Kinaya/Siffantawa

     Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Bara da wasu waÆ™oÆ™in bara a Æ™asar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    Kinaya/Siffantawa

    Salon kinaya shi ne salon da Ɗangambo ya kira siffantawa, wato salon da ake amfani da shi a kira wani da sunan wani da ba shi ba da nufi mai saurare ko karatu ya dubi wannan abin da kwarjini ko saɓanin haka na wancan abin da aka kira shi da sunansa, Yahya (1997). Kinaya kwatance ne na kaitsaye ta hanyar cire kalmomin kwatance da akan shigar tsakanin abin da aka kwatanta da wanda aka kwatanta shi da shi, irin su kamar, sai ka ce, ya fi, da sauransu. Akwai iri wannan salo a cikin waƙoƙin bara. Misali:

     Da bara da bara dan malam,

     Almajiri tsuntsu ne,

     Da ya ji motsin tsaba,

     Sai ya yi hiringi da kunne,

     (Da bara da bara ÆŠan Malam)

    A cikin wannan layi na biyu an siffanta almajiri da tsuntsu ta wajen son tsaba. Wato yadda tsuntsu ke son tsaba yake mayar da hankalinsa wajen da ya ji take, haka nan almajiri yake ba su da bambanci ko kaɗan. A haka wannan ɗa na waƙa yake son a dubi almajiri, mutum mai son ƙoto koyaushe daidai da yadda tsuntsu ke da bukata da shi koyaushe. Almajirai suna faɗin haka domin masu sauraren waƙarsu (waɗanda ake yi wa bara) su san irin tsananin bukatar abinci da masu baran suke da ita. Ƙila haka ya sa a tausaya a ba su sadaka. A wani misalin kuma cewa ake yi:

    Ina masoyan Muhammadu,

    In na ci na sha Muhammadu,

    Ina kirarin Muhammadu,

    Madara da zuma Muhammadu,

     (Madara da zuma Muhammadu)

    A wannan waƙar ma layi na ƙarshe salon kinaya ne, inda aka kira Annabi Muhammadu da madara da zuma. A nan mai waƙar na son mai saurarensa ya riya a ransa yadda madara take da daɗi idan aka saka zuma a cikinta. To irin daɗin wannan daɗin haɗin da ya sani haka Annabi yake da daɗi ga Musulmi. Duk da yake daɗin Annabi ya fi ƙarfin haka, ya kawo wannan ne a matsayin abin shan da yake gani ya fi soyuwa ga mutum.

    Haka a wannan ɗan waƙa mai zuwa shi ma akwai kinaya a cikinsa. Ga abin da ake cewa:

    Jirgi Ɗan Amina alƙawalin duniya,

    Allah ya yi duniya ya yo lahira,

    Ita waccan ta lahira can muka dogara.

    (Jirgi ÆŠan Amina)

    A farkon É—an wannan waÆ™a ne salon kinaya ya fito, wato wajen da aka kira Annabi da sunan jirgi. Abin nufi a nan shi ne, yadda jirgi ke kwasar ayarin jama’a ya tsallakar da su daga haÉ—arin ruwan kogi, haka Annabi ke kuÉ“utar da al’umma daga É“ata da haÉ—arin shiga wuta. MawaÆ™in na son mai saurarensa ya dubi Annabi irin dubin jirgin da ya loda al’umma ya ratsa kogi da su ya kai su ganga lami lafiya ba tare da samun wani haÉ—ari ba. Idan aka lura da dukan misalan da suka gabata, za a ga kwatanta Annabi ne ake da waÉ—annan abubuwa, amma saboda tsananta kwatancen sai aka share kalmomin kwatancen aka yi kinayarsu.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.