La la la la Duniya

     Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Bara da wasu waÆ™oÆ™in bara a Æ™asar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    La la la la Duniya

     Jagora: La la la la Duniya

     Amshi: To

     Jagora: Inda masoyi ya mutu

     Amshi: To

     Jagora: In É—ebi ruwa ga buta

     Amshi: To

     Jagora: In bi rana in bi farin wata

     Amshi: To

     Jagora: Suna suna na sani

     Amshi: To

     Jagora: Wanda malam ya ce in faÉ—i

     Amshi: To

     Jagora: Ni kuma nicce ban faÉ—i

     Amshi: To

     Jagora: Amma yanzu faÉ—i nikai

     Amshi: To

     Jagora: Tun da ban iya kwana ban ci ba

     Amshi: To

     Jagora: Sunan dambu maÆ™ura

     Amshi: To

     Jagora: In babu ruwa É“anna yakai

     Amshi: To

     Jagora: Sunan kwaÉ—É—o MacciÉ—o

     Amshi: To

     Jagora: Su MacciÉ—o sai sanyin É—uwai

     Amshi: To

     Jagora: Sunan zaure Babuga

     Amshi: To

     Jagora: Sunan tantabara Kulu

     Amshi: To

     Jagora: Sunan hankaka Ige

     Amshi: To

     Jagora: Sunan hanya Lailatu

     Amshi: To

     Jagora: Sunan luddai Ummaru

     Amshi: To

     Jagora: Su Ummaru É—ebo tsaki akai

     Amshi: To

     Jagora: Sunan randa Maimuna

     Amshi: To

     Jagora: Su Maimuna sai Æ™aton ciki

     Amshi: To

     Jagora: Sunan mota GargaÉ—a

     Amshi: To

     Jagora: A gargaÉ—a kaya sai Kano

     Amshi: To

     Jagora: Sunan hanwawa Ige

     Amshi: To

     Jagora: Sunan maciji Awwalu

     Amshi: To

     Jagora: Su Awwalu ga kyau ga faÉ—a

     Amshi: To

     Jagora: Sunan jirgi SumbuÆ™a

     Amshi: To

     Jagora: Su sumbuÆ™a ga tashi sama

     Amshi: To

     Jagora: Tuwon masara Malam Hassan

     Amshi: To

     Jagora: A gama shi da sure Alhaji.

     Amshi: To


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.