Kishi da Illolinsa a Mahangar Tatsunniyoyin Hausawa Jiya da Yau

    Published in Federal University Dutsin-ma Journal of Hausa Studies, (FUDJOHAS) a Journal of Hausa Studies, Department of Hausa, Federal University Dutsin-ma, Katsina State Vol. 1. No. 1. Maiden Edition, September, 2021, page 231-242

    www.writersdepository.com

    Kishi da Illolinsa a Mahangar Tatsunniyoyin Hausawa Jiya da Yau
    English Rendition as, Jealousy among Co-Wives and its Implications as Viewed by Hausa Oral Tales

     Bashir Aliyu Sallau
    Sashen Harsunan Nijeriya
    Jami’ar Umaru Musa Yar’adua Katsina

     Da

    Salima Suleman Isa
    Sashen Harsunan Nijeriya
    Jami’ar Umaru Musa Yar’adua Katsina

     

    Abstract

    Rivalry and jealousy which in some cases lead to misunderstanding and resulted in conflicts are inherent among various communities the world over. This usually happens in situations where there is the need to dominate or have total control over something. From time immemorial before the coming of Islam into Hausa land, a Hausa man can marry as many wives as he so wish. This is because possession of so many wives among the Hausa men was and is still a sign of wealth, prosperity as well as dignity. With the coming of Islamic religion into Hausa land and its acceptance by the majority of the Hausa people, it made them to limit the number of their wives to four as stipulated in the teachings of the new religion. In an attempt to have control over their husband, each of the wives will do everything possible to win his heart so that he will make her to be his Mowa ‘the favourite’ and others to be Bora ‘not favourite’. The Mowa and her children are always given special consideration, while the Bora and her children are not given proper care. It is the intention of this paper to look into the issue of jealousy and rivalry among Hausa co-wives as portrayed in Hausa folktales and examine the consequences of such rivalry and the lessons to drive therein for the benefit of our present day society.

    1. 0 Gabatarwa

    Kowace al’umma tana da ire-iren hanyoyin da take bi domin adana tarihinta, al’adunta, muradunta da manufofinta. Haka kuma, kowace al’umma tana da ire-iren hanyoyin da take bayyana abubuwan jin daÉ—inta da ma waÉ—anda ba ta jin daÉ—in su. Wasu al’ummomin wata alama suke zanawa don adana tarihinsu da al’adunsu, wasu kuma rubutawa suke yi, wasu kuma ta hanyar labaran wane ya ji ga wane ne, wasu kuma ta hanyar tatsunniya suke adana muhimman al’amuran da suka shafe su. Ta wannan fuska al’ummar Hausawa ma ba a bar su a baya ba, don kuwa tun kafin zuwan wannan zamani suna da ire-iren hanyoyin da suke adana tarihinsu da al’adunsu da ma dukkan abubuwan da suka shafi rayuwarsu ta yau da kullum. Daga cikin ire-iren waÉ—annan hanyoyi akwai karin magana da kacici-kacici da salon magana da baÆ™ar magana da Æ™arangiya da tatsunniyoyi da sauransu. WaÉ—annan jiga-jigan adabin baka na Hausawa musamman tatsunniyoyi sun fito da cikkakiyar rayuwar Hausawa tun lokaci mai tsawo da ya gabata har zuwa wannan zamani da Bahaushe ya sami hanyoyin rubutu da karatu don adana tarihinsa da al’adunsa da dukkan abin da ya shafi rayuwarsa.

    Hausawa na cewa, “kowa ya yi na gari don kansa”, dalili kuwa shi ne, dukkan wanda ya aikata aikin alheri kome daÉ—ewa zai ga sakamako mai kyau. Haka kuma, idan mutum ya aikata mummunan aiki shi ma, zai ga irin nasa sakamakon daidai da irin yadda ya aikata wannan aiki. Tun lokaci mai tsawo da ya gabata Hausawa suna koya wa ‘ya’yansu tarbiyya mai kyau don su sami sakamako mai kyau a gaba, sannan kuma suna nuna musu irin sakamakon da ake samu idan aka aikata mummunan aiki. Kafin zuwan wannan zamani tatsunniya na daga cikin ire-iren hanyoyin da al’ummar Hausawa suke bi domin koya wa ‘ya’yansu tarbiyya mai kyau da kuma kauce wa mummunar tarbiyya. Ta hanyar tatsunniya ce ake bayyana ire-iren ayyukan da wani ya yi waÉ—anda suka kai shi ga samun nasara a harkar rayuwarsa, sannan kuma ta wannan hanya ce ake nuna wa yara irin sakamakon da wanda ya aikata mummunan aiki ya samu a tasa rayuwar. Tun kafin zuwan wannan zamani abu ne sananne a wurin Hausa idan mutum ya Æ™ara mata, watau ya zama yana da mata É—aya ya Æ™ara suka zama biyu ko uku ko huÉ—u, zai iya fuskantar matsaloli iri daban-daban. Ko kuma ita amaryar da aka Æ™aro ta fuskanci matsala ko uwargida sakamakon kishi da aka iya nuna wa É—aya daga cikin matan. Irin wannan kishi yakan yi munin da zai kai ga matakin mai nuna kishin ta yi abin da zai kai ga cuta wa abokiyar zamanta, ko ‘ya’yanta, ko shi mijin da ya kawo su, da sauran munanan abubuwa waÉ—anda a wasu lokuta kan kai ga rasa rayuwar wani.

    Dangane da haka, wannan takarda za ta duba kishi a wajen Hausawa kamar yadda aka fito da hoton shi cikin tatsunniyoyin Hausawa da ire-iren illolin yin sa, domin koya wa ‘ya’ya tarbiyya mai kyau kuma ingantatta yadda idan suka girma suka yi aure su yi Æ™oÆ™arin kauce wa irin wannan mummunar É—abi’a. Kafin nan za a yi Æ™oÆ™arin bayyana abin da kalmar kishi take nufi da kuma abin da ita kanta tatsunniya take nufi a wajen Hausawa.

     

     

     

    1. 1 Kalmar Kishi a Wajen Hausawa

    Kamar yadda aka bayyana a cikin Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero, a shafi na 247, an dubi kalmar kishi da ma’anoni iri daban-daban kamar haka:

                               i.            Kalmar kishi na nufin rashin jituwa da nuna Æ™yashi irin wanda matan da suke auren mutum É—aya ke yi wa juna.

                            ii.             Tana kuma nufin nuna gaba ga wani a kan wata mace.

                          iii.            Haka kuma, wannan kalma tana nufin tsayawa da nuna Æ™wazo a kan wani ra’ayi ko sana’a d. s. Misali, kishin Æ™asa, kishin zuci, kishin sana’a da sauransu.

    Ita kuma Ingawa (1994: iii) ta bayyana cewa, “kishi na nufin halaya ta sosuwar zuciya da nufin yin magana ko tsokana tsakanin mutane biyu ko fi da suke tarayyar son wani”.

     Bisa la’akari da waÉ—annan manazarta suka ba kalmar kishi, a iya cewa shi dai kishi wani al’amari ne da shafi rayuwar al’umma wanda a wasu lokuta ana yin shi domin samun ci gaba, amma a wasu lokutan kuma ana yin shi don cuta wa wani.

    Kamar yadda aka yi bayani a bayanan da suka gabata, wannan takarda za ta duba fannin kishi ne wanda matan Hausawa suke yi a tsakaninsu wanda a wasu lokuta yakan haifar da illoli ga waÉ—anda suke yin kishi, ko ga ‘ya’yansu ko danginsu ko kuma ga mazan da suke aure. Za a yi haka ne, ta hanyar kawo tatsunniyoyi da yadda aka riÆ™a gudanar da kishi musamman daga cikin waÉ—annan tatsunniyoyi na Hausawa.

     

    1. 2 Tatsuniya

    Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero (2006:433), an bayyana tatsunniya ko gatanan a matsayin labari da ake ba wa yara na hikima don hira.

    A mafi yawancin lokuta ana gabatar da tatsuniya da dare. Idan lokacin rani ne, ana yin tatsuniya a farfajiyar gida, lokacin damina kuwa, na yin ta ne a cikin ɗaki. Wannan kuwa ya faru ne saboda a lokacin rani babu ruwan sama wanda zai jiƙa ƙasa kuma ba za a sami caɓi ba wanda zai hana a zauna ƙasa. Tsofaffi musamman mata ne suke tattara yara maza da mata suna yi musu tatsunniyoyi (Usman, 2009: iɗ).

    A tsarin tatsunniyoyin Hausawa ana ba da labarin mutane, sannan kuma da dabbobi da tsuntsaye da Æ™wari waÉ—anda aka ba siffa irin ta mutane. Tatsunniya tana da matuÆ™ar amfani a wajen Hausawa a lokacin da ya gabata. Dalili kuwa shi ne, kafin zuwan Larabawa da Turawa waÉ—anda suka kawo hanyar rubutu da karatu Æ™asar Hausa, tatsunniyoyi da labarai su ne hanyoyin da ake koya wa yara tarbiyya da halayen na kirki, da hani kan miyagun halayen da kuma dabarun zaman duniya, musamman abubuwan da suka shafi kare kai, samun abinci da kuma ingantacciyar zamantakewar al’ummomi daban-daban (ÆŠangambo, 2008: 30).

    Bayan mutane, mafi shahara daga cikin waÉ—anda suke fitowa a tatsunniyoyin Hausawa sun haÉ—a da Gizo da ƘoÆ™i da Dodo da Dodanniya da Mayya. Haka kuma, a cikin dabbobi ana samun Zaki da Kura da Dila da Giwa da Biri da sauransu. Ana kuma kawo kayan abincin Hausawa da matsayinsu waÉ—anda suka haÉ—a da Shinkafa da Masara da Dawa da Gero da Burtuntuna da sauransu. Wajen aiwatar da tatsnniyoyin Hausawa, mutane kan fito da shigar zamantakewar Hausawa wadda ta shafi sarki da talakawa, attajiri da marasa shi, miji da mata, zaman kishiyoyi da sauran al’amuran rayuwar yau da kullum. Wajen aiwatar da tatsunniya ana fito da irin dangantakar da take tsakanin waÉ—annan rukunoni na al’ummar Hausawa dangane da yadda suke tafiyar da rayuwarsu. A mafi yawancin tatsunniyoyi ana fito da irin zamantakewar da take Tsakanin mata biyu ko fiye waÉ—anda suke auren namiji É—aya, wato zaman kishiyoyi. A irin wannan zaman ana bayyana halayen kowace daga cikin waÉ—annan mata da matsayinsu a wajen mijinsu. Wadda miji ya fi so, ana kiran ta Mowa, wadda kuma miji bai damu da ita sosai ba ana kiran ta Bora. Sakamakon irin wannan zama ne yake haifar da Æ™iyayya da gaba da neman magungunan da za a cuta wa abokin zama ko ‘ya’ya da sauran abubuwa. Ta la’akari da irin wannan zama ne al’ummar Hausawa suka riÆ™a kawo gyara ta hanyar tatsunniya yadda dukkan wanda ya yi abu na kirki zai ga sakamako mai kyau, wanda kuma ya yi mummunan aiki zai gamu da sakamako marar kyau ba da daÉ—ewa ba. Wannan hanya ta taimaka matuÆ™a gaya wajen kawo gyara dangane da yadda al’ummar Hausawa suke gudanar da rayuwarsu. Dalilin haka ne, ya sa Hausawa suke cewa ‘kowa ya gyara ya sani’.

    Yanzu za mu kawo wasu tatsunniyoyi don ganin yadda aka riƙa gwada kishi tsakanin kiyoshi da irin sakamakon da aka samu bayan an aikata abubuwan da ba su kamata a aikata ba.

     

    Tatsinniyar Bora da Mowa

    Gata nan gata nan ku!

    Ta zo mu ji ta!

    Wani mutum yana da mata guda biyu; Mowa da Bora. Kowace tana da É—iya mace, amma É—iyar Mowa ake so ba a son É—iyar Bora. Rannan ita É—iyar Bora sai uwarta ta mutu, sai aka bar ta zaune cikin gidansu babu mai taimaka mata. Da yara suka girma suka kai munzalin ‘yan mata, sai aka riÆ™a kiran É—iyar Bora zance ba a kiran É—iyar Mowa, saboda haka sai aka kama ta aka kulle a cikin É—aki wai don kada ta samu wanda zai aure ta.

                Kullum babansu yana tafiya kasuwa, duk lokacin da zai tafi sai kowa ya ba shi sabtun abin da yake so a sawo ma shi, amma ita É—iyar Bora ba a karÉ“ar sautunta. Rannan sai ta ce babansu idan ya je kasuwa ya sawo mata É—an Sarkin Agadas. To, ashe shi É—an sarkin Agadas ba sai da shi ake yi ba. Uban ya je kasuwa ya yi bincike bai samu É—an sarkin Agadas ba, sai aka ce ma shi, ya koma ya sheda mata baka son inda ake sayar da wannan abu ba. Ashe É—an Sarkin Agadas mutum ne É—an wani babban sarki. Ya koma gida ya sheda mata, ta ce, to, ba komi. Ana nan rannan sai wani mutum yana yawo tallar lalle yana cewa, a sai lalle, a sai lalle, sai ta ce mai lalle kawo. Sai ya ga ta miÆ™o ma shi kuÉ—i ta wata ‘yar Æ™ofa ta É—akin da aka rufe ta. Sai ya ce, ke kuwa mi ya sanya ki cikin wannan hali haka? Sai ta ce, ai ita É—iyar Bora ce, ba a son ta, ba a son ta samu miji ta yi aure, shi ya sa aka kulle ta a nan ciki. Sai mai lalle ya ce, ni kina sona? Sai ta ce, ina son ka. Sai ya ce, to ni kuwa zan aure ki ko a wane hali ne kike ciki zan aure ki. Sai ta ce to. Ashe wannan mai tallar lalle shi ne É—an Sarkin Agadas. Da ya ga inda take ya ba ta lalle, ya kama hanya ya tafi. Da dare ya yi, sai ta ga wani haske kamar na walÆ™iya ya keta rufin É—akin da take ciki ya diro. Suka yi sallama da wannan mutum suka gaggaisa, ya ce, to shi ne wanda ya zo tallar lalle. Shi ke nan sai ta ce, to shi ke nan, mene ne zai ba ta da zai tabbatar mata da cewa yana son ta. Sai ya ce zoben jikin shi, sai kuma ya cire ya ba ta. Daga nan sai ya yi tafiyarsa.

                Ashe a ranar da É—an sarkin nan ya zo kishiyar uwarta na kallon sa, sai ta je ta yo wani sihiri ta sawo tiyyoyinta na allurai ta tsittsira a haryar da yake bi, domin idan ya taka waÉ—annan allurai zai kamu da rashin lafiya har ya mutu. Da ya zo hira sai kuwa ya taka alluran nan, hirar da ba a yi ba ke nan, sai ya koma gida ya yi ta jinya, sai da ya É—auki tsawon lokaci bai dawo ba inda wannan yarinya take. A kwana a tashi, sai ta samu labarin ba shi da lafiya, sai ta shirya tafiya gano shi. Ta yi aski ta É—aura É—an buzunta tana riÆ™e da Æ™oÆ™onta, tana tafiya tana tambaya har ta kusa isa garin, sai ta ji ana cewa ‘duk wanda ke bin wannan hanya ya kula da kyau saboda akwai tsuntsayen da ke cin mutane, ba a bari a kai ga garin da É—an sarkin nan yake. Sai ta lallaÉ“a ta je ta kwanta cikin wannan dajin inda tsuntsayen nan masu cin mutane suke. Sai uban tsuntsayen nan ya ce yana jin Æ™amshin mutum, sai matarsa ta ce, wane mutum ne zai zo ya zauna nan inda muke har a ce ana ji Æ™amshinsa, don Allah ku kwanta kawai ba dai mutum ba ne.

                Can wajen asuba sai tsuntsaye suka tashi suka tafi kiwo da daddare da ma ta ji tsuntsayen na cewa, wannan É—an sarki da bai lafiya da za a samu kashinmu a jika masa da ya warke. Bayan duk sun tafi kiwo sai ta lallaÉ“a ta É—ebi kashinsu ta zuba a Æ™oÆ™onto, ta biyo hanya har garin da É—an sarki yake. Isar ta ke da wuya, sai aka ce, “kai É—an almajiri, ba ka san É—an sarki baya lafiya ba, ba a shiga ba a fita”. Sai ta ce, “aikuwa da za a bar wannan É—an almajiri da ya yi wa É—an sarki magani”. Sai suka ce haba! “Mu ma kammu mun yi mun kasa balle kai”. Sai ta ce,  “ku dai bar ni in shiga”. Sai aka ce, “to a Æ™yale shi mu gani”. Tana zuwa bakin Æ™ofar É—akin da É—an sarki yake, sai ta fara yin bara tana cewa:

                            ‘ÆŠan Sarki Agadas,

                            Jiya na je Magori,

                            Juma ta ce,

                            In gaishe ka. ’

    Sai É—an sarki ya ce:

                            ‘Yaushe ka ga Magori,

                            Juma ta ce,

                            Ka gaishe ni?’

    Sai Almajiri ya ce:

                            ‘Daren jiya na je Magori,

                            Juma ta ce in gaishe ka. ’

                Daga nan sai suka ga É—an sarki ya tashi ya buÉ—e ido, sai suka fara mamaki, sai suka ce, “almajiri ka Æ™ara matsawa kusa da shi mana”. Sai ta matsa, ta sake cewa:

                            ‘ÆŠan Sarkin Agadas,

                            Jiya na je Magori,

                            Juma ta ce,

                            In gaishe ka, ’

    Sai É—an Sarki ya ce:

                            ‘Da yaushe ka je Magori,

                            Juma ta ce ka gaishe ni|”?

    Sai almajiri ya ce:

                            “Daren jiya na je Magori,

                            Juma ta ce in gaishe ka. ”

    Sai É—an Sarki ya tashi zaune ya buÉ—e ido, sai almajiri ya jiÆ™a maganin nan da ke cikin Æ™oÆ™onsa (kashin tsuntsaye) ya ba shi ya sha, take sai É—an Sarki ya miÆ™e, ya samu lafiya aka yi ta mamaki. Da almajiri ya yi sati guda ya ce, zai tafi gida. Aka ce an ba shi rabin gari, ya ce ba ya so, aka ce, “to mi za a baka”? sai ya ce, “É—an Sarkin Agadas ya ba shi zobensa”. Za a rako shi, ya ce, “a’a, shi kaÉ—ai ya zo, shi kaÉ—ai zai koma, a garinsu ba a rakiya”. ÆŠan almajiri ya yi tafiyarsa gida.

    Bayan kwana biyu, sai É—an Sarki ya shirya tafiya zuwa wajen wannan yarinya (budurwarsa) a fusace zai je ya É—auke mata kai, saboda yana tunanin a sanadiyar ta ne ya kamu da cuta. Ya É—aga wata babarbarar takobi zai É—auke mata kai, sai ta ce. “Kash! Don É—an almajirin da ya yi maka magani ka yi haÆ™uri ka yi mani rayuwa”. Sai ya sauke hannunsa, sai ya sake É—aga hannunsa zai sare mata kai, ta sake cewa, “don É—an almajirin nan da ya yi maka magani ka yi mani rai”. Sai da aka yi haka sau uku, ga na ukun ne ya ce, wai a ina ta samu labarin É—an almajiri? Sai ta ce, ai ita ce É—an almajiri. Sai ya ce, a’a, bai yarda ba. Sai ta É—auko ma shi buzun da ta tafi da shi da Æ™oÆ™on da ta jiÆ™a masa magani ta ce, “kai a Æ™arshe ka ga zoben da ka ba ni. Na ji labari ne kawai na tafi daga nan domin in yi maka magani. Sai wannan É—an Sarki ya saurara wa wannan yarinya kuma daga Æ™arshe ya aure ta. Sarki kuwa ya haÉ—a masu komai da komai na zaman duniya suka zauna suka yi ta haihuwarsu da ‘ya’yansu. Ita kuma wadda ta yi asiri baÆ™in ciki ya kama ta har ya zama shi ne magamin mutuwarta.

                Ƙungurus kan kusu ba don Gizo ba da na yi Æ™arya.

     

    Darasin da aka Koya Daga Wannan Tatsunniya

    A wannan tatsunniya an fahimci baƙin kishi ya sa aka yi wa ɗan Sarkin Agadas sammun da ya kamu da ciwo saboda yana son ɗiyar Bora. Ita kuma ɗiyar Bora da ta sami labari, ta tafi garinsu ta ba shi magani ya sha ya warke ya zo garinsu har ya aure ta. Wadda ta yi sihiri kuma sakamakon baƙin ciki ta mutu.

     

    Tatsunniyar Mai Mata Biyu

    Gata nan gata nan ku!

    Ta zo mu ji ta!

    Wani mutum ne yana da mata biyu, kowace sai ta haifi É—a namiji, kuma su duka yaran sai Allah ya haÉ—a kansu suna son juna, amma ita É—ayar matar ba ta son É—an da ba nata ba. Wata rana sai ta sa wasu suka tafi da shi daji suka haÆ™a rami suka rufe shi da ransa, da gari ya waye sai É—anta ya tambaye ta baba ina Ille (ÆŠan’uwansa)? Sai ta ce, ita ma ba ta gan shi ba tun jiya, Æ™ila ma da ya je daji can ya mutu. Sai kuwa ya haÉ—a kayansa ya nufi daji yana waÆ™a yana cewa:

                            ‘’Ille Ille nawa,

                            Ille na Tatuba,

                            Ille sannu,

    Allah ka kai ni,

    Kushewar Ille,

    Amin’,

                Sai ya yi ta tafiya yana rera wannan waÆ™a. Can yana zuwa kusa da wani Æ™abari sai ya sake rera wannan waÆ™a yana cewa:

                            ‘Ille Ille nawa,

                            Ille na Tatuba,

                            Ille sannu,

                            Allah ya kai ni,

                            Kusheawar Ille,

                            Amin. ’

                Sai ya ji an amsa, sai ya tona ramin, sai ya ga É—an’uwansa jikinsa duk ya yi gashi liya-liya mai kyau, sai ya aske ma shi wannan gashin. Da mutane sun gan su sai su yi ta gudu. Da suka isa gida, sai uwarsa ta ce, kai da wa kuke tare ne ? Sai ya ce, ai É—an’uwana ne Ille na tafi na nemo shi. Nan take ta yanke ta faÉ—i ta some.

    Ƙungurus kan Kusu ba don Gizo ba da na yi ƙarya.

     

    Darasin da aka Koya Daga Wannan Tatsunniya

    Wannan tatsunniya kamar wadda ta gabace ta, an nuna baÆ™in kishi wanda ya yi dalilin da mai kishin ta binne É—an kishiyarta saboda ba ta son shi. Kasancewar É—an da ta haifa yana son É—an’uwansa ya shiga daji ya gano É—an’uwansa ya dawo da shi gida. Ganin haka, ya sa mahaifiyarsa ta faÉ—i ta mutu saboda baÆ™in kishi.

     

    Tatsunniyar Shinkafa da Dawa da Masara da Burtuntuna

    Gata nan gata nan ku!

    Ta zo mu ji ta!

    Da Shinkafa da Dawa da Masara suka yi kwalliya za su je wajen É—an sarki, sai Burtuntuna ta ce za ta bi su, sai suka ce ba su zuwa da ita Æ™azama ce. Suka shirya suka kama hanya, suna cikin tafiya sai suka ga wata tsohuwa tana wanka bakin hanya, sai ta ce wa Shinkafa yarinya zo ki cuÉ—a ni, sai ta ce, kam, in yo kwalliya zan je wajen É—an sarki, ki ce in cuÉ—a ki, lallai kin Æ™wala. Sai ta ce wa Masara, yarinya cuÉ—a ni, sai ta ce, ba wannan ya kawo ni ba. Sai ta ce wa Dawa, yarinya cuÉ—a ni, sai dawa ta ce, mi zai kai ni in taÉ“a bayan tsohuwa kamar ki, Allah ya kiyaye. Can bayan sun wuce, sai ga Burtuntuna, ta zo za ta wuce, sai tsohuwa ta ce, yarinya cuÉ—a ni, sai ta ce, to. Sai ta yi ta cuÉ—a ta, kafin ta gama, sai bayan tsohuwar nan ya É“urma, sai tsohuwar nan ta ce mata, mi kika gani, sai ta ce, Æ™wayaye guda biyu, babba da Æ™arami. Sai tsohuwar ta ce, É—auko Æ™aramin ki fasa, sai ta ce to. Ta fasa shi, sai ga zinari, azurfa, tufafi sabbi da kayan kwalliya iri-iri, ta ce ta É—auka ta sanya. Ta ce, to daga nan ina za ki? Sai ta ce, wajen wani É—an sarki. Sai ta ce, kin san sunan shi? Ta ce a ‘a, sai tsohuwar nan ta gaya mata sunan shi ‘ÆŠaskinÉ—ari’, ta ce, to shi ke nan na gode.

    Kafin Burtuntuna ta isa Shinkafa da Masara da Dawa sun daɗe da isa da suka isa Shinkafa ta fara ƙwanƙwasa ƙofa ɗan sarki ta ce:

                            ‘Assalam Salam

                            ÆŠan yaro,

                            Assalam Salam’

    Sai ya ce:                    ‘Wa ce ce ce,

                                        Take ma ni,

                                        Assalam Salam?’

    Sai ta ce:                     ‘Shinkafarka ce,

                                        ÆŠan Yaro,

                                        Mai dahuwa da É—aÉ—i. ’

    Sai ya ce:                    ‘To na ji naki suna yarinya,

                                        Ba ni nawa suna. ’

    Sai ta ce:                     ‘Ban sanka ba,

                                        ÆŠan Yaro,

                                        Ban sanka ba’

    Sai ya ce:                    ‘To ja da baya,

                                        Yarinya,

                                        To ja da baya,

                                        Ki sha kuka. ’

    Sai ta koma gefe guda ta yi ta rusa kuka,

    Sai Masara ita ma ta zo ta ƙwanƙwasa ƙofar ɗan sarki.

    Ta ce :                         ‘Assalam Salam

                                        ÆŠan Yaro,

                                        Assalam Salam. ’

    Sai ya ce :                   ‘Wa ce ce ce,

                                        Take ma ni,

                                        Assalam Salam ?’

    Sai ta ce :                    ‘Masararka ce,

                                        ÆŠan yaro,

                                        Mai tuwo da haske, ’

    Sai ya ce:                    ‘To na ji naki suna,

                                        Yarinya,

                                        Ba ni nawa suna,

    Sai ta ce:         ‘           Ban sanka,

                                        ÆŠan Yaro,

                                        Ban sanka ba. ’

    Sai ta ce:         ‘           To ja da baya

                                        Yarinya,

                                        To ja da baya,

                                        Ki sha kuka, ’

    Ita ma shi ke nan ta koma gefe guda ta yi ta rusa kuka.

    Daga nan sai Dawa ta shigo, ita ma ta ƙwanƙwasa ƙofar Ɗan sarki kamar haka:

    Ta ce:                          Assalam Salam,

                                        ÆŠan yaro,

    Assalam Salam,

    Sai ya ce:                    ‘Wace ce ce,

                                        Take ma ni,

                                        Assalam Salam, ’

    Sai ta ce :                    ‘Dawarka ce,

                                        ÆŠan yaro,

                                        Mai tuwo da garÉ—i, ’

    Sai ya ce:                    ‘To na ji naki suna,

                                        Yarinya,

                                        Ba ni nawa suna, ’

    Sai ta ce:                     ‘Ban sanka ba,

                                        ÆŠan yaro,

                                        Ban sanka ba, ’

    Sai ya ce:                    ‘To ja da baya,

                                        Yarinya,

                                        To ja da baya,

                                        Ki sha kuka, ’

    Sai ita ma ta ta koma gefe guda ta yi ta kuka tare da abokan tafiyarta Shinkafa da Masara.

    Ana nan, can sai suka hangi Burtuntuna ta taho, sai suka riÆ™a gulmar ta suna cewa, “waccan shegiyar ko wa ya ara mata kaya gulmamma, muma mun kasa balle ita Æ™azama”. Da ta iso ta gaishe su, amma ko kallon ta ba su yi ba balle su amsa mata, ta dai Æ™yale su ta isa wajen Æ™ofar É—an sarki ta Æ™wanÆ™wasa.

    Ta ce:                          ‘Assalam Salam,

                                        ÆŠan yaro,

                                        Assalam Salam, ’

    Sai ya ce:                    ‘Wa ce ce ce,

                                        Take ma ni,

                                        Assalam Salam, ’

    Sai ta ce:                     Burtuntunar ka ce,

                                        ÆŠan yaro,

                                        Mai tuwo da baÆ™i, ’

    Sai ya ce :                   ‘To na ji naki suna,

                                        Yarinya,

                                        Ba ni nawa suna, ’

    Sai ta ce:                     ‘ÆŠaskinÉ—ari,

                                        ÆŠan yaro,

                                        ÆŠaskinÉ—ari, ’

    Sai ya ce:                    ‘BuÉ—e ki shigo,

                                        Yarinya,

                                        BuÉ—e ki shigo, ’

    Sai ta buɗe ta shiga, aka ɗaura mata aure da ɗan sarki, sai Shinkafa ta ce, ni zan yi maki niƙa, Masara ta ce, ni zan riƙa yi maki wanki da wanke-wanke, Dawa ta ce ni zan riƙa yi maki shara da sauran aikace-aikace. Saboda haka, dukkansu sai suka kasance barori a wurin ta.

    Ƙungurus kan Kusu ba don Gizo ba da na yi ƙarya. Ko yanzu ma ita na giggirba maku.

     

    Darasin da aka Koya Daga Wannan Tatsunniya

    A wannan tatsunniya an kawo nau’o’in abincin Hausawa aka ba su siffa irin ta mutane yadda kowace ta bayyana irin kishin da take yi wa wadda ba su so wato Burtuntuna. Kasancewar Burtunuta tana da tarbiyya mai kyau ya sa ta sami nasara saÉ“anin danginta da suka nuna rashin tarbiyya wajen taimaka wa tsohuwa. Taimakon da yi wa wannan tsohuwa ya sa ta sami dukkan abubuwan da take bukata wanda ya kai ta ga auren DaskinÉ—ari. Wannan nasara da ta samu ya sa waÉ—anda ba su Æ™aunar ta suka aminci su yi mata barantaka.

                                                         

    Tatsunniyar ‘Yan Mata Uku

    Gata nan gata nan ku!

    Ta zo mu ji ta!

    WaÉ—ansu ‘yan mata da ma uwayensu su uku suka haife, da ka haife su uku sai guda ta ce, “ita dai ta yi alÆ™awarin cewa, idan suka girma ta isa misalin aikata abinci da kanta, to za a ba ta Æ™warar masara guda za tai abincin da wannan dukkan mutanen da ke cikin garinsu da Æ™auyen garinsu in aka ci abincin ba su Æ™oshi a yanka ta”. Kuma guda ta ce, ita kuma ta ce za a É—auko mata Æ™warar burji É—aya za ta yi daÉ“e da shi dukkan wanda ke garinsu da Æ™auyen garinsu idan suka zo bisa dawakinsu su take taÉ“en idan suka Æ™wantala shi Sarki ya yanka ta”. Ita kuma ta uku ta ce, “ita kuma in ta auri Sarkin garinsu, kuma za ta haifi ‘ya’ya biyu, kuma za su yi kama da Sarki, idan ba su kama da Sarkin nan ba, Sarki ya sa a yanka.

    Shi ke nan, Allah mai yau mai gobe, sai suka isa. Rannan ita guda aka ba ta masara ta je ta yi tuwo da ita duk aka ci tuwon nan har aka bar shi. Guda ta yi daÉ“enta duk dawakin garin da Æ™auyuka suka zo suka taka daÉ“en amma bai Æ™wantalu ba, sai aka zo ga wannan guda ta uku sai aka yi mata aure, kuma sai ta auri wannan Sarki na garinsu. Ana nan ana nan, sai ta sami ciki shi ke nan za ta haihu uwargidan nan ta zo ta kasa ta tsare wurin wannan mai haihuwa. Ta haifi ‘ya’yanta biyu duk maza, sai uwargida Sarki ta É—auki waÉ—annan ‘ya’ya ta je ta kai su ta É“oye, ta zubar da su, ta samo Jan kwatakwarai guda biyu sai ta kawo ta aje mata, sai ta tafi neman ungozama. To, haihuwar fari ba a magana don maijego tana gani da idonta abin da uwargida ta yi. Da ungozoma ta zo ta ce, “jama’a wannan abu ba mutane ba ne Æ™adangaru ne! Ke ma kin ga ni!. Ke ma kin gani! Ke ma kin gani! A kira wannan, a kira wannan, Ƙadangaru ne! Ke ma kin gani! Ungozoma ta tsantsame su aka je aka gaya wa Sarki an sami Æ™aruwa. Sarki ya taho yana kusuma ya samu ‘ya’ya guda biyu, yana zuwa sai ya sami waÉ—annan ‘ya’ya Æ™adangaru ne rangwaÉ—a-rangwaÉ—a. Sai ya ce, “kawai mi ake jira da ita, a je a yanka wannan mata”. Duk wanda ka kira sai ya ce bai zai iya yanka wannan mata ba. Sai aka sami wani dogari guda ya ce shi zai iya yanka ta. Da suka tafi wannan mata ya kai ta Æ™ungurmin daji ya ce, “bari in aje ki a nan, idan na aje ki zan riÆ™a kawo maki dussa da sabara ki riÆ™a ci, za ki iya zama?” Ta ce, “wanda za a raba da rayuwar shi in ya zauna nan, ai ba wani abu ba ne ba”. Ta zauna cikin wannan daji, shi kuma wannan dogari ya sami wannan Babarbarar Takobi wadda Sarki ya ba shi ya kaso tsutsaye da ita ya goge mata jini, sannan ya kawo wa Sarki suturar da ta fita da ita ya ce ma shi, “an kashe ta”. Shi ke nan Sarki ya ba shi rabin gari da ya ce ya kashe wannan mata.

    Ana nan ana nan, rannan sai wata tsohuwa ta je tana É—ibar tafasa sai ta ga wani abu yana motsi cikin ciyayi an lulluÉ“e shi, tana dubawa ta ga ‘ya’ya guda biyu jawur-jawur da su ga su kamar Larabawa. Tsohuwa ta É—auke su ta gyara tai ta tattalin waÉ—annan yara, suka girma suka zama mutane sai ta sai masu dawaki kuma tana yi masu É—unki iri É—aya. Shi ke nan rannan suka matsa za su ban ruwa tsohuwar nan ta ce, ba zan bar ku ku fita ba. Idan aka ganku ba za a bari ku riÆ™a dawowa inda nike ba, suka ce, ai babu mai iya raba mu da ke. Suka tafi rannan wannan ban ruwa, in suka gabato wurin ban ruwa sai su tsaya, domin jama’a dukkan waÉ—anda za su zo kallon su, su kuma suna waÆ™a suna cewa:

                   “Sunan mu “yan damariri,

                   Mu ‘yan masu gari,

    Mun diƙisa, mun diƙisa,

    Baƙin kishi ya sa aka jeho mu ta bayan katanga.

    To, shi ke nan sai su ba dawakinsu ruwa. Rannan da suka je ban ruwa sai aka je aka ce ma Sarki, ai an samu waÉ—ansu ‘ya’ya, sai Sarki ya zo da karin kan shi don ya ga waÉ—annan ‘ya’ya. Yana ganinsu sai ya hana waÉ—annan ‘ya’ya su koma gidan wannan tsohuwa, suka bijire suka ce ba za su bi wannan Sarki ba, suka koma gidan wannan tsohuwa da suka saba da ita. Ta ga yadda waÉ—annan yara suka dawo ba kamar yadda suka saba ba, sai ta ce, “wai mi ya faru”?” Suka ce, “an haÉ—o su ne da Sarki”. Ta ce, “ai ka gani daman abin da nike gaya maku ke nan, na ce ka da ku fita, kuka ce sai kun fita, to yanzu ga shi za a Æ™wace mani ku na kuma sami abina. Allah ne ya ba ni”.

    Shi ke nan waÉ—annan yara suna nan tare da tsohuwa sai Sarki ya sa aka tara mutane, ya sa aka aiwaka waÉ—annan yara ana so a ga wace ce ta haife su, wannan tsohuwa dai an san ba ta haihuwa, sai aka ce yanzu duk garin za a yi taro kowace ta yo abinci duk wadda waÉ—annan yara suka ci abincinta ita ce ta haife su, kuma kowace ta kawo takalminta tare da abincin. Rannan aka É—auki wannan taro aka cika gari da fadar Sarki, kowa ya kawo abinci da takalmi, wani nama, kowane da kalar abincin da zai kawo. Ai kuwa aka zo, waÉ—annan yara suka zo bisa dawakinsu duk abincin da suka É—aga sai dai su maida shi su rufe. Zuwa can sai ga wata mahaukaciya ta zo da tuwo na dussa miyar sabara da takalminta cirarre ta zo ta aje abinta. WaÉ—annan yara suna kawowa wurin tuwon wannan mahaukaciya sai suka buga wawa, É—aya ya sa takalmi guda ya yi ma shi daidai sai aka ce, to wannan mahaukaciyar ita ce ta haife su. To, ina ta samu waÉ—annan ‘ya’ya? Sai wannan dogari ya ce, matar da aka ba shi aka ce ya kashe, amma bai kashe ta ba, ita ta haifi waÉ—annan ‘ya’ya har suka kai haka. Aka ce, ai matar Sarki uwargida ita ta zubar da su, maijego na gani amma saboda haihuwar fari ba a magana shi ya sa ba ta gaya wa kowa ba. Da Sarki ya ji haka, sai ya ce, a je a fiddo wannan mata a yanka ta. Da aka É—auko uwargidan Sarki aka yanke, ita wannan aka je aka wanke aka gyara ta, ita ta zama matar Sarki.

     

    Darasin da aka Koya Daga Wannan Tatsunniya

    A wannan tatsunniya an fito da baÆ™in kishi wanda ya yi sanadiyyar É—auke ‘ya’yan amarya aka jefar da su, amma da yake suna da sauran kwana tsohuwa ta É—auke su ta rene su har suka girma gaskiya ta bayyana. Sakamakon mummunan aikin da uwargidan Sarki ta yi na nuna baÆ™in kishi Sarki ya sa aka yanka ta. Ita kuma amarya aka mayar da ita É—akinta ta zama uwargidan Sarki.

     

    Tatsunniyar Mairo

    Gata nan gata nan ku!

    Ta zo mu ji ta!

    Wata yarinya ce marainiya sunanta Mairo. Kishiyar uwarta ba ta kyautata mata, ko abinci za ta ba ta sai ta ba ta marar daÉ—i. Duk lokacin da ta ci abincin sai ta kama ciwon ciki. Rannan sai saurayinta ya ce mata, “wai mi ke sa ki ciwon ciki?” Sai ta ce, abincin da ake ba ta ne domin ita ba san shi take ba, babu yadda za ta yi ne, sai ya ce za ki iya barin cin abincin? Sai ta ce, a’a, idan ta bar cin abincin za ta tayar wa babanta hankali saboda haka za ta yi haÆ™uri ta ci gaba da cin abincin haka nan.

    Saurayin nan nata sai ya ba ta shawara cewa, idan ta baki abinci ki ci, kina ci sai ki yi mata mutuwar Æ™arya, ni kuma sai in zo inyi maki Æ™abari nan cikin gidan, za ta gane Æ™ila za ta riÆ™a sauÆ™aÆ™a maki ta daina baki wannan abincin marar daÉ—i, sai kuwa ta yarda. Rannan sai aka ba ta wannan abinci, sai kuwa ta ci, tana ci sai ta kama murÉ—e – murÉ—e, daga nan sai ta yi mutuwar Æ™arya. Shi ke nan sai wannan saurayin ya zo gidan nan yana cewa:

    Wayyo Mairo! wayyo Mairo!

    Sami Allah,

    Mairo ‘yar farar yarinya,

    Sami Allah,

    Ciwon cikin da kan jiƙe kanwa,

    Sami Allah,

    Mairo tafarnuwa aka ba ta,

    Sami Allah,

    Da ma ka gewaya ban É—aki,

    Sami Allah,

    In ka ga ‘yar Æ™asa Mairo ce,

    Sami Allah,

    Sai wannan saurayi ya fashe da kuka ya je yana tambayar wannan mata ina Mairo? Sai ya ce, shi kuwa ya ji Mairo na magana, sai ta ce, yo wanda ya mutu yana magana? Sai ya ce, “to da kin ce ba ki san inda take ba, sai ki zo ki fiddo ta, ai ke ce kika kashe ta”. Sai ta ce, “a’a, ciwon ciki ta yi ta rasu. Sai aka kama gardama, sai ya je ya tono Mairo ya fiddo ta, sai yake sheda wa babanta abin da ken. Daga nan sai uban Mairo ya ce, I, dama yasan wannan mata ba ta son Mairo, sai saurayin ya ce idan za a aura ma shi ita, zai riÆ™a ba ta abinci mai kyau ta daina cin abincin wannan mata tun da gaskiya kashe ta za ta yi, sai ya ce to shi ke nan. Uba ya aura wa wannan saurayi Mairo ya ci gaba da kawo mata abinci mai kyau, ashe ita wannan mata ba ta so, duk lokacin da saurayin nan ya kawo wa Mairo abinci, sai ta É—auke ta je ta sanya ma shi magani cikin abinci. Sai Allah Ya nuna wa wannan yarinya sai ta Æ™i cin shi. Wannan abu kuwa na É“ata wa uban Mairo rai. Rannan dai sai ya ce, za a kai wannan yarinya ta tare gidan mijinta tun da dai ba ki daina cutar da ita, baÆ™in ciki ya dame ta kamar ta kashe kanta.

    Rannan sai wannan mata ta je ta yi wa wannan saurayi asiri ta kashe shi, yarinyar nan kuwa ta yi kuka har ta gode Allah, ubanta ya riƙa lallashin ta yana cewa, ta yi haƙuri Allah zai ba ta wani. Ana nan rannan sai Allah ya kawo wani mai kuɗi ya zo ya ce yana son ta, gashi kuma shi shiryayye ne duk irin sihirin matar nan ba zai kama shi ba. Aka ɗaura masu aure ya ce, shi zai yi mata komai na kayan ɗaki ya ɗauke wa iyayenta komai da komai. Sai baƙin ciki ya kama wannan mata ta kamu da cuta, ga ɗiyarta babu wanda ya zo ya ce yana son ta. Takaicin duniya ya addabi matar nan ita kuwa Mairo ta auri mijinta suka yi ta zamansu na lumana da jin daɗi da kwanciyar hankali.

    Ƙungurus kan Kusu ba don Gizo ba da na yi ƙarya.

     

    Darasin da aka Koya Daga Wannan Tatsunniya

    Kamar sauran tatsunniyoyin da suka gabata, wannan tatsunniya ma ta bayyana sakamakon baƙin kishi. Daga gare za a amfani da cewa duk zakaran da Allah Ya nufa ya yi cara, sai ya yi ko da ana muzuru ana shaho. Hakan ya bayyana ne sakamakon dukkan sihirce-sihircen da wannan mata ta yi, sai da Mairo ta aure wanda za ya rufa mata asiri. Kasancewar haka ne, takaici da baƙin ciki suka kama wannan mata kuma suka yi dalilin mutuwarta.

     

    Kammalawa

    Halin zamantakewar kowace al’umma yana tafiya ne da É“arna da gyara. Wannan dalilin ne ya sa kowace al’umma take da hanyoyin da take bi don gyara É“arnar da take a cikin al’ummar. Al’ummar Hausawa duk da kasancewar kafin shigowar baÆ™i ba ta da hanyoyin rubutu da karatu waÉ—anda za ta yi amfani da su wajen koyar da tarbiyya da sauran abubuwan da suka shafi rayuwa, wannan bai sa sun zauna haka nan ba wata madogara. Tun lokaci mai tsawo da ya gabata Hausawa na amfani da tatsunniyoyi wajen koya wa ‘ya’yansu halayen na kirki da kuma hani ga aikata munanan ayyuka. Wannan hanya ta taimaka matuÆ™a gaya wajen rage aikata wasu munanan ayyuka musamman zama tsakanin kishiyoyi. Ta hanyar tatsunniyoyi al’ummar Hausawa sun bayyana wa al’umma ire-iren illolin da baÆ™in kishi yake haifarwa. Ta wannan fuska tatsunniyoyin Hausawa sun taimaka wajen bayyana illolin kishi da sakamakon da yake haifarwa. Sauraron waÉ—annan tatsunniyoyi sun taimaka sosai wajen watsar da baÆ™in kishi don gudun kar abin da ya faru ga wance ya faru gare ki.

    Manazarta

    ÆŠangambo, A. (1990) “Gadon FeÉ—e Adabin Hausa (Ba a Buga ba).

    ÆŠangambo, A. (2008) Rabe-Raben Adabin Hausa (Sabon Tsari) Amana Publishers Limited. Zaria: New Kano Road, Kaduna State.

    Gusau, S. M. (2008) Dabarun Nazarin Adabin Hausa, Kano: Benchmark Publishers Limited.

    Ingawa, Z. S. (1983) “Magungunan Hausa Don Mata: Nazari Kan Matan Hausawa da Ire-Iren Bukatunsu na Magunguna. Kundin Digiri Na ÆŠaya. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Ingawa, Z. S. (1994) “Kishi Kumallon Mata: Nazarin Sigoginsa a Rayuwar Hausawa. Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero (2006) Wallafar Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.

    Mukhtar, I. (2000) Jagoran Nazarin Ƙagaggun Labarai, Kano: Adamu Joji Publishers.

    Sallau, B. A. “Tatsunniyoyi da Aka Tattara a Ƙaramar Hukumar Mashi ta Jihar Katsina”, Hausa Folktales, Research Project 2A, sponsored by Dr. Bukar Usman Foundation Research in Folktales in Nigeria, under the able Chairmanship of Professor Abdu Yahya Bichi, submitted on 24th January, 2014.

    Skinner, N. (1980) AN Anthology of Hausa Literature in Translation.  Zaria: NNPC.

    Yahaya, I. Y. (1981) “Adabin Gargajiya a Makarantun Sakandare. Lacca da ya gabatar a Makarantar ‘Yammata ta Dala.

    Yahaya, I. Y. (2015) Labarun Gargajiya 1, Ibadan: University Press.

    Umar, M. B. (1984) Dangantakar Adabin Baka da Al’adun Gargajiya na Hausa. Kano: Triumph Publishing Company.

    Usman, B. (2009) Muguwar Kishiya (Da Wasu Labarai) Taskar Tatsunniyoyi Littafi na Goma Sha HuÉ—u. Kano: Gidan Dabino Publishers. 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.