Kari

     Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Bara da wasu waÆ™oÆ™in bara a Æ™asar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    Kari

    Kari shi ne awon da mawaÆ™i ya É—ora waÆ™arsa a kai. Akwai hanyoyi biyu da masu nazarin waÆ™a suka bayar da ake iya auna karin waÆ™ar baka da su. Hanya ta farko ita ce ra’in Gusau (2003) wadda ya kira ta gidan dara. Hanya ta biyu ita ce ra’in Dunfawa (2003) wadda ya kira Bahaushen Kari.

    A hanya ta farko ana ƙirga yawan gaɓoɓin kowane layi ne gwargwadon yawansu, sai a iya cewa tana kan gajeren kari ko dogo ko kuma matsakaici. Misali:

     Jagora: Kai É—an na burge – burge,

     Amshi: Burge.

    Jagora: ÆŠan na burge – burge,

    Amshi: Burge.

    Jagora: Ga Inna ta yi baƙi,

    Amshi: Burge.

    Jagora: Baƙin da ba su ƙoshi,

    Jagora: Baƙin da ba su ƙoshi.

     (ÆŠan Naburgi)

     

    Kai/É—an/na/bur/gi/bur/gi

    g / g / g / g / g/ g/ g

     

    Ga/in/na/ta/yi/ba/ ƙi

     g/ g/ g/ g/ g/ g/ g

     

     Ba/Æ™in/da/ba/su/Æ™o/shi

     g/ g/ g/ g/ g/ g/ g

     

    Idan aka lura za a ga kowane layi na ɗan waƙar da ta gabata yana da gurbi kari (gaɓa) bakwai (7), wanda ya nuna karin waƙar matsakaice ne.Gusau (2003:53)

     

    Hanya ta biyu kuwa Dunfawa (2003), an nuna ana samun kari ne daga sautin kiÉ—an da ke tafiya tare da waÆ™ar abin da ya kira ’Æ™ira’. Daga gaÉ“oÉ“in sauti huÉ—u na Æ™arshe da layukan waÆ™a ke Æ™arewa tare da sautin kiÉ—a ake samun karin waÆ™ar. Ta wannan hanya ya ce ake samun karuruwa bakwai. Misali:

    Jagora: Maula ta Sidi maula ta Balarabe.

    Amshi: Maula.

    Ja gora: Babban gida da daÉ—in bara yake.

    Amshi: Maula.

    Jagora: Waccan ta ba ka waccan ta hana maka.

    Amshi: Maula.

    Ja gora: Waccan ta É—auki kulki ta aza maka.

     Amshi: Maula.

     (Maula ta sidi)

    Idan aka lura sai a ga gaɓoɓi huɗu na layin farko su ne Balarabe, na layi na biyu su ne bara yake, na layi na uku hana maka, na layi na huɗu su ne aza maka. Wato haka abin yake:

     Balaarabee = v-v-

     Baraa yakee = v-v-

     Hanna maka = v-v-

     Azaa makaa = v-v-

    A bisa wannan awo an sami karin da ya kira mai ‘cassawa’, wanda gajerar gaÉ“a da doguwa ke karÉ“a-karÉ“a, Dunfawa (2003:29). A bisa ra’i na biyu sai mu ce wannan waÆ™a tana bisa kari mai cassawai.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.