Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Garkuwan Bauchi Amadun kari
G/Waƙa: Garkuwan Bauchi
Amadun Kari.
Jagora: Garkuwan Bauchi
Amadun Kari.
. ‘Y/
Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Wannan kiɗa, duk kiɗan manoma ne,
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Na Garkuwan Bauchi
Amadun Kari.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Wannan kiɗan duk kiɗan manoma ne,
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Na Garkuwan Bauchi
Amadun Kari.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Ku gyara gona, ku
share gonarku,
: In
damina ta iso ruwa ya zo
: Ku
shuka komai, amma a gonakku,
: Ya
zamanto komai duk mai amfani.
: Mai
shuka komai ba zai rasa komai ba.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun
Kari.
Jagora: Idan mutun ya ga
bai da gona yau,
: Ya
shiga a zucci ya shuka alheri,
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Mai shuka wannan
ba zai rasa komai ba,
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Mu tama ‘yan
Bauchi godiyar Allah,
: Nan
aka yo baba Amadun kari.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Garkuwan Bauchi
Amadun Kari.x2
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun
Kari.x2
Jagora: Ma’aikata, kun a
yi ma horon[1]
nan,
:
Idan mutun ya shige cikin ofis,
:
Idan ya taso a nan cikin ofis
: In
la’asar ta yi ta riga ta yi,
: Ya ɗauki mota ya doshi
gonassa.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Ya ɗauki mota ya doshi
gonassa,
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Ya ɗauki doka ta Amadun
kari.x2
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun
Kari.x2
Jagora: Garkuwan Bauchi
Amadun Kari.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun
Kari.
Jagora: Ka ga gida,
: Sai
ka ce gidan Rasdan[2]
: Sai
suka ce,
: Man
gidan na gona ne.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun
Kari.
Jagora: Wace gona ta
Amadun Kari,
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Garkuwan Bauchi
Amadun Kari.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Amadu ne,
: Yay
yi garkuwan Bauchi,
:
Kana ya zo,
: Yay
yi garkuwan aiki.x2
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun
Kari.x2
Jagora: Garkuwan Bauchi
Amadun Kari.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Wo garkuwan Bauchi
Amadun kari.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Wannan kiɗa, duk kiɗan manoma ne.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Don masu koyi da
Amadun Kari.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Na ɗauki doka, ta
Amadun kari,
:
Kula da gona yana da alfanu.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun
Kari.
Jagora: Kula da gona yana
da alfanu.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Wo Garkuwan Bauchi
Amadun Kari.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Mu tama ‘yan
Bauchi godiyar Allah.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Nan aka yo[3]
baba Amadun kari.
‘Y/
Amshi:
Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Garkuwan Bauchi
Amadun Kari.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Wannan kiɗan duk kiɗan manoma ne.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Amadu ne yay yi
garkuwan Bauchi,
:
Kana ya zo yay yi garkuwan aiki.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Amadu in yac ci
garkuwan Bauchi,
:
Sannan ya zo yay yi garkuwar aiki[4].
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Garkuwan Bauchi
Amadun Kari.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Ce wa manoma ku
gyara gonakku.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Ka duba Shata na
Yelwa mai waƙa,
: In na
yi yawo, na gama waƙata,
: Na
zo gida na ga damina ta yi,
: In
tahi gona in gyara gonata,
: Ina
ta koyi da Amadun Kari.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun
Kari.
Jagora: In tafi gona, da
ni da yarana,
:
Muna ta koyi da Amadun Kari.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Muna ta koyi da
Amadun Kari.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Garkuwan Bauchi
Amadun Kari.x2
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun
Kari.x2
Jagora: Mu tama[5]
‘yan Bauchi godiyar Allah.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Nan aka wo baba
Amadun Kari.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Wo Garkuwan Bauchi
Amadun Kari.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
Jagora: Wanga kiɗan duk kiɗan manoma ne.
‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.