Garba Dauran (Ta biyu)

    Citation: BunguÉ—u, U.H. (2022). WaÆ™oÆ™in Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Amali  Sububu

    Garba Dauran (Ta biyu)

    Alhaji Garba mutumen garin Dauran ne wanda aka san shi da aiyukan noma sosai da sosai. Kodayake ÆŠanboko ne bai saki harkar noma ba, kuma ya sami É—aukaka a cikinta, wannan kan ja hankalin Amali don yin waÆ™arsa ga irinsu.  

         G/WaÆ™a : Gona yake ba ya wargi[1] da noma,

      : Aiki sabon halin Garba Dauran.

      

      Jagora: Kuma na matsa sallama Garba Dauran,

      : An ce Garba bai kwan gari ba,

      : Amina ina mijin naki yay yi.

    ‘Y/Amshi: Ta ce mani tai ku biÉ—o shi gona.

      : Gona yake ba ya wargi da noma,

      : Aiki sabon halin Garba Dauran.

     

         Jagora: Ku gwada mani inda zan iske Garbu[2],  : A gwada mani inda zan iske Garbu,

      : Nik kau tahi nig ga Æ™ura ga gona,

      : Han na aza guguwa ce ka noma,

      : Kuma nit tuna guguwa ba ta kuyye,

      : Ko mota ce ka gafcen jigawa,

      : Mota bata yo kamannin mutum ba,

      : Niz zaburara nit tarekke gabanai.

    ‘Y/Amshi: Yac ce gudu mai dume ga a jima.

      : Gona yake ba ya wargi da noma,

      : Aiki sabon halin Garba Dauran.

     

         Jagora: Gona yake ba ya wargi da noma,

      : Aiki sabon halin Garba Dauran.

    ‘Y/Amshi: Gona yake ba ya wargi da noma,

      : Aiki sabon halin Garba Dauran.

     

         Jagora: Goga yi huÉ—a yi huci uban Nura,

    ‘Y/Amshi: Ai ka isa kai iyaka ka dawo,

    : A biyo ka da ƙoƙunan[3] shikka gero,

    : Gona yake ba ya wargi da noma,

    : Aiki sabon halin Garba Dauran.

     

         Jagora: Kana tahe dai kana Æ™era kuyye,

    ‘Y/Amshi: Ana biye ko ana shikka wake.

     

    Jagora: Kana tahe dai kana ƙera kuyye,

    ‘Y/Amshi: Ana biye ko ana shikka maiwa.

       

    Jagora: Kana tahe dai kana ƙera kuyye,

    ‘Y/Amshi: Ana biye ko ana shikka wake,

      : Gona yake ba ya wargi da noma,

      : Aiki sabon halin Garba Dauran.

     

         Jagora: Na zo kallo gidan Garba Dauran,

      : Na yo kallo gidan Garba Dauran,

      : Ga shanu nasu gehe daban can,

      : Tumaki nasu gehe daban can,

    : Awaki nasu gehe daban can,

    : Ga zabbi nasu gehe daban can,

    : Ga kaji nasu gehe daban can,

    ‘Y/Amshi: Kuma kowane an aza mai abinci,

    : Gona yake ba ya wargi da noma,

      : Aiki sabon halin Garba Dauran.

     

    Jagora: In dai rana tana É“ata baya,

    ‘Y/Amshi: Da na tahi an gasa man jikina,

    : Gona yake ba ya wargi da noma,

    : Aiki sabon halin Garba Dauran,

     

    Jagora: Gona yake ba ya wargi da noma,

      : Aiki sabon halin Garba Dauran.

    ‘Y/Amshi: Gona yake ba ya wargi da noma,

    : Aiki sabon halin Garba Dauran,

     

    Jagora: Gulbi[4] kake sai gada sai ga jirgi,

      : Gulbi kake sai gada sai ga jirgi,

      : In ba a yi ma gada ba a jirgi,

    ‘Y/Amshi: Kowa ka shiga kana kundume[5] shi.

    : Gona yake ba ya wargi da noma,

    : Aiki sabon halin Garba Dauran,

     

         Jagora: ÆŠan Ammani nis sani ad da noma,

    ‘Y/Amshi: Amma kuma ba ya hin Garba Dauran,

     

         Jagora: Kotoko nis sani ad da noma shi ma,

    ‘Y/Amshi: Amma kuma ba ya hin Garba Dauran.

     

         Jagora: Aikau Anne shina gyara gona,

    ‘Y/Amshi: Amma kuma ba ya hin Garba Dauran,

     

         Jagora: Jijji nis sani ad da noma shi ma,

    ‘Y/Amshi: Amma kuma ba ya hin Garba Dauran,

     

         Jagora: Ko Ummaru na sani na da noma shi ma,

    ‘Y/Amshi: Amma kuma ba ya hin Garba Dauran,

     

    Jagora: Gaɓan Ɗankaiwa na gyara gona,

    ‘Y/Amshi: Amma kuma ba ya hin Garba Dauran,

     

         Jagora: Ko alhaji Ali na can da noma,

    ‘Y/Amshi: Amma kuma ba ya hin Garba Dauran,

     

         Jagora: Gulbi kake sai gada sai ga jirgi,

      : Gulbi kake sai gada sai ga jirgi,

      : In ba a yi ma gada ba a jirgi,

    ‘Y/Amshi: Gona yake ba ya wargi da noma,

    : Aiki sabon halin Garba Dauran,

     

         Jagora: Gona yake ba ya wargi da noma,

      : Aiki sabon halin Garba Dauran,

    ‘Y/Amshi: Gona yake ba ya wargi da noma,

    : Aiki sabon halin Garba Dauran.



    [1]  Wasa/rashin kula.

    [2]  Suna ne wato Garba/ Abubakar.

    [3]  ‘Yan Æ™ananan Æ™orai.

    [4]  Kogi.

    [5]  Nutsar da shi.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.