Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali Sububu. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Kammalawa
Komai ya yi farko zai yi ƙarshe in ban da ikon Allah, wannan aikin ya zo ƙarshensa a wannan lokaci, Allah ya ba da ikon ƙare aikin ne wanda a cikinsa ne aka binciki tarihi da waƙoƙin shahararren mawaƙin noman ne na wannan yanki na Yammacin Arew, wato
jihohin Sakkwato da Kabi da Zamfara wanda kowa ya sani da suna Amali Sububu. An dubi salsalar[1]
mawaƙin sannan aka dubi yadda ya fara
waƙoƙinsa da yadda suka bunƙasa a ƙasar Hausa bakiɗaya. An kuma yi tarken turakun
waƙoƙin Amali Sububu manya da ƙananansu. Bayan wannan an kawo waƙoƙin Amali Sububu waɗanda ya yi
wa manoma, da kuma waƙoƙinsa da ya yi wa waɗansu mutane waɗanda ba
manoma ba, ko kuma a ce waƙoƙinsa da ya yi don noma da waɗanda ya yi
ba don noma ba. An kuma bayar da wani ɗan taƙaitaccen bayani a kan mutanen da Amalin ya yi wa waƙar kafin a kawo kowace waƙar da ya yi
masu, don a gane su kurum, a kuma san inda suka fito. Da fatar wannan aikin ya
amfanar da jama’a musamman manazartan adabin Hausa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.