Jibo Mai Ruwan Gabas

     Citation: Bungudu, H. U. (2023). ZaÉ“aÉ“É“un waÆ™oÆ™in mawaÆ™an baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bungudu
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Noma

    Jibo Mai Ruwan Gabas

      G/WaÆ™a: Bai tsaya gida ba,

    : Ya wa gona dirar kago[1],

    : Ya nome ta.

     

    Jagora: Bai tsaya gida ba,

    : Ya wa gona dirar kago,

    : Ya nome ta.

      ‘Y/ Amshi: Bai tsaya gida ba,

    : Ya wa gona dirar kago,

    : Ya nome ta.

     

      Jagora: Sai dare Æ™anen Ba’u.

    ‘Y/ Amshi: Mijin Ba’u ne,

    : Mijin ƙwairon ganga.

     

      Jagora: Ƙwairo ko miji,

    :Ya ji daÉ—in aure.

    ‘Y/ Amshi: Ai ba ya ce ma matatai Inna.

     

      Jagora: In mace bata son ka,

    : Kai kac ce ka so ta,

    : Gwadin saiɓi[2] kenan,

    : Sai ta sa ka suma.

    ‘Y/ Amshi: Kana ta raki

    : Tana hwaÉ—in na rena ka.

    : Bai tsaya gida ba,

    : Ya wa gona dirar kago,

    : Ya nome ta.

     

      Jagora: Ta Bunu É—anki yai doki,

    : Ki yi guÉ—a.

    ‘Y/ Amshi: Ki kau aza man,

    : Sirdina.

     

    Jagora: Damu ki bada kahu.

    ‘Y/ Amshi: Ham mai Æ™arhi yana licin kawo,

     

      Jagora: Hassi da a uwaÉ— É—a.

    ‘Y/ Amshi: Bada jalala[3] takai,

    : Sabo licin[4] ƙauna.

    : Bai tsaya gida ba,

    : Ya wa gona dirar kago,

    : Ya nome ta.

     

     Jagora: Mai zwarin[5] wuri magajin.

    ‘Y/ Amshi: Malam mai zwarin wuri,

    : Magajin ÆŠanhawwa.

    : Bai tsaya gida ba,

     

      Jagora: A gaida jibo,

    : Mai ruwan Gabas.

    ‘Y/ Amshi: Bardoki a gaida jibo,

    : Mai ruwan Gabas,

    : Na gode ma.

    : Bai tsaya gida ba,

    : Ya wa gona dirar kago,

    : Ya nome ta.

     

      Jagora: Mai garaya da yas sha yunwa,

    : Sai ya biya gidan Sodo,

    : Sai yas sha hura ta gero,

    : Ya É—auko Garaya,

    : Yana ta ta kiÉ—i,

    : Barzan[6] barzan,

    : Barzan barzan,

    : Barzan zanzan,

    : Barzan zan,

    : Barzan bazan,

    : Barzam barzan,

    : Bazam barzam,

    : Barzan barzan,

    : Zarzan.

    : Bazam bazam,

    : Barzan barzan zarzan ,

    : Dodon gina gije kanun gayya.

    : Sodangi[7] É—an waÉ—an Tungat tunku,

     ‘Y/ Amshi: Geronka ya yi kyau,

    : Gwarzon Dango.

    : Bai tsaya gida ba,

    : Ya wa gona dirar kago,

    : Ya nome ta.

     

    Jagora: Kare mai kashe barewa,

    : Ko mai kashe É“auna,

    : Gami da gwanki,

    ‘Y/ Amshi: Wannan sunanshi,

    : Ya haye man su yanzu,

    : Bai tsaya gida ba,

    : Ya wa gona dirar kago,

    : Ya nome ta.

     

     Jagora: Mai garaya da yah hole,

    : Ya kama zahin mahalba,

    : Su dai sai taƙamab baƙin taggo[8],

    : Ga burtu kahe da kai,

    : Ga  Allad dawwama.

     

     Jagora: Sai dare Æ™anen Ba’u.

    ‘Y/ Amshi: Mijin Ba’u ne,

    : Mijin ƙwairon ganga.

    : Bai tsaya gida ba,

    : Ya wa gona dirar kago,

    : Ya nome ta.

     

      Jagora: Mai zwarin wuri magajin.

    ‘Y/ Amshi: Mamman,

    : Mai zwarin wuri maga..,

    : Jin ÆŠanhawwa.

    : Bai tsaya gida ba,

    : Ya wa gona dirar kago,

    : Ya nome ta.

     

      Jagora: A gaida Jibo,

    : Mai ruwan Gabas.

    ‘Y/ Amshi: Bardoki a gaida Jibo,

    : Mai ruwan Gabas,

    : Na gode ma.

    : Bai tsaya gida ba,

    : Ya wa gona dirar kago,

    : Ya nome ta.

     

      Jagora: Mai zwarin wuri magajin.

    ‘Y/ Amshi: Mamman mai zwarin wuri,

    : Magajin ÆŠanhawwa.



    [1]  ÆŠanbisa na É—akin/jinka.

    [2]  Maganganu maras makama.

    [3]  Kaza yake nufi da wannan Kalmar.

    [4]  Ina-nika-aza ga yaro wanda iyaye suke yi don nuna masa Æ™auna. Wato su riÆ™a yi masa duk abin da yake so.

    [5]  HaÉ—ama/son ya samu shi kaÉ—ai/handama da babakere.

    [6]  Wato yadda garayar take amo ne ya sifanta.

    [7]  Mai so da taimakon danginsa.

    [8]  Riga/Taguwa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.