misali:

 Iya kalin-kalin-kalin,

 Iya kalin na malamai,

 Iya komi kike biɗa,

 Iya Allah na ba ki shi,

 Ki sami farin ɗa,

 Abu mahaddaci,

 Ya haddaci sittin,

 Ya san sunnoni,

 Ya sami hankuri,

 Hankuri na duniya,

 Wanda kowa yake biɗa.

 (Iya Kalin-kalin)

Wannan wata waƙar bara ce da almajirai ke amfani da ita wajen bara. A cikin waƙar mabaracin na nuna fatar alheari ga matar da yake yi wa bara. Babban fatar alheri ga matar aure bai wuce ta sami haihuwa ba, kuma ƙari ga haka abin da za ta haifa ya zama ɗa namiji. Kowa ya san yadda mutane ke kallon ɗa namiji da daraja ba sai al’ummar Hausawa ba, domin an ɗauka shi ne magajin gida saɓanin mace da za ta yi aure ta koma wani gida. Haka kuma, ɗan da yake fatar matar ta haifa ya kasance mai kyawon hali kuma masanin Ƙur’ani ne, ilmin da kowane Musulmi ke kwaɗayin samu. Duk wannan zai samu ne bayan ta sami duk wani abu da take nema daga wurin Allah. Haka kuma cewa ‘Allah zai ba ki shi’ kamar wani tabbaci ne.

Post a Comment

0 Comments