𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh.
menene hukunchin wanda yawu yake taruwa a bakinsa koda yana sallah?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh
Wanda yawu yake taruwa acikin bakin sa a lokacin
da yaje yana a halin sallah babu komai akansa in shaa Allah, domin taruwan yawu
a bakin mai yin sallah baya daga cikin abubuwa da suke ruguza sallah ko su
karhantar da ita don haka babu komai akansa in shaa Allah, sai dai saboda
yanayin karatun wanda yawu ya taru a bakin sa ba lallai bane ya fita dakyau
yadda ake bukata to sai ya samu wani kyalle mai kauri karami wanda yasan zai
iya yin amfani dashi wajen cire yawun daga cikin bakin sa ba tare da yayi motsi
mai yawa ba ta yadda zai zamana cewa karatun sallar sa yana fita kamar yadda
ake bukata, kuma muna addu'ar Allah ya bashi lafiya domin wannan yana da alaƙa da rashin lafiya sai a bibiyi masana
harkan lafiya in shaa Allah za'a samu abinda zai takaita faruwan hakan akai
akai koda ba a daina ba gaba daya Allah ne mafi sani
Ustaz Hussaini Haruna Kuriga
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/IƘUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.