Hashimu Uban Maza

    Citation: BunguÉ—u, U.H. (2022). WaÆ™oÆ™in Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Amali  Sububu

    Hashimu Uban Maza

    Hashimu Uban maza ɗan garin Tcibiri ne ta yankin Maradun ta jihara Zamfara. Yana da ƙaƙarin aikin gona don haka Amali ya yi masa waƙa.

     

        G/WaÆ™a : In zo mu ga hashimu uban maza,

    : Namijin ƙwazo ba shi gasuwa.

     

    Jagora: Hashimu guda ne muka gani,

    ‘Y/Amshi: In za ku hwaÉ—a mana ina wani?

    : Namijin ƙwazo ba ka gasuwa,

    : In zo mu ga Hashimu Uban maza.

     

    Jagora: Gyado tahi duƙe ga gaban ƙasa.

    ‘Y/Amshi: Mu gane ka idonka na masassari[1],  

    : Namijin ƙwazo baka gasuwa,

    : In zo mu ga Hashimu Uban maza.x2

     

    Jagora: Shi dai gona ba ta É—auke noma nai,

      : Sai dai karkara isa noma,

      : Ko ‘Yah Hali ba ta nan,

      : Balle kuma ‘Yah Hali na kusa,

      : In ya nome ita ka hizge hannunai,

      : Ta yo gida da shi,

      : To in bata tarbe ba ba shi dawowa birni,

      : Mi yakai gida?

      ‘Y/Amshi: Sai dai ya shige dawa kamad damo.

    : Namijin ƙwazo ba ka gasuwa,

    : In zo mu ga Hashimu Uban maza.

     

     Jagora: Gyado[2] tahi gicce ga gaban Æ™asa.

      ‘Y/Amshi: Mu gane ka idonka na masassari[3],

    : Namijin ƙwazo baka gasuwa,

    : In zo mu ga Hashimu Uban maza.

     

     Jagora: Sabon gero mai tagomashi ÆŠanmantu,

      : Abin zaman gari,

      : Danginka suna kwaÉ—an zama da kai,

      : DattiÉ“e suna kwaÉ—an zama da kai,

      : ‘Yan yara suna kwaÉ—an zama da kai,

      : Matanka suna kwaÉ—an zama da kai,

      : Mai son ka yana kwaÉ—an zama da kai,

      : Yau kowac ce ba ya son ka ya saÉ“a,

      : Ba shi ne da ranka ba.

       ‘Y/Amshi: Balle ya hana maka ka kwan biyu.

    : Namijin ƙwazo ba ka gasuwa,

    : In zo mu ga Hashimu Uban maza.

      Jagora: Ko can giwa ita ka haihuwag giwa,

    : Kowa na ganin kama,

    : Ita dai kura ba mu san bunsurunta ba,

       ‘Y/Amshi: Sai dai ta hi huskata[4] karen É“uki,

    : Namijin ƙwazo ba ka gasuwa,

    : In zo mu ga Hashimu Uban maza.

     

      Jagora: Shi ya aika in taho garai,

    : Ban samu zuwa ba,

    : Sai da anka kwana biyu,

    : Yac ce ban gane ka ba,

    : Ni ko nic ce gani nan tahe,

    : NiÉ— É—auki duma ni azo ma barwaina,

    : Dan nan nis shigo gaba,

    : Han nij ji ana gardama gari,

    : Wasu na cewa ga Amali can,

    : Wasu ko sun ce ba Amali ne ba,

    : A a abin can Amali ne yad danno,

    : Koje uban É—umi,

    : WaÉ—anga da nac ce Amali ne sun kayat,

    : Su nay yi hankali,

    : Dan nan daÉ—a nig gangaro gari,

    ; Yab ba mu hura sai da munka bat ta gari,

    : Yac ce bat ta nan ku sha,

    : Yab ba mu tuwo sai da munka bas shi gari,

    : Yac ce bas shi nan ku ci,

    : Sannan ga goronmu ya isa,

    : Sannan ga tabammu ta isa,

    : Sannan kuma yab ba ni tagguwa[5],

    : Ka san kau taggon ga ya hi riga,

    : Ko an É—unke shi tagguwa,

    : Wata ‘yar riga ba ta kai garai,

    : Yab ban naira arba’in da shidda mu É—auka,

    : Mu sai ruwa mu sha,

    ‘Y/Amshi: Yac ce a haÉ—a muna mu tai gida.

    : Namijin ƙwazo ba ka gasuwa,

    : In zo mu ga Hashimu Uban maza.

     

    Jagora: Kowa aika nit taho garai,

    : Ko ya ba ni kaÉ—anna,

    : Ba ni rena girma nai,

    : Sai dai in yi mai kaÉ—an,

    : Marai nike mai kirmtcin É—umi ÆŠan Isah,

    : Koje uban batu,

    : Suda nike mai sintirin É—umi ta-ta-ta,

    : Had dai ta hihhika.

    ‘Y/Amshi: DaÉ—in maganammu da Æ™araurawa,

    : Namijin ƙwazo ba ka gasuwa,

    : In zo mu ga Hashimu Uban maza.x2

     

    Jagora: Dab bakin yaƙi ana ganin yunwa,

    : Amma ba a ga tcada ba,

    : Dag kakanninmu har uwayenmu,

    : Kowa bai ga tcada ba,

    : Bakin tsaba duk tiya ta kai sitta,

    : Dan nan ai ta hanƙuri,

    : Dan nan kuma har anka sa tarau[6],

    : Dan nan tak Koma sule biyu,

    : Dan nan kuma har anka sa tarau,

    : Yanzu tiya ba ta taɓuwa,

    : Kaman naira shidda za ka cin kwano,

    : Amma ba na cin dare,

    : Duniyar ba mu gane ma kanta ba,

    : Wasu na tashi suna barin ƙasa,

    : Wasu na Komowa zuwa gida,

    : Wasu kau sun dai ɗauki hanƙuri,

    : Duniya ba a gane ma kanta ba,

    : Allah ya bamma kainai sani,

    ; Kowa na aikin rashin gani.

    ‘Y/Amshi: Allah ka aza mu ga abin Æ™warai.

    : Namijin ƙwazo ba ka gasuwa,

    : In zo mu ga Hashimu Uban maza.

     

    Jagora: Hashimu guda ne na Tcibiri[7],

    : Hashimu guda ne munka gani.

    ‘Y/Amshi: In zaku hwaÉ—a mana ina wani?

    : Namijin ƙwazo ba ka gasuwa,

    : In zo mu ga Hashimu Uban maza.

     

         Jagora: Bana an yi hwari[8] munka sha wuyar noma,

    : Kwana arba’in da É—ai ba sanyi,

    : Muna ganin wuya,

    : Ga gero duk kunnuwashi sun bushe,

    : Kowa na ta zullumi.

    ‘Y/Amshi: Namijin Æ™wazo ba ka gasuwa[9],

    : In zo mu ga Hashimu Uban maza.



    [1]  Idanu suna kamar su rufe saboda wahala.

    [2]  Wata dabba ce mai haÆ™ora zago-zago, yana amfani da haÆ™oransa ne wajen tonon Æ™asa.

    [3]  Ƙifce-Æ™ifcen ido.

    [4]  Fuskantar, ta fi yin kama da wani abu.

    [5]  Yadin da zai É—unka sutura.

    [6]  Kwabo da É—ari.

    [7]  Sunan wani gari ne a jamhuriyar Nijer.

    [8]  Yankewar ruwan sama a lokacin damina, wanda kan sa yabanya ta fara bushewa don rashin ruwa.

    [9]  Ba a iya gasarsa wajen aiki.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.