Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Garba Na Yabo
G/ waƙa: Sa maza gudu mai raba gardama,
: Garba jan zaki.
Jagora:
To mu je gaba madalla Garba,
: Mai yi ma noma bugun tambarin yaro,
: Ina Garba na Yabo bai san da rana ba,
: Ai wassaka ni, wa maska ni,
: Ka zan tabbataw wada,
: Inda uwab Bala mai dubun mato,
: Ai inda uwak Kini mai dubun mato,
: Ai Garba,
: Ka dai gama da
hanƙuri,
: Garba ka hanƙure mani.x2
: Abu Garba ka hanƙure mani,
: Garba na Yabo bai
san da rana ba.
Jagora: Garba Ɗanmaliki sai
marece wurin aiki,
: Mai kwana yana
lisahin aiki,
: Yabo akwai ɗiya maza,
: Yabo akwai
mazaizan biɗad dawa,
: Ni kulu na san ɗiya mazan,
: Ni Kulu ko
mazaizanmu sun san ni,
: Yabo kun taimaki
Hauwa mai kodalin aiki,
:
Ai Yabo kun taimaki Hauwa mai sa maza aiki.
Jagora : Ai
wassaka ni, wa maska ni,
: Ka zan tabbataw wada,
: Ɗebe batun kiɗi da ak kiɗe,
: Ko na bari mi ka sha man kai?
: Ni kulu na ji an yi liman,
: Wasu basu bi nai dadaɗin rai,
: To bare kiɗi kiɗe ko na bari,
: Mi ka sha man kai?
: Don dai galibin mutane,
: Halin mutane dun na shanu ne,
: In dai nagge ta ga ɓanna,
: Aniya takai don a koro ta,
: Ko an bat tata yi ɓanna,
: Ɓannag go ko ɓata ƙwasshe ta,
: Ɓannak kai takai don biɗam magana,
: Allah dai ya taimaka,
: Tabaraka Allah ya ba ‘Yanmaza sa’a.
: Abu da matansu ko sun ji daɗinsu,
: Na Sadiyya Garba bai san da rana ba,
: Na Mairi mai kai marece wurin aiki.
Jagora : Ƙanen
muhammadu Garba.x2
: Garba maƙi gudu maigidana ne,
: Ka ga su wane su ka gayyat taɓi,
: Da kaɗassu taɗ ɗwaɗe[1],
: Sai gayya yakai da kainai,
: Mata aniya kukai tunda ta ɗwaɗe,
: Sabko kukai tunda ta ɗwaɗe,
: Tun ba a jinjima ba mata,
: Sai ga itace ga kanunsu
: Sai wata tambaya yakai,
: Shanu sun yi ɓanna ga kaɗakka,
: Sun ce ja ka ban wuri,
: Kai hakanan kakan hwara ƙaryakka.
Jagora:
Kaɗakka[2] ko ƙuje bai hwaɗa ba,
: Sai in hwa bayanmu,
: Ai dai ƙwazo yana da daɗi,
: Kai ga irin wanda kas samu.
: Ya rangame na auna,
: Amsa yakai har a yo taɓi[3],
: Ya bar su sai ma’auni,
: Hwaɗin[4] ma’aunin kamaf fanka.
: Inda dai da zucciya,
: Da kowa ka ce sai ta ɗau tata.
: Sai ka yi sunanka tungurun,
: Ka huta da laihin biyab bashi.
: Ka ga su wane na ta kware ɗaki,
: Suna baibaye zaure.
: Halama kun hi son zaure,
: Kun hi cin moriyaz zaure?
Jagora : Ai
bakin yini sukai,
: Hauwa uwat Tuni bana kwana ba.
: Ka ga su wane na ta kware munta,
: Suna dwaɗe bayansu.
: Halan ruhwan ɗuwan ‘yan bori,
: Kukai don ku sha iska.
: Inji uwab Bala mai dubun mato,
: Garba Ɗanmaliki ka biyasheni na gode.
: Ai na Salihu mai kai marece wurin aiki.
: Mazana ku gama da hanƙuri,
: Allah ɗai yaz zan guda maza,
: Ai ya ishi duniya maigida Garba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.