Ticker

6/recent/ticker-posts

Jikan Dodo Dan Gwamma

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Jikan Dodo Ɗan Gwamma

 

 G/Waƙa: Ɗan Sarki,

: A gode maka,

: Jikan Dodo,

: Ɗan Gwamna.

 

 Jagora: Sai dai a yi maganin yunwa,

: Dawon jiya ya ƙi yami[1],

  ‘Y/ Amshi: In ba nono banga afki ba,

: Ɗan Sarki,

: A gode maka,

: Jikan Dodo,

: Ɗan Gwamna.

 

 Jagora: Ya tahi daji,

:Ba ya dawowa,

: Kullun,

: Daga duƙe sai duƙe.

  ‘Y/ Amshi: Ɗan Sarki,

: A gode maka,

: Jikan Dodo,

: Ɗan Gwamna.

 Jagora: Ya tahi daji,

: Ba ya dawowa,

: Kullu,

: Daga duƙe sai duƙe.

  ‘Y/ Amshi: Gyado mai ƙoƙarin gabce,

: Mijin ɗiya,

: Jikan nomau,

: Ɗanɗa Ango,

: Karsanin Ali,

: Gungaman Iro,

: Ɗan Jatau ,

: Ɗan Sarki,

: A gode maka,

: Jikan Dodo,

: Ɗan Gwamna.

 

 Jagora: Haba kanda[2] ku tambayo doki,

: Garba ya  ba ni daidai ne,

: Waƙatai sai daniz zaɓa.

 ‘Y/ Amshi: Ya saurara da kunnenai,

: Ya san ba sukana[3] ta ba,

: Ya san ba wagara[4] ce ba,

: Ɗan Sarki,

: A gode maka,

: Jikan Dodo,

: Ɗan Gwamna.

 

 Jagora: Sai na biɗi doki mai geza,

: Sai ka yi danda ko hurde,

: Dokin faifai[5] doki ne.

‘Y/ Amshi: Amman bai gadi sirdi ba,

 

Jagora: Doki ɗauke ga jikka,

 ‘Y/ Amshi: Jikka sai dai ka ɗauka,

: Ba ya ɗaukak ka,

: Dokin faifai,

: Ba ya ɗauka ba,

: Ko akuya tai girma,

: Dokin hwaihwai,

: Baya rama ta.

: Ɗan Sarki,

: A gode maka,

: Jikan Dodo,

: Ɗan Gwamna.

 

Jagora: Shanshambu[6]

: Da Ƙirya,

‘Y/Amshi : Da Suwaga,

: Sun yi jeri,

: Sun bi hanya,

: Ban ga shawa ba,

 

Jagogra: Tulaƙi da bukaɗa da buƙe[7].

: Ko guda,

‘Y/Amshi: Ba zani ɗauka ba,

: Ɗan Sarki,

: A gode maka,

: Jikan Dodo,

: Ɗan Gwamna.

  Jagora: Mai tcintuwak kuɗɗin Ƙwairo,

: Na gane,

: Sai yay yi tuma,

  ‘Y/Amshi: Sai mu sake dubara,

: Mai soshiya da susu[8],

: Ya ishe bizi,

: Bai yi susa ba,

: In ka so shi ka sosa,

: Kahin wuya nasonku ya ƙaru,

: Sannan in anshi sisina,

: In kau ba ka bai wa,

: To yi jawabi,

: In ji hujjak ka.

: Ɗan Sarki,

: A gode maka,

: Jikan Dodo,

: Ɗan Gwamna.x2



[1]  Tsami.

[2]  Kafin.

[3]  Magana wadda ba da gaske ba, wato marar muhimmanci.

[4]  Yawon banza/wahalar banza.

[5]  Sallamar da ake yi wa makaɗi ta kuɗi, a da can ga faifai akan azo kuɗin a kawo ma makaɗin don kowa ya gani. Kodayake ba dokin aka baiwa makaɗi ba, ta yiwu kuɗin da aka ba shi suna iya sayen doki ko ma su wu wuce na sayen dokin. Sai makaɗan su ce ka bas u doki amma na faifai, (hwaihwai inji Sakkwatawa).

[6]  Mutum mara jiki/ ramamme.

[7]  Sunaye nr mawaƙin ya zana na wani mutum mai ƙiba wanda bai san ciwon kansa ba/sauna/wawa.

[8]  Soson wanka.

Post a Comment

0 Comments