Ticker

Limamin Da Ake Tunanin Yana Bugun-Ƙasa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Malami ne wani lokaci yana yin limanci a unguwa, amma waɗansu sun shaida cewa yana buga ƙasa, watau boka ne yana duba, waɗansu kuma sun ce ba su gani ba. To, yaya hukuncin limancinsa? Ya halatta a bi shi sallah? Jazaakumul Laahu Khairan.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuhu.

A asali kowane musulmi ana ɗaukarsa mutumin kirki ne na-gari, kuma ayyukan ibadarsa ingantattu ne, karɓaɓɓu a wurin Allaah Subhaanahu Wa Ta’aala (in Shã Allãh), sai lokacin da aka tabbatar da akasin haka. Don haka, wannan Limami sallarsa da limancinsa duk sun inganta har sai lokacin da aka tabbatar, ta sahihiyar hanya cewa ba musulmi ba ne. Tabbatar da wannan kuma, watau tabbatar da cewa wane kaza, wanda musuluncinsa ya riga ya tabbata, ya fita daga musulunci ya koma cikin kafirci, ba ƙaramin aiki ba ne. Domin sai an tabbatar da haɗuwar dukkan sharuɗɗa da koruwar dukkan abubuwan da suke hana kafircin sauka a kansa, kamar yadda malaman Aƙeeda da Tawheed suka yi bayani.

Samun waɗansu sun yi zargi ko ma sun yi shaidar cewa yana bugun-ƙasa bai isa dalili ba a kan tabbatar da haka, har sai lokacin da shugaban musulmi (Sarkin Musulmi ko Alƙalin Musulunci) ya bincika kuma ya tabbatar da gaskiyar hakan a shariance. Amma kafin a samu tabbacin hakan sai mu tsaya ga maganar da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya faɗa:

يُصَلُّونَ لَكُمْ ، فَإِنْ أَصَابُوا فَلَكُمْ وَلَهُمْ ، وَإِنْ أَخْطَأُوا فَلَكُمْ وَعَلَيْهِمْ

Suna yi muku limancin sallah, to idan suka dace ku da su duk kun dace, idan kuma suka yi kuskure to, ku kun dace su kuma suna da laifi.

Amma duk da haka, idan akwai wani masallacin a kusa wanda aka san limaminsa ba shi da irin wannan halin da ake zargi, to gara mutum ya tafi can kawai domin samun natsuwa.

 WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DIcJIƘrWyLP0oBOMSnDi5P

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments