Kanoma

     Citation: Bungudu, H. U. (2023). ZaÉ“aÉ“É“un waÆ™oÆ™in mawaÆ™an baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bungudu
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Noma

    Kanoma

     

      G/WaÆ™a: Kanoma  ka fi Æ™arhin gida,

    : Abu mai turu.

     

      Jagora: Eh Æ™warai

      ‘Y/ Amshi: Kanoma  ka fi Æ™arhin gida,

    : Abu mai turu.

     

      Jagora: Kai na ji daÉ—i Æ™warai.

     ‘Y/ Amshi: Kanoma ka fi Æ™arhin gida,

    : Abu mai turu.

     

     Jagora: Mazaje ku kama noma x2.

     ‘Y/ Amshi: Kowa  yak ki noma,

    : Wuya na cim mai.

     Jagora: In taÆ™amak ka iko,

    : Kai ko doki dubu garai,

    : Ga bayi,

     ‘Y/ Amshi: Sai  an kai maka damu[1] ka sha.

     

     Jagora: In  taÆ™amak iko kai ko,

    : Doki dubu garai ga bayi.

     ‘Y/ Amshi: Sai  an kai maka damu ka sha,

     

     Jagora: In taÆ™amak ka ilmi ba’a,

    : Karatu a kammale baki dai.

    ‘Y/ Amshi: Sai an aje damman gero nai.

     

    Jagora: Kowa ya aje gero ya,

    : Aje dawa ya aje damman,

    : Maiwa’ ita!

    ‘Y/ Amshi: Wannan ya wuce renin kowa .

     

    Jagora: Shi wanda baya da gero,

    : Baya da kuÉ—É—in sayen,

    : Abinci ko É—ai.

    ‘Y/ Amshi: Sai dai ya karkace baki É—ai.

     

    Jagora: Kara Bala da sauƙi.

    ‘Y/ Amshi: Ashe bana ya ji wuya,

    : Ba daÉ—i.

     

    Jagora: Wane tsiya ta sa mashi taggo[2].

    ‘Y/ Amshi: Ta yi baki Ḱirin kama da koren kaiwa.

     

    Jagora: Ka bari sai da dagumi yaka Ḱarya,

    : Karya .

    ‘Y/ Amshi: Sai  babu na dagumi ya ba  karya.

     

     Jagora: In kash shigo ga birni ka ishe kowa,

    : Da na shi bindi x2.

     ‘Y/ Amshi: Samu ko zan gar niya,

    : Ka so ka baya kaima ,

    : Ka zama dud da sauran,

    : Ka ji wuyar maza da aikon gona x2.

     

    Jagora: Ko ban san ka,

    : Ko da na goye ba bai x2.

    ‘Y/ Amshi: Kazo sarki ga katon banza x2.

     

    Jagora: Allah shi waddan duhun Ḱyara.

    ‘Y/ Amshi: Sannun da aiki da yai ko bai zoba,

    : Ka ji wuyar maza ka yi aikin gona ,

     

    Jagora: Tashin tsiya  ba ni labarin,

    : Ta ce da kasa da geme.

    ‘Y/ Amshi: Duka da Ḱyar sun ka,

    : Banbanta mai,

    : Kai maza sun ka,

    : Maimaita ma x2.

     

     Jagora: Yau dai ga Aliyu ya  ba ni doki.

    ‘Y/ Amshi: Yanzu noma yaka kari,

    : Dai dai.

     

    Jagora: Kai na gaban  su da  duki,

    : Sannu da aiki.

    ‘Y/ Amshi: Yan zu noma ya kari ko,

    : Dai .

     

     Jagora: Duk kai duro kay yi mata. 

    ‘Y/ Amshi: Ya  barman abu da Æ™waryar nono.

     Jagora: Ga ta da raina wata mata.

    ‘Y/ Amshi: Ya  barman abu da Æ™waryar nono.



    [1] Fura musamman furar gero.

    [2]  Tufafi tagguwa kamar yadda Sakkwatawa suke cewa, ma’ana riga.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.