Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali Sububu. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Gora Uwat Tuwo
Gora mutumiyar Gidan bisa ce ta cikin ƙaramar hukumar mulkin Maradun, amma tana aure a garin
Gidan Nababba a ƙarƙashin ƙaramar hukumar Shinkafi, duk a
cikin jihar Zamfara. A can take tuwo-tuwo, kuma ta shahara ga sana’ar don haka
Amali ya yi mata waƙa.
G/Waƙa : Za ni ga Gora uwat tuwo,
: Ta Sa’idu buƙatakki ta biya,
Jagora: Ni
dai wance miyakki,
: Ban ga ta yi ba,
‘Y/Amshi:
Tun ban lasa ba,
: Ga ƙuda ciki,
: Za ni ga Gora uwat tuwo,
: Ta Sa’idu buƙatakki ta biya,
Jagora: Ai
na ga tuwonki wance,
: Sai makaho,
: Sai ko wanda ba gida kusa,
: Da ya ci tuwon kwabo,
: Ya burkuce hanji,
‘Y/Amshi:
Sai zuwa wurin amai,
: Za ni ga Gora uwat tuwo,
: Ta Sa’idu buƙatakki ta biya,
Jagora: Mu dai ga Gora mun kawo hari[1],
: In na ishe Gora tana gida,
: Kurawa sai in yi hira nan,
: In na ishe Gora ba ta gida,
: Ɗan Goje in
wuce,
: Ta Maguru,
‘Y/Amshi:
Za ni ga Gora uwat tuwo,
: Ta Sa’idu buƙatakki ta biya,
Jagora: Ga
Ummaru ya yanka saniya ta kwabe[2],
: Ta yi mai ƙwarai-ƙwarai,
: Ga Gora ta taho da kwano,
: Ta ce Sanda ga ni na taho,
: Ta sai ƙassan[3]
goma sha bakwai,
: Ta sai tsoka ta hwan huɗu Kuma,
: Ga tosshi[4] ta
sawo da yaji,
: Ga kinba da ciitta ta sawo,
: Gyara miyakki mai halin ɗiya,
: Da ka ci tuwonta sai zuhwa ya kubcikke ma,
: Sai ka yi santi.
‘Y/Amshi:
Sannan ka ji jiɓi yana yima ƙawa[5],
: Za ni ga Gora uwat tuwo,
: Ta Sa’idu buƙatakki ta biya,
Jagora:
Allah ya baki martabar miya, x2
‘Y/Amshi: Kuma Allah yai miki hwarin jini,
: Za ni ga gora uwat tuwo,
: Ta Sa’idu buƙatakki ta
biya.
Jagora:
Kuma Allah yai maki hwarin jini,
‘Y/Amshi:
Kuma Allah yai miki hwarin jini,
: Za ni ga gora uwat tuwo,
: Ta Sa’idu buƙatakki ta
biya.
Jagora:
Ni dai wance miyakki,
: Ban ga ta yi ba,
‘Y/Amshi:
Tun ban lasa ba,
: Ga ƙuda ciki,
: Za ni ga Gora uwat tuwo,
: Ta Sa’idu buƙatakki ta biya,
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.