Ticker

Lauwali Tsare Bakin Aiki

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Lauwali Tsare Bakin Aiki

 G/Waƙa: Ya ci gona da niyya yas saba,

: Lauwali maganin sabrad[1] daji.

 Jagora: Haba banawa ku zan ƙwazon aiki.

 ‘Y/ Amshi: Babu mai bada samu sai Allah,

: Ya ci gona da niyya yas saba,

: Lauwali maganin sabrad daji.

 

Jagora: Kai dai Lauwal tsare bakin aiki,x2

 ‘Y/ Amshi: Gidanku ba a yada kayen noma ba.

: Ya ci gona da niyya yas saba,

: Lauwali maganin sabrad daji.

 

 Jagora: Gyara gona ka zan sa mat taki,x2

 ‘Y/ Amshi: Gidanku ba a yada kayen noma ba.

: Ya ci gona da niyya yas saba,

: Lauwali maganin sabrad daji.

 

 Jagora: Ɗan Mai tuwo yo alama Ɗan mantai,x2

 ‘Y/ Amshi: Mai dakaken ciyawa ɗan baushi,x2

: Ya ci gona da niyya yas saba,

: Lauwali maganin sabrad daji.

 

 Jagora: Haba banawa ku zan ƙwazon aiki,x2

 ‘Y/ Amshi: Babu mai bada samu sai Allah.x2

 

Jagora: In kaga ƙato da ragga raggo ne,

 ‘Y/ Amshi: Raggo na yalla bai kama aikin gona ba.

: Lawali maganin saurar daji.

 

Jagora: Kai dai Lawal.

 ‘Y/ Amshi: Tsare bakin aiki.

: Babu mai bada samu sai Allah,

: Ya ci gona tahiya ya saba.

 

 Jagora: In kaga ƙato da ragga raggo ne,

 ‘Y/ Amshi: Raggo na kila bai kama aikin gona ba,

: Ya ci gona da niyya yas saba,

: Lauwali maganin sabrad daji.



[1]  Gonar da ba a noma ba idan ta sunƙume da haki.

Post a Comment

0 Comments