Ticker

Garba Bai san wuyag gargare ba

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Garba Bai san wuyag gargare ba

Garba Bai san wuyag gargare ba mutumen garin Kalgo ne ta cikin yankin Sabonbirni. Yana noma ƙwarai da gaske kuma ya sami rufin asirinsa ta hanyar noma, Amali ya yi masa waƙar noma ne domin irin faɗi-tashinsa a harkar noma.

 

G/Waƙa : Bai san wuyag gargare ba,

: Ga Garba can za mu jiɗa[1],

: Namijin da noma ka wa haske.

 

Jagora  : Allah ka bar man masoyana.

‘Y/Amshi: Ya Allah ka bar muna mijin

: daga,

: Bai san wuyag gargare ba,

: Ga Garba can za mu jiɗa,

: Namijin da noma ka wa haske,

 

Jagora: Sannu da lubta[2] kalme ga yashi,

  ‘Y/Amshi: Sannu da assako[3] ɓurgujen laka.

  : Bai san wuyag gargare ba,

: Ga Garba can za mu jiɗa,

: Namijin da noma ka wa haske,

 

Jagora  : Sannu da jehwa kalme ga turɗa[4]

‘Y/Amshi: Sannu da assako ɓurgujen laka

 

Jagora  : Na gode Allah da Annabi,

   : Na gode girman manoma,

   : In na yi taggo da riga,

   : Albarkacin masu kafce,

   : In ka ga ƙube ga kaina,

   : Albarkacin masu huɗa,

   : In na yi zoben azuhwa,

   : Albarkacin masu ƙwazo,

   : In na yi mata na wari,

   : Albarkacin masu kaibe

   : Na gode Allah da Annabi,

   : Na gode girman manoma,

‘Y/Amshi: Ba mu rena girman manoma ba,

   : Bai san wuyag gargare ba,

: Ga Garba can za mu jiɗa,

: Namijin da noma ka wa haske.

 

  Jagora  : Kui aniya ku saba da kafce,

   : Kun san biɗa ba ta ƙin ku,

   : In ka ga yaro da wandon yadi,

   : Da taggo[5] da riga,

: Hak kag ga ƙube ga kainai,

   : Ka tabbata ya yi kafce,

   : Ka san ba ya samun su kyauta.

 ‘Y/Amshi: Allah baya yin wane kan banza.

   : Bai damu yin gargare ba,

: Ga Garba can za mu jiɗa,

: Namijin da noma ka wa haske.

 

Jagora  : Kui aniya ku saba da ƙwazo,

   : Kun san biɗa bata ƙin ku,

   : In ka ga yaro da mata tcadadda,

   : Tana runguma tai,

   : Hannunta na lalaba tai,

: Ya yi baƙi ƙirin da baƙin lalle.

: Abu dai kamaz zai karewa,

: Allan ko baran bai karewa,

: Nonnonta na inguza tai,

: Ka tabbatar ya yi gabce,

: Ka san ba ta iske shi kyauta,

‘Y/Amshi: Sai an sha wuya za a shan daɗi.

   : Bai san wuyag gargare ba,

: Ga Garba can za mu jiɗa,

: Namijin da noma ka wa haske.

 

Jagora  : Sai an sha wuya za a shan daɗi,

: Ka san,

  ‘Y/Amshi: Sai an sha wuya za a shan daɗi.

   : Bai san wuyag gargare ba,

: Ga Garba can za mu jiɗa,

: Namijin da noma ka wa haske.

    

Jagora: Ni niz zo gida ni ishe shi,

   : Nik ko taho lahiya lau,

   : Nik ko iso lahiya lau,

   : Nig ganai lahiya lau,

   : Shi yag ganan lahiya lau,

   : Yab bani taggo da riga,

   : Gami da ƙube da wando,

   : Gami da dokin hawowa,

: Gami da kuɗɗi tamanin,

: Ni godiya ɗai nikai mai,

: Kuma shi godiya ɗai shi kai,

: Kuma had da hwata[6] shinai man,

: Wada kat taho lahiya lau,

: Ka zo gida lahiya lau,

: Don albarkacin mai iyawa,

: Sarkin nan da yab busa sheɗa[7],

: Don albarkacin Annabi nai,

   : Don darajjar Abu mai riƙonmu,

: Garba naukku sarkin Musulmi,

‘Y/Amshi: ‘Yan amin ku amsa muna hwata.

   : Bai san wuyag gargare ba,

: Ga Garba can za mu jiɗa,

: Namijin da noma ka wa haske.

 

Jagora: Bankwana yana bani tausai,

: Da sunka zo rakkiya ta,

   : Nid dibi jamin mutane,

   :  Za ni rabo da huskam masoyana,

   : Sai zucciya taj jiye man,

   : Ka san ba ƙashi ag gare ta ba,

   : Sai niɗ ɗora ƙyallin hawaye,

   : Sai wataran da ku masu so na,

   : Ko mu game da ku masu so na,

   : Ko ko dai ya zan ba gamewa,

   : Saboda ban san da rai ba,

   : Hakanga na ba ni tsoro,

‘Y/Amshi: Bai san wuyag gargare ba,

: Ga Garba can zamu jiɗa,

: Namijin da noma ka wa haske.



[1]  Sauka.

[2]  Soka wani abu a cikin wani abu mai sanyi, wanto wanda ruwa ya jiƙe shi sosai kamar ƙasa.

[3]  Jirkito/juyowa.

[4]  Ƙasa mai ɗuski wadda kan buce ƙafafuwan mai tafiya a kanta.

[5]  Taguwa/riga.

[6]  Fatar alheri.

[7]  Numfashi.

Post a Comment

0 Comments