Haruna

    Citation: Bungudu, H. U. (2023). ZaÉ“aÉ“É“un waÆ™oÆ™in mawaÆ™an baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bungudu
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Noma

    Haruna

     

    G/Waƙa: Yai halin girma,

    : Yai halin yabawa,

    : Haruna ya hi mano,

    : Ma biÉ—an na kainai.

     

    Jagora: Gidan Haruna,

    : Za ni yo kiÉ—ina,

    : Mai kai dare..,

      ‘Y/ Amshi: Mai kai dare daji,

    : Baya tadda[1] kainai.

    : Yai halin girma,

    : Yai halin yabawa,

    : Haruna ya hi mano,

    : Ma biÉ—an na kainai.

      Jagora: Amman na zaÉ“i mai iko,

    : Korau É—iyan manoma,

    : In damana ta komo

    : Ku kama hauya,

    : Kun san rayuwa,

    : Rannan ba zama akai ba,

    : In ana noma,

    : Ba zama akai ba.

    : Rannan mai zaman saƙa,

    : Shina wahalsa  kainai,

    : Kuma mai hwarauta,

    : Ba sassabe[2] yakai ba,

    : Rannan mai zaman dara,

    : Wannan ba shi fara binne

    : To maza ku É—au kalme,

    : Ko kuÉ—auki kwasa,

    : Kui sassabe daji,

    : Kui kashe kalage,

    : To É—an da bai da dame,

    : Mace ba ta so nai

    ‘Y/ Amshi: Bai da dame[3],

    : Macce ba ta so nai.

     

     Jagora: To É—an da bai da hura,

    ‘Y/ Amshi: Macce bata so nai.

    : Yai halin girma,

    : Yai halin yabawa,

    : Haruna ya hi mano,

    : Ma biÉ—an na kainai.

     

     Jagora: Ka san kowal aje,

    : Mata baabin dakawa,

    : Kun san shina cikin wahala,

    : Ta zakkona ishe mai.

    : Ko can batun Allah,

     ‘Y/ Amshi: Ko can batun Allah,

    : Babu mai hanawa.

    : Yai halin girma,

    : Yai halin yabawa,

    : Haruna ya hi mano,

    : Ma biÉ—an na kainai.

     

     Jagora: Sannan Arabazan ko,

    : Mawa can na tana nan,

    : Ka san Haruna na gode.

    : Garba yamiƙa min.

    : Don ya bada ingarma,

    : Tungar mai hwarin ƙahwahu

    : Sannan Gidan kuru,

    : Zan sauka Haruna na nan.

    : Shi Haruna nagode,

    : Ya biya kiÉ—ina.

    : Sannan zani na Zango,

    : In gano manoma,

    : Allah shi bar Labaran,

    : Mai halin yabawa,

    : Allah..

    ‘Y/ Amshi: Ya hi mu yaba

    : Wa ya bam mu tare,

    : Yai halin girma,

    : Yai halin yabawa,

    : Haruna ya hi mano,

    : Ma biÉ—an na kainai.

     Jagora: Sannan ka hwaÉ—a ma raggo,

    : Bana bai

    : San halin Rugum ba,

    : Don kun ga ‘yan makaÉ—a,

    : Sai ku ce Rugum na,

    : Kuma had da masu duma,

    : Had da mai kalangu,

    : Dud dai inda sun yi kiÉ—i,

    : Sai a ce Rugum na,

    : Kuma had da mai,

    : Kotso

    : Sai a ce Rugum na,

    : Kuma had da mai,

    : Taushi sai a ce Rugum na,

    : Kuma had da mai,

    : Ganga

    : Sai a ce Rugum na,

    : Kuma had da mai,

    : Goge sai a ce Rugum na.

    : Mai gunduwa[4] ka kiÉ—i,

    : Sai a ce Rugum na,

    : Kuma had da mai,

    : Kwamsa sai a ce Rugum na,

    : Kuma had da mai,

    : Gora sai a ce Rugum na,

    : Kuma had da mai,

    : Goge sai a ce Rugum na,

    : Kuma had da mai,

    : Kuntugi

    : Sai a ce Rugum na,

    : Ka san ni ar Rugum,

    : Da gani babu tambaya ba,

    : Ka san ni ar Rugum,

    : Yarana Rugum suna nan,

    : Kun san karonmu sai manya,

    : Sai gidan saraki[5],

    : To É—an da..

      ‘Y/Amshi: ÆŠan da yad dace,

    : Bisa duniyag ga,x2

    : Yai halin girma,

    : Yai halin yabawa,

    : Haruna ya hi mano,

    : Ma biÉ—an na kainai.

     

     Jagora: Amma ni zan kiÉ—i Gumi,

    : Don in gano manoma,

    : Ka san Bello na gode,

    : Ya biya kiÉ—ina,

    : ÆŠan noma mai abin noma,

    : Shina da kyuta,

    : Dub Bello ÆŠan Jabiri,

    : Ya biya kiÉ—ina,

    : Dub Bello mai,

    : Gona wadda ba irin ta,

    : Sannan ni zan Tsarna,

    : Za ni sauka,

    : Tsarnawa na yi kiÉ—i,

    : Don Haruna na nan,

    : Ka san Haruna shid[6] da gida,

    : Wanda ba iri nai.

    : Allahx2

    ‘Y/ Amshi: Allah ya hi mu yabawa,

    : Ya bar nu tare,x2

    : Yai halin girma,

    : Yai halin yabawa,

    : Haruna ya hi mano,

    : Ma biÉ—an na kainai.

    Jagora: Dan nan Debetu zan,

    : Koma wa ÆŠanladi na can,

    : Ka san ÆŠanladi na gode,

    : Ya biya kiÉ—ina,

    : Amma Ma’azu na gode,

    : Shi ya biya kiÉ—ina,

    : Dan nan Turanki zan,

    : Koma wa gidan manoma,

    : In na ga ÆŠan’indo,

    : Bani shan takaici[7],

    : Allah,

    ‘Y/ Amshi: Ya Æ™ara yabawa,

    : Ya bam mu tare,

    : Yai halin girma,

    : Yai halin yabawa,

    : Haruna ya hi manoma,

    : BiÉ—an na kainai.

     

     Jagora: Amma maza inai maku,

    : Horo É—iyan manoma,

    : Ka san ni yadda ba ni kiÉ—i,

    : Sai kiÉ—in manoma,

    : Amma kiÉ—in hura,

    : Mai daÉ—i ga ‘yan manoma.

    : Amma ga wanda ya aje,

    : Gero cikin rihenu[8],

    : Amma ka hwaÉ—a ma raggo,

    : To bana sai,

    : Ya ji ƙwal ga kainai,

    : To É—an Karen shege,

    : Ba mu ba ka kyauta,

    : Yai halin girma[9],

    : Yai halin yabawa,

    : Haruna ya hi mano,

    : Ma biÉ—an na kainai.



    [1]  Kulawa ko damuwa, ma’ana dai hankalinsa a kwance..

    [2]  Gyara gona ta hanyar sassare kututturai da tottohi.

    [3]  Daurin hatsi wanda ake É—aurawa idan za a É—auko daga gona zuwa gida.

    [4]  Wata ‘yar ganga ce da ake kiÉ—in nomad a ita wadda ba ta kai girman gangar noma ba.

    [5]  Masu sarauta.

    [6]  Shi ke da.

    [7]  Haushi/jin kunya.

    [8]  Rumbuna.

    [9]  Kyauta/kyautatawa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.