Ticker

Ka Rike Kalme Ka Yi Gona

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Ka Riƙe Kalme Ka Yi Gona

  G/Waƙa: To ka riƙe kalme ka yi gona,

: Yaƙi rashin aiki bari wargi[1].

 

  Jagora: To ka riƙe kalme ka yi gona,

: Ka yaƙi rashin aiki mu ji daɗi.

. ‘Y/ Amshi: To ka riƙe kalme ka yi gona,

: Yaƙi rashin aiki bari wargi.

 

 Jagora: Najeriya ƙasarmu ta gado,x2

: Mu gukiyammu da rai mun bat a,

 ‘Y/ Amshi: Do haka sai kowa ya yi himma,

: Mu yaƙI rashin ɗa’a mu ji daɗi.

: To ka riƙe kalme ka yi gona,

: Yaƙi rashin aiki bari wargi.

 

 Jagora: Najeriya ƙasarmu ta gado,

: Mu dukiyammu da rai mun ba ta,

 ‘Y/ Amshi: Do haka sai kowa ya yi himma,

: Mu yaƙi rashin ɗa’a mu ji daɗi.

: To ka riƙe kalme ka yi gona,

: Yaƙi rashin aiki bari wargi.

 

  Jagora: Ko hassada zunɗe ko ƙeta.

 ‘Y/ Amshi: Wannan ba tarbiyya ta ba.

; Ka ji rashin ɗa’ag gat a banza.

 

  Jagora: Ko hassada zunɗe ko ƙeta.

 ‘Y/ Amshi: Wannan ba tarbiyya ta ba.

; Ka ji rashin ɗa’ak ka ta hwarko.

: To ka riƙe kalme ka yi gona,

: Yaƙi rashin aiki bari wargi.

 

  Jagora: Do na jiya a wajen malammai,

: Na ƙara ji a wajen manyanmu,

: Buyadin illa biyadin Musa,

: Bin na gaba shi ne bin Allah,

 ‘Y/ Amshi: Mu bi sarkinmu da malammanmu,

: Yadda ƙasan nan za ta yi daidai.

: To ka riƙe kalme ka yi gona,

: Yaƙi rashin aiki bari wargi.

 

 Jagora: ‘Yan hwasa ƙwabri da wasu ɓarayi,

; Ga wani horo wanda na yo maku

: Kowas san Allah ke baiwa,

: Kuma yas san Allah ke karɓa.

 ‘Y/ Amshi: Ka san wannan ba ya da wani jahilci.

: In dai ba niyyar rikici ba,

: To ka riƙe kalme ka yi gona,

: Yaƙi rashin aiki bari wargi.

 

  Jagora: ‘Yan hwasa ƙwabri da wasu ɓarayi,

; Ga wani horo wanda na yo maku

: Kowas san Allah ke baiwa,

: Kuma yas san Allah ke karɓa.

 ‘Y/ Amshi: Ka san wannan ba ya da wani jahilci.

: In dai ba niyyar rikici ba,

: To ka riƙe kalme ka yi gona,

: Yaƙi rashin aiki bari wargi.

 

 Jagora: Ina shugaban ƙasa ko Gwamna?

: Waɗanda suke zamani yanzu,

: Ku ɗauki halin Sa Amadu Bello,

: Zamanin da yana yin mulki,

: Hangi gusun kadiba Arewa.

  ‘Y/ Amshi: Eburbody yaɗ ɗauke mu,

: Bai yi ƙabilanci ga ƙasa ba.

: To ka riƙe kalme ka yi gona,

: Yaƙi rashin aiki bari wargi.

 

  Jagora: Ku kuma mat azan maku horo,,

: Ku kuma mat azan jishe ku,

: Yawon banza ko sakarci,

: Shi ma Wannan bay a da kyawo,

: Don Allah kowace ta yi aure,

 ‘Y/ Amshi: Mu kama yaƙi da rashin ɗa’a,

: Musa ba ɓacin ku ya yo ba.

: To ka riƙe kalme ka yi gona,

: Yaƙi rashin aiki bari wargi.

 

 Jagora: Ku kuma matazan maku horo,,

: Ku kuma matazan jishe ku,

: Yawon banza ko sakarci,

: Shi ma Wannan bay a da kyawo,

: Don Allah kowace ta yi aure,

 ‘Y/ Amshi: Mu kama yaƙI da rashin ɗa’a,

: Musa ba ɓacin ku ya yo ba.

: To ka riƙe kalme ka yi gona,

: Yaƙi rashin aiki bari wargi.

 

  Jagora: Abin da ya ci mani tuwo a ƙwarya,

: Ka ga mutun na aikin Gammen,

: To amman kuma bai riƙa noma,,

 ‘Y/ Amshi: Ya yi rashin ɗa’a Ɗan’bau,

: Sannan bai kyauta ma ƙasa ba.

 

  Jagora: Ma’aikatan Gwamnati ga horo,

: In dai kun je aikin Gwammen,

: To ku riƙe shi amanr Allah.

 ‘Y/ Amshi: In ka ƙi yi ka cuci ƙasa.

: Ka cuci mutan ƙauye da na birni.

 

 Jagora: Ku kuma mat azan maku horo,,

: Ku kuma mat azan jishe ku,

: Yawon banza ko sakarci,

: Shi ma Wannan bay a da kyawo,

: Don Allah kowace ta yi aure,

 ‘Y/ Amshi: Mu kama yaƙI da rashin ɗa’a,

: Musa ba ɓacin ku ya yo ba.

: To ka riƙe kalme ka yi gona,

: Yaƙi rashin aiki bari wargi.



[1]  Rashin yin aikin gona shi ne wargi ga makaɗa alhaji Musa Ɗan Ba’u, wato mutum ya tsaya yana wasa da rayuwarsa.

Post a Comment

0 Comments