Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Iyalin Ɗan jumma
G/Waƙa: Ya riƙa
gona da anniya,
: Ga
Hashimu Ɗan Labbo niz zaka.
Jagora: Hirgita gona ƙanen
magaji.
‘Y/ Amshi: A bar maka noma ka yi ta yi,
: Ya
riƙa gona da anniya,
: Ga
Hashimu Ɗan Labbo niz zaka.
Jagora: Ɗanlamso Ɗan
Tashikka Ɗan Shawai.
‘Y/ Amshi: Ɗan
Tashuka Ɗan Shawai.
: Biɗi kwashe[1]
ka yi zahwa[2],
: Ya
riƙa gona da anniya,
: Ga
Hashimu Ɗan Labbo niz zaka.
Jagora: Ga iyalin Ɗan
jumma nit taho,
‘Y/ Amshi: Sun san riƙa
turu da ƙa’ida.
Jagora: In hairan na yi duniya.
‘Y/ Amshi: Duk tare da Ɗan
jumma niy yi shi.
Jagora: Kuma in sheri niy yi duniya.
‘Y/ Amshi: Dut tare da Ɗan
jumma niy yi shi.
Jagora: Lalle in sheri niy yi duniya.
‘Y/ Amshi: Dut tare da Ɗan
jumma niy yi shi.
: Ya
riƙa gona da anniya[3],
: Ga
Hashimu Ɗan Labbo niz zaka.
Jagora: To na yi saduda da hamdala,x2
‘Y/ Amshi: Hasken ‘yan gayya da ya
wuce,
:
Allahu ya gammai[4] da
gafara,
: Ya
riƙa gona da anniya,
: Ga
Hashimu Ɗan Labbo niz zaka.x2
Jagora: Ɗan lamso ɗan Tashuka Ɗan
Shawai.
‘Y/ Amshi:: Biɗi kwashe ka yi
zahwa[5].
Jagora: Kowa yazo kasuwa ranar juma’a,
‘Y/ Amshi: Ya san zahwa ta gyra duniya.
Jagora: Da akwai rogo naga dankali.
‘Y/ Amshi: Hat tare da janjare[6]
zay yawa,
: Ya
riƙa noma da anniya,
: Ga
Hashimu Ɗan Labbo niz zaka.
Jagora: Ga iyalin Ɗan
Jimma nit tahho.
‘Y/ Amshi: Sun riƙa
turu da ƙa’ida[7].
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.