Haruna Dan Mani (Sarkin Noman Mayanci)

    Citation: Bungudu, H. U. (2023). ZaÉ“aÉ“É“un waÆ™oÆ™in mawaÆ™an baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bungudu
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Noma

    Haruna Dan Mani (Sarkin Noman Mayanci)

     

    G/Waƙa : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

      Jagora : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

    ‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

      Jagora : Haruna ÆŠan Mani,

    : Barkar ka da ya kin kai,

    : Tausar yama,

    : Ga wag ga ƙasa duk mai riƙe kalme,

    : Ya san da kai.

    ‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

      Jagora : Ga Ladan ga Karto tare da Ada na dangi,

    : Sai sun zo aiki ya ka ƙarewa,

    : Nan da nan,

    : Tunda sai sun zo aiki ya ka ƙarewa,

    : Nan da nan.

    ‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

      Jagora  : Tunda sabra ba ta buwaya,

    : In sun ka zo,

    : Saboda na san samra ba ta buwaya,

    : In sun ka zo.

     ‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

      Jagora : To ai ko can ‘yan yara,

    : Ka katsewa don wuya.

    ‘Y/Amshi : Arna bakin rai suka aiki,

    : In sun ka zo,

    : Aiki in kuma bai ƙare ba,

    : Su sha ‘Billahillazi,

    : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

     Jagora: Himma na Abu,

    : Kai ma ni kyauta daidai da ni,

    : Ni kuma in shirya maka waƙa,

    : Dai-dai da kai.x2

    ‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

      Jagora : ÆŠan Mani ka gaji bajinta,

    : Wajjen uwa,

    : ÆŠan Mani ka ga ji bajinta,

    : Wajjen uba.

    : Kai ÆŠan Mani ka ga ji bajinta,

    : Wajjen uwa,

    : ÆŠan Mani ka gaji bajinta,

    : Wajjen uba.

    : To ni kuma ba raggon makaÉ—i,

    : Nah haihoni ba.

    ‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

      Jagora  : Yanzu Mayanci,

    : Can aka sabga[1] ta ƙwarai,

    : Abin da duk nir roƙa,

    : Ba a cewa babu shi,

    : Audu bara na saki da su,

    : Na zo in shaida maka,

    : Yunwar tsaba garan,

    : Na zo in shaida maka,

    : Yunwar kuÉ—É—i garan,

    : Tamkar jariri nike,

    : Ni ban san babu ba.

    ‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

      Jagora : Abu Tafidan Zurmi,

    : Tare da Sarkin Noma,

    : Haruna ban yi musun,

    : In samu kujera wajjensu ba.

    ‘Y/Amshi: Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

      Jagora : Garba Abu Daura,

    : ÆŠan Alhajiya shiryayyen mutum,

    : Garba Abu Dauran, 

    : ÆŠan Alhajiya shiryayyen mutum.

    ‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

     Jagora : Haruna ÆŠan Mani,

    ‘Y/Amshi : Barkar ka da yaÆ™in tausar yama,

    : Ga wag ga ƙasa,

    : Duk mai riƙa kalme,

    : Ya san da kai.

     

     Jagora : Audu na aje roÆ™o gidan ka,

    : Gidan katanga mi ag ga rai?

      ‘Y/Amshi: Wajjen mai miÆ™a muna samu,

    : Can munka yi,

    : Mijin Jaɓɓo da Hauwa da Inno,

    : Cikakken mutum,

    : Allah bai yo Alhaji,

    : Samnan[2] dattijo ba,

    : Wahabu Allah bai yo Alhaji,

    : Samnan dattijo ba,

     

    Jagora : Imani ya kammala,

    : Guri nai ya cika,

    : Kamar ya je aikin hajji,

    : Ya samu gida Gusau.

     ‘Y/Amshi: Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

      Jagora : Tunau Cika Hanna,

    : Babba na Alhaji Sabon gari,

    : Mai nasarar damana,

    : Mijin Jaɓɓo na dan hababba,

    : Na tuba duk banga mutum,

    : Mai nomanka ba,

    : Ƙasar ga na duba duk,

    : Banga mutum mai nomanka ba.

    ‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona yakwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

    Jagora : KiÉ—in da niy yi ma,

    : Ga rediyo nika kai,

    : Amma sai jama’a,

    : Sun ce mani waƙar nan ta shiga,

    : KiÉ—in da niy yi ma,

    : Ga rediyo nika kai,

    : Amma sai jama’a,

    : Sun ce mani waƙar nan ta shiga.

    : Mijin Inno ka yi man wasiƙa,

    : Ta kai ga ran,

    : Na san alheri muka samu,

    : In munka zo.

     

      Jagora  : Mijin JaÉ“É“o da kay yi man wasiÆ™a,

    : Ta kai garan,

     ‘Y/Amshi : Na san alheri muka samu,

    : In mun ka zo.

     

      Jagora  : Mai gidan Kuluwa ka yi man wasiÆ™a,

    : Ta kai garan.

      ‘Y/Amshi: Na san alheri muka samu in munka zo,

    : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

    Jagora : Gabas ga Mayanci,

    : Ba su da daji ko É—an kaÉ—an,

    : Sarkin noman yamma,

    : Ga kwalta ya sassabe,

    : Gabas ga Mayanci,

    : Ba su da daji ko É—an kaÉ—an,

    : Sarkin noman yamma,

    : Ga kwalta ya sassabe[3],

     

     Jagora: To in dai niz zo Mayanci,

    : In zo da mayaya niyo,

    : Sai na tahi na gano,

    : Bahillacen arziki,

    : Ni dai ban rena ma muhaman, 

    : ÆŠan zainaba ba.

    ‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

      Jagora: Haruna ÆŠan Mani,

    : Barkar ka da yaƙin,

    : Tausar yama,

    ‘Y/Amshi : Ga wag ga Æ™asa,

    : Duk mai riƙe kalme,

    : Ya san da kai.

    : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

      Jagora: Haruna ÆŠan Mani,

      ‘Y/Amshi: Barkar ka da yaÆ™in,

    : Tausar yama.

    : Ga wag ga ƙasa,

    : Duk mai rike kalme,

    : Ya san da kai.

    : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

     Jagora: ÆŠan Mani barkak ka da yaÆ™in,

    : Tausar yama,

    : Ɗan Mani barkak ka da yaƙin,

    : Noman hatsi,

    : Dan Mani,

    : Barkak ka da yaƙin,

    : Noman gyaÉ—a.

      ‘Y/Amshi: Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

      Jagora: Haruna ÆŠan Mani,

    ‘Y/Amshi: Barkar ka da yaÆ™in,

    : Tausar yama,

    : Ga wag ga ƙasa,

    : Duk mai riƙe kalme,

    : Ya san da kai.

    : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu,

     

      Jagora: Ya nuna min Isa,

    : Jikan Jatau halin bajinta,

    : Shi ya yi man,

    : Zaman[4] ya ba,

    : Audun Baraka,

    : Kyautar goÉ—iya[5].

     

    Jagora: ÆŠan Masanin BunguÉ—u, 

    : Mijin Hajiya Rabi,

    : Mijin Hajiya Hafsi,

    : Mijin Hajiya Hasiya,

     ‘Y/Amshi : Ni dai ban re na ba,

    : Da halin girmanka ba,

    : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

      Jagora: Haruna ÆŠan Mani,

    : Barkar ka  da yaÆ™in,

    :Tausar yama.

    ‘Y/Amshi: Ga wag ga Æ™asa,

    : Duk mai riƙa kalme,

    : Ya san da kai.

     

      Jagora: ÆŠanmasanin BunguÉ—u,

    : Mijin Hajiya Rabi,

    : Mijin Hajiya Hafsi,

    : Mijin Hajiya Hasiya,

    : Mijin Hajiya hasiya,

      ‘Y/Amshi : Ni dai ban rena ba,

    : Da halin girmanka ba,

    : Don ko ka taimaka,

    : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona yakwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

      Jagora: Haruna Dan Mani,

    : Barkar ka da yaƙin,

    : Tausar yama,

    ‘Y/Amshi: Ga wag ga Æ™asa,

    : Duk mai riƙe kalme,

    : Ya san da kai,

     

     Jagora: Mijin JaÉ“É“o da kay yi min wasiÆ™a,

    : Ta kai garan,

      ‘Y/Amshi : Nasan alheri muka sa mu,

    : In mun ka zo,

     

    Jagora : Mai gidan Inno,

    : Ka yi min wasiƙa,

    : Ta kai garan.

     ‘Y/Amshi  : Na san alheri muka samu,

    : In mun ka zo.

     

    Jagora: Mai gidan Kuluwa,

    : Ka yi min wasiƙa,

    : Ta kai garan.

     ‘Y/Amshi  : Na san alheri muka samu,

    : In mun ka zo.

    : To in dai ba ka miƙa mana,

    : Damman geronka ba,

    : Ka na da halin miƙa,

    : Muna damman wazobiya[6].

    ‘Y/Amshi: Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

      Jagora: To shi dai raggo,

    : Ba ya buƙatar komi garan,

    : To shi dai raggo,

    : Ba ya bukatar komi garan,

    ‘Y/Amshi: Gaya mai ko ni,

    : Ba ni buƙatar komi garai.

     

      Jagora: Tunda daga mazan kirki,

      ‘Y/Amshi : Mis sa mu biyas,

    : Shaggun gorina.

    : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

      Jagora : Gidan mutumin kirki,

    : Aka samun sabgar[7] ƙwarai,

    : Gidan raggo sai masu,

      ‘Y/Amshi: Sai masu shiririta ar akwai.

    : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona yakwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

      Jagora : Ya nuna min isa,

    : Jikan Jatau halin bajinta,

    : Shi yay yi min,

    : Zaman ya ba Audun Baraka,

    : Ka ban goÉ—iya[8],

    : Baban su Kabiru,

    : Yanzu miƙa min raƙumi,

      ‘Y/Amshi: Mu nemi akala[9] in riÆ™a,

    : ÆŠaukar kaya da shi.

    : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu,

     

      Jagora  : Randa yay yi Noma,

    : Yas samu abinci nai ya isai,

    : Gidan raggo ko yaushe,

    : Abinci  ya bar isa,

    : Shi dai raggo babu hatsi,

    : Ba kuÉ—in saye,

    : Matanai sun firgita,

    : Sun ce duk sun hita,

     ‘Y/Amshi: Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

     Jagora  : To shi dai rag go ,

    : Babu hatsi ba kuÉ—É—in saye,

    : Matanai sun firgita,

    : Sun ce duk sun fita,

    : Agaji raggo tun yinwar ga,

    : Danye ya ci,

    : Bagudu don Allah,

    : ÆŠan ‘yam mashi rogo,

    : ÆŠanye ya ci,

    : Ya É—au kwashe,

    : Za ya ginar sanyun kirshiya,

    : Da yay noma yaÉ— É—ebe,

    : Ƙalilan yag gurgura,

     ‘Y/Amshi : Sai yac ce sayenta,

    : Ashe Æ™aiÆ™ai  ag garai.

    : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

    Jagora: Ran batun ilimin nan,

    : Za’a biÉ—ar babban malami,

    : Wurin Noma nan za’a biÉ—am,

    : Mai ƙarfi ya zo.

     ‘Y/Amshi : Mu kama kiÉ—i,

    : Mu kam haka Allah,

    : Yay yo da mu.

     

    Jagora  : Kai mu kama kiÉ—i,

    ‘Y/Amshi : Mu kan haka Allah,

    : Yay yo da mu.

    : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

      Jagora  : ÆŠan Mani ka gaji bajinta,

    : Wajen uwa,

    : Ni kuma ba samnan, 

      ‘Y/Amshi: MakaÉ—i nah haihoni ba,

     

    Jagora : Na gode Adamu Abdullahi Kanoma,

    : Dogo ba’a canye ka ga,

    : Aikin radiyo ba.

      ‘Y/ Amshi: Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

     Jagora: To na aje roÆ™o gidan,

    : Bahili[10] mi ag garai?

    : Garkar mai miƙa mini

    : In ba ni

    : To na aje roƙo gidan

    : Bajinta mi ag garai

    : Garkar mai miƙa mini

    : Can munka yi.

    ‘Y/Amshi: Sarkin Noma

    : Mai hana aikin gona Ya kwan

    : Matsa a gama manya

    : Makasa sabra ÆŠan Abu

     

      Jagora: Na Magajin Gari,

    : Mijin Jaɓɓo,

    : Da Inno da Hauwa cikakken mutum,

    : Allah bai yo Alhaji,

     ‘Y/Amshi : Samnan dattijo ba,

    : Wahabu Allah bai yo Alhaji,

    : Samnan dattijo ba.

     

     Jagora: Imani ya kamala,

    : Guri na ya cika,

    : Kamar ya je sallah,

    : Haji ya samu gida Gusau.

    ‘Y/Amshi: Wuri shidda garai,

    : Kowa ne kau ba É—an tsito[11] ba,

    : Kowa ne wuri an É—ebi,

    : Buhun shinkafa É—ari,

    : Wanga guri an É—ebi,

    : Buhun shinkafa É—ari,

    : Ni na san mota,

    : Aka É—aukar ranar jida.

      ‘Y/Amshi: Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona yakwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

     Jagora: Gabas da Mayanci,

    : Ba su da daji ko dan kaÉ—an,

     ‘Y/Amshi  : Sarkin Noman yamma,

    : Ga kwalta ya sassabe.

    : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona yakwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

     Jagora: Da ya noma hatsi nai,

    : Ya fitar da haƙƙin[12] Rabbana,

    : Ba ya barin sai masu bidar,

    : Zakka sun  matsu.

     ‘Y/Amshi: Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu,

     

     Jagora: Da ya darme hatsi nai,

    : Ya fit da hakin Rabbana,

    : Ba ya barin sai masu biÉ—ar,

    : Zakka sun matsu,

    : Ya nuna man Isa,

    : Jikan Jatau halin bajin ta,

    : Shi yay yi man,

    : Zaman ya ba Audun,

    : Baraka kyautar goÉ—iya.

     ‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

     Jagora: Ginjimin Tukur ka ban goÉ—iya,

    : Baban su Kabiru,

    : Sake miƙa man Raƙumi,

    : Na nemi akala,

    : In riƙa ɗaukar kaya da shi.

     ‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.

     

    Jagora: Haruna ÆŠan Mani,

      ‘Y/Amshi: Barkak ka da yaÆ™in,

    : Tausar yama,

    : Ga wag ga ƙasa dum,

    : Mai riƙa kalme,

    : Ya san da kai.

    : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra[13] ÆŠan Abu.

     

      Jagora: Mijin JaÉ“É“o da kay yi man wasiÆ™a,

    : Ta kai garan.

    : Na san alheri muka samu,

    : In mun ka zo.

    : Mai gidan Inno ka yi min wasiƙa,

    : Ta kai garan,

    : Na san alheri muka samu,

    : In mun ka zo.

    ‘Y/Amshi : Sarkin Noma,

    : Mai hana aikin gona ya kwan,

    : Matsa a gama manya,

    : Makasa sabra ÆŠan Abu.



    [1]  Hidima/Sha’ani.

    [2]  Saunan mutun wato raggo wanda bai iya noma abincinsa.

    [3]  Sare ‘yan itatuwa da ciyayi domin a gyara gona don noma.

    [4]  Saboda.

    [5]  Matashiyar macen doki.

    [6]  KuÉ—i.

    [7]  Halayya.

    [8]  Maccen doki.

    [9]  Igiyar da ake É—aura wa raÆ™umi ana ja.

    [10]  Raggo

    [11]  KaÉ—an

    [12]  Zakka.

    [13]  Wurin da ba a noma ba wanda hakukuwa suka fito daba-daban.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.