Garba Dauran (Ta farko)

    Citation: BunguÉ—u, U.H. (2022). WaÆ™oÆ™in Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Amali  Sububu

    Garba Dauran (Ta farko)

    Garba Dauran Shahararren manomi ne a yankin Zurmi ta jihar Zamfara. Ma’aikacin gwamnati ne wanda ya shugabanci Æ™aramar hukumar zurmi a 2011 har zuwa 2015. Yana da manya-manyan gonaki kuma mai arzikin noma ne, hakan ya sa mawaÆ™a suke yi masa waÆ™a daga cikinsu har da Amali  Sububu.

     

         G/WaÆ™a : Jijjihi[1] yakai daji,

    : Baya wargi,

      : Kodayaushe shi dai bai,

    : San sake ba,

    : In yi mai kiÉ—in aiki,

    : Garba Dauran.

     

     Jagora: Mun kwana munka yo sallah,

    : Munka dawo,

      : Amali na yi hul tanki,

    : Tun da sahe,

      : Ni dai ina ta É—ora giya,

    : Babu dama,

      : Mun zo Arewa mun yi kwana,

      : Munka kwan nan.

    ‘Y/Amshi: Jijjihi yakai daji,

    : Baya wargi,

      : Kodayaushe shi dai bai,

    : San sake ba,

    : In yi mai kiÉ—in aiki,

    : Garba Dauran.

     

    Jagora: Mun kwana munka yo sallah,

    : Munka dawo,

      : Amali niy yi hul tanki,

    : Tun da sahe,

      : Ni dai ina ta jehwa giya,

    : Babu dama,

      : Mun yo Arewa zamu kwana,

    : Munka kwana,

      : Ran nan ana cikin la’asar,

    : Munka dawo.

     

    ‘Y/Amshi: Jijjihi yakai daji,

    : Baya wargi,

      : Kodayaushe shi dai bai,

    : San sake ba,

    : In yi mai kiÉ—in aiki,

    : Garba Dauran.



    [1]  Sammako tun gari bai waye ba.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.