Kambamawa

     Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Bara da wasu waÆ™oÆ™in bara a Æ™asar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    Kambamawa

    Ita wannan wani lafazi ne ko furuci da mawaƙa kan yi wanda sai a ga abu ne mai wuya haka ta auku, sukan faɗi abin da ba zai yiwu ba, su nuna ya auku ko zai auku; ko kuma su ce in ma ya auku ba zai hana haddasa wani abu ba. Ɗangambo, (2007:43).

    Wato ke nan kambamawa shi ne faɗin aukuwar wani abu wanda hankali bai iya kamawa kuma a ce haƙiƙa ya auku. Mawaƙa na amfani da wannan salo domin nuna ƙololuwar wani abu da suke son nunawa. Misali:

     “Mara goma ta yaro ce,

     Ni saba’in nika canyewa,

    Ga sittin bisa leɓona,

    Ko ƙoshi ban fara ba.

     (Iya Siriri)

    A wannan waÆ™ar mabaracin yana son ya nuna shi ma’abucin cin abinci ne har yadda ba a zato. Domin tabbatar da haka sai ya É—an bayar da labari irin abin da yake iya canyewa. Mai bara na yin haka domin kada masu ba shi sadaka su yi ba shi abinci komai yawansa. Sai ya gaya masu ga abin da yake ci kuma duk da haka ba don ya ishe shi ba. Wannan ci da almajirin da ke rera wannan waÆ™a yake da’awar yana da shi kambamawa ce, cin nasa ko alama bai kai haka ba ko kusa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.