Ticker

Jikan Barmo

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Jikan Barmo

 

G/Waƙa: Yaro Wanda As Shiryayye.

 

  Jagora: Aiki ya  hirgice ɗan Musa,

: Jikan Barmo maza manoma,

: Mai wa gona shigar gayya.

‘Y/Amshi  : Dan ka taso aikin ka noma,

: Aiki in ya buwaya sai su,

: Don ka taso aikin manoma,

: Aiki in ya buwaya sai shi.

 

  Jagora  : Aiki ba za ya ƙarewa ba,

: In ba dan soja anka kai rai ba,

: Yaƙi ba za ya ƙare wa ba,

: In ba ɗan soja anka kai rai ba.

  ‘Y/ Amshi  : Aiki ya  hirgice ɗan musa ,

: Jikan barmo maza manoma,

: Mai tsoron zuciyar uba,

: Sannan shi ba ya batu nai,

 

Jagora : In dai nauyin buhu guda,

: Ba ya kashe jaki da adda ƙarhi,

: Bayan dai nauyin buhu guda,

: Baya kashe jaki da adda ƙarhi,

: Yaro ne wanda as shiryayye,

: Gaba dai gaba dai ɗan Musa,

: Ga tsoron zuciyar uba,

: Sannan shi baya tsallake batu nai.

  ‘Y/ Amshi  : Aiki ya  hirgice ɗan Musa,

: Yaro ba dai yakai garai ba,

: Ko ya anka shinhiɗa mai,

: Kai yaro ba zai kai ga rai ba,

: Ko ya anka shinhiɗa mai,

: Musa in ya kama noma,

: Kafin ya cimma ka,

: Ni ya zata taki sanin dawowa tai da sahe,

: Ya take sawun kura,

: In an kai bayan mangariba,

: Ita kura ta take sani nai,

: Aiki ya  hirgice Ɗan Musa,

: Jikan Barmo maza manoma,

: Mai ma gona shurin gaba,

: Yaro ne wanda ar shiryayye,

 

Jagora : Tsoho ya bar biɗar budurwa,

: In ba dogon kwaɗai garai ba,

: Tsoho yabar biɗar budurwa,

: In ba dogon kwaɗai garai ba,

: Tsoho yabar biɗar budurwa,

: Ko in ya biɗe[1] ta hira,

: In har taso ta tsugunna shi,

: Da ta zo sai ta durƙusa mai,

: Ta ce mai yaushe kaz zo.

‘Y/ Amshi : Aiki ya  hirgice ɗan Musa,

: Jikan Barmo maza manoma,

: Mai ma gona shuwen gaba,

: Yaro ne wanda as shiryayye.

 

 Jagora: Ya ce aiko su aka yi,

: Sai ya ce ba aiko shi aka yi ba,

: Ya ce aiko shi aka yi,

: Sai ya ce ba aiko shi aka yi ba,

: Ya ce mai ɗan karen taɓaɓɓe[2],

: Ya ce mata yar karan taɓaɓɓe,

: Ki bamu kuɗin da munka bayar,

: In ba kuɗin ubanki ne ba.

 ‘Y/ Amshi: Aiki ya  hirgice ɗan Musa,

: Jikan Barmo maza manoma,

: Mai ma gona shigar gayya,

: Yaro ne wanda as shiryayye.

 

  Jagora  : Yaro ne wanda ar shiryayye,

: Gaba dai gaba dai gaba ɗan Musa,

: Ga tsoron zuciyar uba.



[1]  Neman hira

[2]  Mahaukaci/ mai wata taɓuwa.

Post a Comment

0 Comments