Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Isah Kure
G/Waƙa
: Akwai hura gidanai,
:
Yana tsaye da hure[1].
Jagora: Akwai hura gidanai,
:
Yana tsaye da hure.
‘Y/
Amshi:
Akwai hura gidanai,
:
Yana tsaye da hure.
Jagora: Kure mai abin rabo,
‘Y/Amshi:
Ko wata yag hwaɗi a ɗauka,
Jagora: Kure mai abin daka,
‘Y/Amshi: Ko wata hwaɗi a ɗauka.
Jagora: Yaro gahwarak ka ga,,
‘Y/Amshi: Manya sun taho ga aiki.x2
Jagora: Barau na goɗe,
‘Y/ Amshi: Wata’ala ya taimake shi,
Jagora: Sarkin shanu ka biya,
‘Y/
Amshi:
Wata’ala ya taimake shi.
Jagora: Alhaji Babawo ka
biya,
‘Y/
Amshi:
Wata’ala ya taimake ku.
:
Akwai hura gidanai,
:
Yana tsaye da hure.
Jagora: Bari roƙon
jini ga sa,
‘Y/ Amshi: Rannan ba jinni garab[2]
ba,
Jagora: In don kyauta gida garat,
‘Y/
Amshi:
Ko rowa gida gareta..
Jagora: Ku san kyauta tana
dad aɗi,
‘Y/
Amshi:
Ko rowa tana da zahi.
:
Akwai hura gidanai,
:
Yana tsaye da hure.
Jagora: Kowas samu duniya,
‘Y/ Amshi: Ya ci gad duniya ta ci shi.
Jagora: Kowas samu duniya,
‘Y/ Amshi: Shi ci gad duniya ta ci shi.
Jagora: Bari mu ci ki duniya.x2
‘Y/Amshi: Kandan duniya ki ci mu.x2
:
Akwai hura gidanai,
:
Yana tsaye da hure.
Jagora: Gero na gidanka Isah,
‘Y/
Amshi:
Yau kowat taho a ba shi,
Jagora: Dawa na gidanka Dule,
‘Y/
Amshi:
Yau kowat taho a ba shi.
Jagora: Masara gata nan ga Isah,
‘Y/
Amshi:
Yau kowat taho a ba shi.
Jagora: Kowake da shi da,
‘Y/Amshi:
Shinkahwa gashi nan gidanku.
Jagora: Yaro gahwarak ka
ga,
‘Y/
Amshi:
Manya sun taho ga aiki.
:
Akwai hura gidanai,
:
Yana tsaye da hure.
Jagora: Tafi gona biɗah hatci,
‘Y/ Amshi: Kowayai shi za ya samo.
Jagora: Tafi gona biɗah hura,
‘Y/ Amshi: Kowayai shi za ya samo.
Jagora: Ga makaɗin ɗiya nan,
‘Y/
Amshi:
Sauna ban zuwa gidansu,
:
Akwai hura gidanai,
:
Yana tsaye da hure.
Jagora: ‘Yan Keratsa ku ka noma,
‘Y/Amshi:
Wata’alah ya taimake su.
Jagora: ‘Yan Keratsa kun biya,
‘Y/ Amshi: Wata’alah ya taimake su.
Jagora: Gidan zago za ni
na kiɗi,
‘Y/ Amshi: Don Allah tsaya mu samo.
Jagora: Ko Usumanu ya biya,
‘Y/Amshi: Wata’ala Ya taimake su.
Jagora: Ga Ummaru Manu ya biya,
‘Y/Amshi: Wata’ala Ya taimake su.
Jagora: Usmanu ya biya kiɗi,
:
Wata’ala ya taimake su.
‘Y/
Amshi:
Wata’ala ya taimake su.
Jagora: Jikan Magaji na gode,
‘Y/
Amshi:
Ya biya buƙata.
Jagora: Jika ka biya kiɗi,
‘Y/ Amshi: Wata’ala ya taimake su.
:
Akwai hura gidanai,
:
Yana tsaye da hure.
Jagora; Zango zani na kiɗi,
‘Y/
Amshi:
Wata’ala Shi taimake su,
Jagora: Sarkin noma ya biya kiɗi,
:
Jikan Magaji na gode,
Jagora: Adamu ka ga ɗan ɗane naia,
‘Y/ Amshi: Wata’ala shi taimake su.
Jagora: Muhammadu ka biya
kiɗi,
‘Y/ Amshi: Wata’ala ya taimake su.
Jagora: Musa ka biya kiɗi,
‘Y/ Amshi: Wata’ala ya taimake su.
:
Akwai hura gidanai,
:
Yana tsaye da hure.
Jagora: Ni dai zan kiɗi Turus,
‘Y/ Amshi: Domin in biya buƙata.
Jagora: Isahn Maidawa shi da Idi,
‘Y/ Amshi: Wata’ala ya taimake su.
Jagora: Ɗanbara ya biya kiɗi,x2
‘Y/ Amshi: Wata’ala ya taimake su.x2
:
Akwai hura gidanai,
:
Yana tsaye da hure.
Jagora: Garba Abubakar ka kyauta,
‘Y/ Amshi: Wata’ala ya taimake su.
:
Akwai hura gidanai,
:
Yana tsaye da hure.
Jagora: Tafi gona biɗah hura,
‘Y/ Amshi: Kowa yai shi za ya samo.
Jagora: Tafi gona biɗah[3]
hatci,
‘Y/ Amshi: Kowa yai shi za ya samo.
:
Akwai hura gidanai,
:
Yana tsaye da hure.
Jagora: Kowab bani in hwaɗi,x2
‘Y/ Amshi: Don kwab bani ba yawaige.x2
:
Akwai hura gidanai,
:
Yana tsaye da hure.
Jagora: In dai maganin
maza,
: Ɗalha
‘Y/ Amshi: Wata’ala ya taimake su.
Jagora: Ɗalha ya biya kiɗi.x2
‘Y/
Amshi:
Wata’ala ya taimake su.x2
Jagora: Sarkin noma ya biya kiɗi.
‘Y/ Amshi: Wata’ala ya taimake su.
Jagora: Na gode ma Garba mai kuɗi.
‘Y/ Amshi: Wata’ala ya taimake su.
:
Akwai hura gidanai,
:
Yana tsaye da hure.
Jagora: Tafi gona biɗah hura,
‘Y/ Amshi: Kowa yai shi za ya samo.
:
Akwai hura gidanai,
:
Yana tsaye da hure.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.