Ticker

6/recent/ticker-posts

Garba Gwarzon Maza

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Garba Gwarzon Maza

 

 G/Waƙa : Garba Gwanzon maza,

: Allah ya yi ma,

: Baibayan[1] noma.

 

  Jagora: Garba Gwanzon maza,

: Allah ya yi ma,

: Baibayan noma.

‘Y/ Amshi: Garba Gwanzon maza,

: Allah ya yi ma,

: Baibayan noma.

 

  Jagora: Tafi gona shire,

: Ɗan Muhamman,

‘Y/Amshi: Allah ba ka

: Ɗan Kandaren Musa,

: Garba Gwanzon maza,

: Allah ya yi ma,

: Baibayan noma.

 

 Jagora: Kowaz zo Ƙiri,

:Ya gode Allah,

 ‘Y/Amshi: Don ƙamshin hatci,

: Suka tarbonai,

: Garba Gwanzon maza,

: Allah ya yi ma,

: Baibayan noma.

 

Jagora: Giwa sa gaba inda kiy yi,

 ‘Y/Amshi: Don Allah ƙetare,

: Ba ya yin komi,

: Garba Gwanzon maza,

: Allah ya yi ma,

: Baibayan noma.

 

 Jagora: Ga abu ukku su za su,x2

‘Y/ Amshi: Ba su kwanawas su,

: Wuri guda mun sani lalle,x2

: Garba Gwanzon maza,

: Allah ya yi ma,

: Baibayan noma.

 

 Jagora: Mata da miji,x2

: Da yunwa wuri ɗai,

 ‘Y/ Amshi: In sun kwan ukku,

: Wani na barin wani nan.,

: Garba Gwanzon maza,

: Allah ya yi ma,

: Baibayan noma.

 

 Jagora: Zan naga kan wuri,x2

‘Y/ Amshi: Inda duk ke ɓoye,

: Hura tana nan tana yami.x2

: Garba Gwanzon maza,

: Allah ya yi ma,

: Baibayan noma.

 

 Jagora: Ja gaban maza kake,

: Na Mamman,

 ‘Y/ Amshi: Ka gwada ko hura bata yin yami,

: Garba Gwanzon maza,

: Allah ya yi ma,

: Baibayan noma.



[1]  Arziki/rufin asiri.

Post a Comment

0 Comments