Ticker

Gwauro (Dudu)

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Gwauro (Dudu)

Amadu ne sunansa a garin Gidan Nababba yake na  ƙasar Shinkafi ta jihar Zamfara. Amali ya yi masa waƙa ne saboda zamansa gwauro na tsawon lokaci.

 

   G/Waƙa : Sannu da gaskanta[1] wuta,

: Sannu da gaskanta wutas sanwa,

 

 Jagora: Sannu da gaskanta wuta.

‘Y/Amshi: Sannu da gaskanta wuta,

: Sannu da gaskanta wutar sanwa,

: Mi za ta yi ma?

: Gwauro,

: Barka da walaƙanci,

 

 Jagora: Sannu da gaskanta wuta dai,

‘Y/Amshi: Sannu da gaskanta wutar sanwa,

: Mi za ta yi ma?  

: Gwauro,

: Barka da walaƙanci.

 

 Jagora: Sannu da gaskanta wuta gwauro,

‘Y/Amshi: Sannu da gaskanta wutar sanwa.

 

 Jagora: Na ɗoke ka lambuwal[2],

: Sabon injin na ƙasar isa,

‘Y/Amshi: Mi za ta yi ma?

: Gwauro,

: Barka da walaƙanci.

 

 Jagora: Na ɗauke ka lambuwal.

‘Y/Amshi: Sabon injin na ƙasar Isa.

 

 Jagora: Komai lokaci garai.

‘Y/Amshi: Don haka yac ce,

: Mu yi mai waƙa.

: Mi za ta yi ma?

: Gwauro,

: Barka da walaƙanci,

 

 Jagora: Komai lokaci garai.

‘Y/Amshi: Don haka yac ce,

: Mu yi mai waƙa,

 

 Jagora: Gaggarje bushi[3] wuta.

‘Y/Amshi: Yanzu ta kama,

: Mu ga haskenta.

 

 Jagora: Gaggarje bushi wuta,

‘Y/Amshi: Yanzu ta kama,

: Mu ga haskenta,

 

 Jagora: Sa mata hwanho[4],

: Mu ga haskenta,

‘Y/Amshi: Yanzu ta kama,

: Mu ga haskenta,

: Mi za ta yi ma?

: Gwauro,

: Barka da walaƙanci.

 

 Jagora: Dudu tun yana da mata tai,

: Ya ima daka,

: Ya iya wankin surhe.

  ‘Y/Amshi: Ya iya cincimta ruwan sanwa.

: Mi za ta yi ma?

 : Gwauro,

: Barka da walaƙanci.

 

 Jagora: Dudu tun yana da mata tai,

: Ya ima daka ,

: Ya iya warkin Surhe,

‘Y/Amshi: Ya iya cimcimta ruwan sanwa.

: Mi za ta yi ma?

: Gwauro barka da walaƙanci,

 

 Jagora: An aike shi kassuwa,

; Ya ishe rogon taɓe,

: Dudu yab bada taro,

‘Y/Amshi: Yak kaɓe saye,

: Da hushin hwarin.

: Mi zata yi ma?

: Gwauro,

: Barka da walaƙanci.

 

 Jagora: Gaggarje bushi wuta,

‘Y/Amshi: Yanzu ta kama,

: Mu ga haskenta.

 

 Jagora: Dudu ka ƙi yin tsawo.

‘Y/Amshi: Don kada tsaba,

: Ta ga damak ka.

: Mi zata yima?

: Gwauro barka,

: Da walaƙanci.

 

 Jagora: Amadu ka ƙi yin tsawo.

‘Y/Amshi: Don kada reda[5],

: Ya ga damak ka.

: Mi zata yi ma?

: Gwauro,

: Barka da walaƙanci.

 

 Jagora: Ka san in ana kiɗin bindiga,

: Ba a jin amon ƙyestu,

: In kana daka,

: Dudu mata su aje,

‘Y/Amshi: Sai ka kirɓa a ji ɗan nasu,

: Mi za ta yima?

: Gwauro barka,

: Da walaƙanci.

 

 Jagora: Sai ka kirɓa su hito su kau.

‘Y/Amshi: Sai ka kirɓa aji ɗan nasu.

: Mi za ta yi ma?

: Gwauro barka,

: Da walaƙanci.

 

 Jagora: Ga Dudu yana daka,

: Ga mata suna daka,

: Amma ba a jin dakan mata,

: Nashi ya haye.

‘Y/Amshi: Mun ishe ya sa,

: Ribiɗin hwarin.

: Mi za ta yi ma?

: Gwauro,

: Barka da walaƙanci.

 

 Jagora: Ga Dudu yana daka,

: Ga mata suna daka,

: Amma ba a jin dakan mata,

: Nashi ya haye.

‘Y/Amshi: Mun ishe ya sa,

: Ribiɗin[6] hwarin.

: Mi za ta yi ma?

: Gwauro,

: Barka da walaƙanci.

 

 Jagora: Gwauro,

: In ana tsaron tsuntsu,

: Ba ya cin tuwo,

: Kuma dai ba ya shan hura,

: Yayin cin tumu[7] yakai.

‘Y/Amshi: Can yaka lalata hatci daji,

: Mi za ta yi ma?

: Gwauro,

: Barka da walaƙanci.

 

 Jagora: Amadu in ana tsaron tsuntsu,

: Ba ya cin tuwo,

: Kuma dai ba ya Shan hura,

: Yayin cin tumu yakai.

‘Y/Amshi: Can yaka muzanta hatci daji.

: Mi za ta yi ma?

: Gwauro,

: Barka da walaƙanci.

 

 Jagora: Duk gonar da kak karam ma tumu[8],

: Ta ɓace ɓari,

: Wannan ba ta yin da,

‘Y/Amshi: In ka ga hatci tsaitsaye bici[9] ne,

: Mi za ta yi ma?

: Gwauro,

: Barka da walaƙanci,

 

 Jagora: Babu hatci tsaitsaye ya zwage,

‘Y/Amshi: In ka ga hatci tsaitsaye bici ne,

: Mi za ta yi ma?

: Gwauro,

: Barka da walaƙanci.

 

 Jagora: Gaggarje[10] bushi wuta.

‘Y/Amshi: Yanzu ta kama muga haskenta,

 

 Jagora: Sannu da kamkamta wuta,

‘Y/Amshi: Sannu da kamkamta wuta,

 

 Jagora: Dole ka kamkamta wuta Amadu,

‘Y/Amshi: Dole ka kamkamta wutas sanwa,

 

 Jagora: Amadu barka da walaƙanci,

‘Y/Amshi: Amadu barka da walaƙanci,

 

 Jagora: Gwauro barka da ganin reni.

‘Y/Amshi: Gwauro barka da walaƙanci.

 

 Jagora: Amadu barka da zama ‘yamti[11],

‘Y/Amshi: Amadu barka da zama ‘yamti.

: Mi za ta yi ma?

: Gwauro barka da walaƙanci.

 

4.0.5 Gwauro (Ma’azu)

Ma’azu wani Bafulatanin daji ne Amali ya yi wa wannan waƙa. A garin  Sububu yake ta ƙaramar hukumar Maradun a jihar Zamfara. 

 

   G/Waƙa : Sai na taho ga mai huskar shanu,

: Mai kamar kare ya katce.

 

 Jagora: Sai na taho ga mai huskar shanu.

‘Y/Amshi: Sai na taho ga mai huskar shanu,

  : Ga Ma’azu gwauron daji.

 

 Jagora: Sai na taho da mai hikimar banza,

  : Mai kamar kare ya gibce.

‘Y/Amshi: Sai na taho ga mai huskar shanu,

  : Ga Ma’azu gwauron daji.

 

 Jagora: Gwauro mai hankalin sayaki[12].

‘Y/Amshi: Gwauro mai hankalin katsattcen doki,

  : Sai na taho ga mai huskas shanu,

  : Ga Ma’azu gwauron daji.

 

 Jagora: Gwauro mai hankalin sayaki.

‘Y/Amshi: Gwauro mai hankalin katsattcen doki,

  : Sai na taho ga mai huskas shanu,

: Ga Ma’azu gwauron daji.

 

 Jagora: Ba bin gari ya kai ba.

‘Y/Amshi: Sai ya bi shalla ya ɗora kukan mesa,

: Sai na taho ga mai huskar shanu,

  : Ga Mu’azu gwauron daji.

 

 Jagora: Ba bin gari shi kai ba.

‘Y/Amshi: Sai ya bi shalla ya ɗora kukan mesa.

 

 Jagora: Ƙannenka sun hana maka twatsa,

  : Sun bakka nan ga kwamtsad ebe[13],

‘Y/Amshi: Sai na taho ga huskar shanu,

  : Ga Mu’azu gwauron daji.

 

 Jagora: Ƙannenka sun hana ma twatsa.

‘Y/Amshi: Sun bakka nan ga kwamtsad ebe,

  : Sai na taho ga huskar shanu ,

: Ga Mu’azu gwauron daji,

 

 Jagora: Kai ku ji banza ta gane banza,

‘Y/Amshi: Mu’azu gwauro da kudaku[14] nai daji.

 

 Jagora: Banza ta shikka banza,

‘Y/Amshi: Mu’azu gwauro da kudaku nai daji,

 

 Jagora: Kai ku ji noma ta no,.. kai!

‘Y/Amshi: Mu’azu gwauro da kudaku nai daji,

 

 Jagora: Kai ku ji banza ta noma banza.

 

‘Y/Amshi: mu’azu gwauro da kudaku ya noma,

  : Sai na taho ga huskad banza ga,

  : Mu’azu gwauron daji,

 

 Jagora: Gwauro mai hankalin sayaki,

‘Y/Amshi: Gwauro mai hankalin katcattcen doki,

 

 Jagora: Taho mai kama da ɗan kai hwata,

‘Y/Amshi: Taho mai kama da turmin kuka,

 

 Jagora: Taho mai kama da bangon zaure,

‘Y/Amshi: Taho mai kama da turmin kuka.

  :Sai na taho ga mai huskad shanu,

  : Ga ma’azu gwauron daji.

 

 Jagora: Gwauro bai san halin batun mata ba,

  : Sai ga mu’azu ya kai sisi.

‘Y/Amshi: Sai nataho a mai huskad shanu ga,

  : Mu’azu gwauron daji.

 

 Jagora: ‘Yan nan tac ce ina jiranka dan nan,

  : Sai ga Mu’azu ya kai sittah[15],

‘Y/Amshi: Sai na taho ga mai huskad shanu,

  : Ga mu’azu gwauron daji.

 

 Jagora: Rannan yas saida zakarunai,

  : Dan nan sai ga Mu’azu ya kai ukku,

‘Y/Amshi: Sai na taho ga mai huskas shanu,

  : Ga Mu’azu gwauron daji.

 

 Jagora: Rannan yas saida akuyatai dannan,

  : Sai ga mu’azu ya kai nera.

‘Y/Amshi: Sai na taho ga mai huskad shanu, 

  : Ga Mu’azu gwauron daji.

    

 Jagora: Rannan yas saida tunkiyatai dan nan,

  : Sai ga Mu’azu ya kai fefa.

‘Y/Amshi: Sai na taho ga huskas shanu,

  : Ga Mu’azu gwauron daji.

 

 Jagora  : Tac ce Mu’azu ya kai kuɗɗi,

  : Bai zo wurin batun hira ba.

‘Y/Amshi: Sai na taho ga mai huskas shanu,

  : Ga Mu’azu gwauron daji,

 

 Jagora: An ce Mu’azu ya kai kuɗɗi, 

  : Bai zo wurin biɗad aure ba.

‘Y/Amshi: Sai na taho ga mai huskas shanu,

  : Ga Mu’azu gwauron daji.

 Jagora  : Shi ko rannan Mu’azu sai yag gyara,

  : Rannan Mu’azu sai ya uhwa[16],

‘Y/Amshi: Sai na taho ga mai huskad shanu,

  : Ga Mu’azu gwauron daji.

 

 Jagora: Yac ce ‘yan Tubali salamu alaikum,

‘Y/Amshi: Yau na taho biɗad kunkunne[17],

  : Sai na taho ga mai husakas shanu,

  : Ga Mu’azu gwauron daji.

 

 Jagora: Sai na taho ga mai hikimab banza,

: Mai kamak kare ya girtce.

‘Y/Amshi: Sai na taho ga mai huskas shanu,

  : Ga Mu’azu gwauron daji.

 

 Jagora: Banza ta gane banza ga Mu’azu,

  : Gwauro da kudaku nai daji.

‘Y/Amshi: Sai na taho ga mai huskas shanu,

  : Ga Mu’azu gwauron daji.

 

 Jagora: Banza ta gane banza. 

 ‘Y/Amshi: Ga Mu’azu gwauro da kudaku nai Daji.



[1]  Shirya itace ko wani makamashi don kunna wutar sanwa.

[2]  Na farko/lamba ta ɗaya.

[3]  Hura wuta da iskan baki.

[4]  Busa iska.

[5]  Niƙa

[6]  Dakan gero har ya yi gari bayan an surfe.

[7]  Zangarniyar gero wanda akan zaɓa a gasa a kware a ci.

[8]  Gero wanda ya fara ƙusa mai ido, wanda manoma kan ɗebo su kawo gida a riƙa gasawa anai murmutsawa ana ci

[9]  Gero wanda bai yi ido ba marar ƙwari.

[10]  Dagewa.

[11]  Zama babu mata.

[12]  Kura.

[13]  ‘Yayan nunu da ake fasawa a cinye tuwon, wannan tuwon da ke ciki shi ake kira ebe.

[14]  Dankali.

[15]  Sule da sisi.

[16]  Tserewa/Guduwa

[17]  Mata don a aura.

Post a Comment

0 Comments