Gaishe ku Manoman Arewa

     Citation: Bungudu, H. U. (2023). ZaÉ“aÉ“É“un waÆ™oÆ™in mawaÆ™an baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bungudu
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Noma

    Gaishe ku Manoman Arewa

    Wannan waÆ™ar ba wani mutun ya yiwa ita ba sai dai jama’a ya yi wa waÆ™ar saboda noman da suke yi. Dubi yadda yak eta cewa a cikin waÆ™ar:

     G/WaÆ™a: A gaishe ku manoman Arewa.

     

     Jagora: Gaishe ku manoman Arewa.

    . ‘Y/ Amshi: A gaishe ku manoman Arewa.

     

     Jagora: A gaishe ku manoman Arewa.

     ‘Y/ Amshi: A gaishe ku manoman Arewa.

     

     Jagora: A gaishe ku manoman Æ™asammu.

    : A gaishe ku manoman Arewa.

     ‘Y/ Amshi: A gaishe ku manoman Arewa.

     

    Jagora: A gaishe ku manoman jihammu

    : A gaishe ku manoman Arewa.

     ‘Y/ Amshi: A gaishe ku manoman Arewa.

     

    Jagora: Mu dai ‘yan lardin Arewa.

    : Mu dai bakin ƙasar Arewa,

    : Kowace sana’a mun iya ta,

    : Amma fa manoma ne mu ma,

    : A gaishe ku manoman Arewa.

      ‘Y/ Amshi: A gaishe ku manoman Arewa.

     

     Jagora: Idan ka ga mutum ya yi zaune,

    : Babbar riga[1] tana wuyanai,

    : Babbar taguwa tana wuyanai

    : Babban wando yana ƙafatai,

    : Sai ya zama babban manomi.

      ‘Y/ Amshi: A gaishe ku manoman Arewa.

     

     Jagora: Na zaga Æ™auyukan Arewa,

    : In nag a mutun ya yi biki,

    : Ya sa riga ya sa wando,

    : Babbar riga tana wuyanai,

    : Ga agogo yana hannunai,

    : Ga gilashi yana idonai,

    : Ga doki É—andubu yah au,

    : To ya zama babban manomi.

     ‘Y/ Amshi: A gaishe ku manoman Arewa.

     

     Jagora: Han nai sha’awa, na yi zaune,

    : Sai na zama babban manomi.

      ‘Y/ Amshi: A gaishe ku manoman Arewa.

     

     Jagora: A gaishe ku manoma na birni,

    : A gaishe ku manoma na ƙauye,

    : Da kowane manomin Arewa.

     ‘Y/ Amshi: A gaishe ku manoman Arewa.

     

     Jagora: Idan na shiga roÆ™on manoma,

    : Ni hau wani daÉ—i nike ji,

    : Noma shiga Dodon Arewa.

      ‘Y/ Amshi: A gaishe ku manoman Arewa.

     

    3.1.4  Gonar Jori

    Ita kuma wannan waÆ™ar Shata gona ce ya waÆ™e, wato gonar Jori Hammani tsohon shugaban Æ™asar Nijer. Ba kaitsaye mai gonar ne ya yi wa waÆ™ar ba, a a, ya dubi yadda gonar take ne domin ya sanar da jama’ar irin yadda ta Æ™ayatar da shi.

     

     

    Ga yadda waƙar take kamar haka:

     

     G/WaÆ™a: Kowaj je Yamai yai kallo,

    : Wannan bai kamar Shata ba.

    Jagora: Kowaj je Yamai yai kallo,

    : Wannan bai kamar Shata ba.

     ‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

    :Wannan bai kamar Shata ba.

     

    Jagora: Kowaj je Yamai yai kallo,

    : Wannan bai kamar Shata ba,

    : Zaman an kai ni gonar Jori.

     ‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

    : Wannan bai kamar Shata ba.

     

    Jagora: Waje É—aya ga wurin yin[2] gero,

    : Waje É—aya ga wurin yin dawa,

    : Waje É—aya ga wurin alkama nan,

    : Waje É—aya ga wurin shinkafa,

    : Ni an kai ni gonaj Jori.

    ‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

    : Wannan bai kamar Shata ba.

     

    Jagora: A nan kuma ga tumaki,

    : Ta nan kuma na ga shanu

    : Ta nan kuma ga dawaki hertat,

    : Kana na ga garken É“auna,

    : Sadda na taka gonaj Jori.

     ‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

    : Wannan bai kamar Shata ba.

     

    Jagora: Gabas da Arewa gandun sarki,x2

    : Gusun hay Yamma gandun sarki,

    : Ama ka tashi gonaj Jori.

     ‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

    : Wannan bai kamar Shata ba.

     

    Jagora: Afirika duk cikar faÉ—inta,

    : Gona dai mutum zai shirya,

    : Bat a kai ga gonar Jori.

     ‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

    : Wannan bai kamar Shata ba.

     

    Jagora: Zaman an kai ni bakin gona,

    : Na duba Gabas ba iyaka,

    : Na yi Arewa nan ba iyaka,

    : Nai nan Yammaci ba iyaka,

    : Na duba Kudu ba iyaka,

    : Na abu abin mamaki,

    : Don na taka gonaj Jori,

    ‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

    : Wannan bai kamar Shata ba.

     

    Jagora: Ni na je Yamai na ji daÉ—i,

    : Ni na je Yamai nai kallo,

    : Bayan na ga Jori da Aisha,

    : Har aka kai ni gona kallo.

    ‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

    : Wannan bai kamar Shata ba.

     

    Jagora: Ga kwakwa ta ci an shuka,

    : Ga kwakwa ta manja jere,

    : Ga ayaba abarba jere,

    : Ga kwakwa abar kallo nai,

    : Ni an kai ni gona kallo.

    ‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

    : Wannan bai kamar Shata ba.

    Jagora: Nan kuma rijiyar kifi ne,

    : Kai kallonka Shata ka zo

      ‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

    : Wannan bai kamar Shata ba.

     

    Jagora: Ga inibi abincin Turai,

    : In an kai ka gonaj Jori.

    ‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

    : Wannan bai kamar Shata ba.

     

    Jagora: Kai komi kake so ga shi,

    : Komi kai tunani ga shi,

    : Rannan na gano mamaki,

    : In an kai ni gonar Jori.

    ‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

    : Wannan bai kamar Shata ba.

     

    Jagora: Na gode wa sarkin baƙi

    : Isah Bube sarkin baƙi,

    : Shi ya kai ni gona kallo.

    ‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

    : Wannan bai kamar Shata ba.

     

    Jagora: Ka ji kiÉ—in manoma mun yi,x2

    : In an kai mu gonaj Jori.

     ‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

    : Wannan bai kamar Shata ba.

     

    Jagora: Shi kuma Jori É—an Hammani,

    : Bayan shugabancin ƙasa duka,

    : Ni na ba ka sarkin noma.

    ‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

    : Wannan bai kamar Shata ba.

     

    Jagora: Kai da dai aka kai ni gonaj Jori,

    : Nad duƙa abin da nike so,

    : Nis same shi gona gashi,

    : Na yi kirari, nai addu’a duk,

    : Bayan shugabanci ƙasa duka,

    : Han na bashi sarkin noma.

    ‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

    : Wannan bai kamar Shata ba.

     

    Jagora: Shi ke shugabancin ƙasa duka

    : Ni kuma na yi sarkin noma,

    : Shi nak kai wa sarkin noma.

    ‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

    : Wannan bai kamar Shata ba.

     

    Jagora: Afirika duk cikat ta da faÉ—i,

    : Wadda idan ka duba kwata[3],

    : Gonatai a duba a gan ta,

    : Ba mai tsere gonaj Jori.

    ‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

    : Wannan bai kamar Shata ba.



    [1]  Malummalum.

    [2]  Wurin da ake shuka.

    [3]  BakiÉ—aya.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.