Garba Abin Azawa Ga Gona

    Citation: BunguÉ—u, U.H. (2022). WaÆ™oÆ™in Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Amali  Sububu

    Garba Abin Azawa Ga Gona

    A Gidan Rijiya Garba yake Shi ne sarkin fawa garin ne, amma kuma manomi ne sosai yana noma yana samun abin aiki sosai. Amali ya yi masa waƙar noma don ya ƙara sa masa ƙaimi.

     

        G/WaÆ™a : Abin azawa ga gona,

    : ÆŠan Barmo.

      : Yi gabcen Jigawa.

     

         Jagora: Garba abin kwahewa[1],

    : Ga gonaa sai sahe,

      : Yi gabce ka samo.

    ‘Y/Amshi: Abin azawa ga gona,

    : ÆŠan Barmo.

      : Yi gabcen Jigawa.

           

    Jagora:  Za ni ga Garba mai kai ni wajje,

    ‘Y/Amshi: Yau  Za ni ga Garba mai kai ni wajje.

     

         Jagora:  Za ni ga Garba in sha gaba É—ai.

    ‘Y/Amshi: Yau  Za ni ga Garba in sha gaba É—ai.

      : Abin azawa ga gona ÆŠan Barmo.

      : Yi gabcen Jigawa.

     

    Jagora: Na gode ma ran ‘Yam magaji x2

     ‘Y/Amshi: Ba canjin sule tab biÉ—a ba.

      : Abin azawa ga gona ÆŠan Barmo.

      : Yi gabcen Jigawa.

     

    Jagora: Don Allah ka cetan ga gulbi Garba.

      : Don Allah ka hisshe ni wajje.

    ‘Y/Amshi: Abin azawa ga gona ÆŠan Barmo.

      : Yi gabcen Jigawa.

     

    Jagora  :  Za ni ga Garba mai kai ni wajje[2],

    ‘Y/Amshi:  Za ni ga Garba in sha gaba-É—ai.

    : Abin azawa ga gona,

    : ÆŠan Barmo.

      : Yi gabcen Jigawa.

     

    Jagora  : Garba abin kwahewa ga gona,

    : Sai sahe,

      : Yi gabcen jigawa.

    ‘Y/Amshi: Abin azawa ga gona,

    : ÆŠan Barmo.

      : Yi gabcen Jigawa.x2



    [1]  Aza abu ya zauna daram.

    [2]  Ƙarshen gona/biya masa buÆ™ata. 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.