Kamancen Kashi Ko Gazawa

     Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Bara da wasu waÆ™oÆ™in bara a Æ™asar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    Kamancen Kashi Ko Gazawa

    Wannan ita ce kamantawa da mawaƙi kan yi amfani da ita a tsakanin wasu abubuwa biyu amma ya nuna ɗaya bai kai ga ɗayan ba ta fuskar kamar da yake son mai saurarensa ya ɗauka akwai ta tsakanin waɗanna abubuwa biyu. Ana amfani da kalmomi irin su bai kai, ko bai yi, ya kasa da sauran irin waɗannan. Misali:

    Ya Ilahil Arshi, ba ni,

    Hankali da yawan bayani,

    ‘Yan’uwa suka tambaye ni,

    Mui ma waƙar tamu sani,

    Gyara ba zai kamar kashi ba.

     (Aliyu Namangi: Imfiraji)

    A wannan waÆ™ar akwai kamancen kasawa a cikinta a É—ango na biyar, a inda aka kwatanta gyara da kuma kashi a sama, akwai kamantawa ta kashi a ciki – Gyara ba zai kamar kashi ba. Wannan na nufin gyara ya kasa don bai kai ga kashi ba wato wata waÆ™ar da mawaÆ™in zai yi a matsayin gyara ba za ta kai ga ta farko da ya riga ya yi ba, duba a layi na biyar a sama.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.