Labbo Makigudu

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Labbo Maƙigudu

 

 G/ Waƙa: Ai mazan jiran damana koyaushe,

: Labbo riƙa kwarai Labbo noma sabo.

 

  Jagora : Ai Kambazam magiro,

: Labbo maƙigudu Labbo na gode,

: Ai Allah yana taimakon bawanai,

: Labaran noma yana taimakon mai yi nai,

: Labbo riƙa ƙwarai ai Labbo

: Garka kashe mai,

: Na gode Mamman,

: Na gode Mamman,

: Mamman ɗan Aya,

: Ka ga ban rena mai,

: Ai aiki ai sa ka tsare na.

 

Jagora : Ai Ɗanladi ma ai ya biya bashina,

: Ai majidaɗi yara  ba ni son miƙawa,

: Domin Labbo mai kai dare daji,

: Kambazam magiro, ai sun biya sun kyauta,

: Ya ce in na sa kiɗi na bi hali nai,

: To in tai yana ban maraƙi kyauta,

: Maraƙinmu ya zan hannu,

: Tun da na kirai Labbo na huta,

: Ya  ba ni jikka guda da rabi.

 

Jagora : Kai ya ban dame bakwai sabilin zakka,

: Labbo ya taimakan ya kyauta,

: Allah ya riƙa ma mai taimakon bawanai,

: Labbo maƙigudu Labbo noma sabo.

: Riƙa ƙwarai Labbo Ɗan Maiyara,

: Shahe-zane,x2

: Ai  shahe-zane ga rana,

: Ƙi sake zakin kuluwa.

: Aiki dai bai kashe mutum sai dai rana.

 

  Jagora: Allah shi ka maganin wahala ko yaushe,

: Noma ka maganin yunwa na lura,

: Kai kura kwai ku zam aika a dai-dai,

: Ummaru rani da damana ka tsara aiki,

: Ita ko shawara ina ba aji ɗan babba,

: Ai ina namijin cen,

: Da mai biɗar ya ƙi ko yaushe.

Post a Comment

0 Comments