Isuhu Direba

    Citation: BunguÉ—u, U.H. (2022). WaÆ™oÆ™in Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Amali  Sububu

    Isuhu Direba

    Isuhu wato Yusuf direba asalinsa mutumen garin Gatawa ne, amma dai a halin yanzu ya koma da zama a Sabonbirni ta cikin jihar Sakkwato,  A lokacin da Amali ya yi masa waÆ™a direban wata mota ne da ake kira DALTA buÉ—aÉ—É—iya wadda ake É—aukar kaya da ita.  A wancan lokacin an ce babu wanda ya fi shi gudu da mota saboda Æ™warewarsa da tuÆ™in motar. Yana nan da ransa kuma yana sana’arsa ta tuÆ™in mota. Ga waÆ™ar tasa kamar haka:

     

       G/Waka  : Da gaskiya yaka sa mota tahiya,

    : Da lambobin gudu,

     

     Jagora: Da gudu Æ™warai da rashin gudu,

       : Radda kwana nac cika,

    : Tahiya garin kewa[1]akai.

     ‘Y/Amshi: Da gaskiya yaka sa mota tahiya,

    : Da lambobin gudu,

       : Allah ya tsare da tsarewa,

    : Tai ka gama da kowa lahiya.

     

     Jagora: Da gudu Æ™warai da rashin gudu,

       : In dai da kwana duniya,

    : Ai ba a kwana lahira.

      ‘Y/Amshi: kuma radda kwana naccika,

    : Tahiya garin kewa a kai.

     

     Jagora: Sai wataran da ku yan gasawa,

       : Tahiya gida na zani yi,

    ‘Y/Amshi: Tahiya gida na zani yi,

    : Jama’ag ga sai kuma an jima.

     

    Jagora  : In dai magana ta jan mota ce,

       : In dai magana ta cin hanya ce,

       : In dai magana ta jan Æ™arhe ce,

       : Issuhu ya yi malin[2] kowa.

    ‘Y/Amshi: Ba mota ba sai jirgin sama,

       : Da gaskiya yaka sa mota tahiya,

    : Da lambobin gudu,

       : Allah ya tsare da tsarewa,

    : Tai ka gama da kowa lahiya.

     

       Jagora  : Wanga irin yaro da gaugawa kake,

    ‘Y/Amshi: Wanga irin yaro akwai sarmin[3] kwana,

     

       Jagora  : Wanga irin yaro akwai sarmin kwana.

    ‘Y/Amshi: Wanga irin yaro da gaugawa yake.

       

    Jagora  : In ya kai wuri mai turÉ—a,

    : Issuhu hihhikawa[4] za yai,

    ‘Y/Amshi: Ba ya aje ta sai in ya wuce,

       : Da gaskiya yaka sa mota tahiya,

    : Da lambobin gudu,

      : Allah ya tsare da tsarewa

    : Tai ka gama da kowa lahiya.

     

     Jagora  : Wani mai tebur da yaj ja gardama,

       : Shinkafi yaj ja gardama ,

       : Kuma zaya kai kaya Kano,

       : Issuhu ya shigo mota tai,

       : Shi ma za shi kai kaya Kano,

       : Yaro tsaya sai na wuce.

    ‘Y/Amshi: Shi ko yac ce Oga[5] Æ™arya kakai,

     

    Jagora: Dan Yaro tsaya sai na wuce,

    ‘Y/Amshi: Shi ko yac ce Oga shi ak kure,

     

     Jagora  : An ka zuba ta hilin godabe,

       : Mai tebur yana bisa titi,

       : Sai taya guda É—ai ta hwashe,

       : Bai daina ba sauri É—ai yakai.

    ‘Y/Amshi: Samri[6] É—ai yakai,

    : Taya guda kuma ta hwashe,

     

     Jagora  : Mun ka wuce shi Ƙaura ya tsaya,

       : Ya raÉ“a Dauran yaw wuce ,

       : Yar raÉ“a Gurbi yaw wuce,

       : Bai tswalka[7] ba hay yak kai Kano,

       : Ummaru ya riÆ™e mashi hannu.

    ‘Y/Amshi: Don Allah tsaya ka kai Kano.

     

    Jagora  : Sai dai munka dubi agogonai,

    ‘Y/Amshi: Minti biyar yaz zo Kano.

       : Da gaskiya ya kasa injin tahiya,

    : Da lambobin giya,

       : Allah ya tsare da tsarewa,

    : Tai ka gama da kowa lahiya.

     

    Jagora  : Rannan na ishe shi yana hutawa,

       : Ya yi zanne cikin gida,

    : Yac ce taho magana nikai.

       : Ni ko da nit tahi nib biya,

       : Ni ko da nittahi nib biya,

       : Ya ce ina maganak kiÉ—i?

       : Na ce akwai maganak kiÉ—i,

       : In dai sakin waÆ™a ne,

    : Kan da bakwai guda ƙarya ni kai,

       : To kai ! ina maganar gudu?

       : Ya ce akwai maganar gudu,

       : Amali ko ka san awa ?

       : Na ce da shi na san awa.

     

     Jagora: In niy yi awa ban kai ba Kano,

    : Ce ba ni bangon duniya.

        ‘Yan Amshi  : In niy yi awa ban kai ba Kano,

    : Ce ba ni bango duniya.

      : Da gaskiya yaka sa mota tahiya,

    : Da lambobin[8]gudu,

       : Allah ya tsare da tsarewa,

    : Tai ka gama da kowa lahiya.

     

    Jagora  : Mai hijo[9] sakam muna hili.

    ‘Y/Amshi: Bai tahiya da shi Æ™arya yakai.

     

    Jagora: Mai datsun É—aga muna kai ma.

    ‘Y/Amshi: Bai tahiya da shi Æ™arya ya kai.

     

     Jagora: Mai balbo É—aga muna kai ma.

    ‘Y/Amshi: Bai tahiya da shi Æ™arya ya kai.

     

    Jagora  : Mai sharido shi yam muna hili,

    ‘Y/Amshi: Bai tahiya da shi Æ™arya yakai.

     

     Jagora  : Har mai roka ya yam muna hili,

    ‘Y/Amshi: Bai tahiya da shi Æ™arya yakai.

     

    Jagora  : Ku ji dinka[10] tana kumburi ga banza.

    ‘Y/Amshi: Mun ka wuce su bayan Moriki,

       : Da gaskiya yaka sa mota tahiya,

    : Da lambobin gudu,

       : Allah ya tsare da tsarewa.

       : Tai ka gama da kowa lahiya.

     

    Jagora  : Sai wataran da ku yan  Gatawa,

       : Tahiya gidana za ni yi.

    ‘Y/Amshi: Tahiya gidana za ni yi ,

       : Jama’ag ga sai kuma an jima,

       : Da gaskiya yaka sa mota tahiya

    : Da lambobin gudu,

       : Allah ya tsare da tsarewa,

       : Tai ka gama da kowa lahiya.



    [1]  Lahira.

    [2]  Fi/tserewa, maganar fifiko ce.

    [3]  Sauri /hanzari/Gaggawa.

    [4]  Tashi sama.

    [5]  Maigida.

    [6]  Sauri/hanzari yin abu da gaggawa.

    [7]  Wato bai sami wani É“acin rai ba wanda ya sa shi ya yi tswaki.

    [8]  Giyar mota kenan wato ta É—aya har zuwa ta huÉ—u, ko ta biyar ko ma fiye ga waÉ—ansu motocin.

    [9]  Mota Fujo.

    [10] Sunan wata mota ne wadda ake kira C.20 sai mutane suke kiranta kumburin Dinka.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.