Ticker

    Loading......

Mai Galmak Kashin Haki Isah

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Mai Galmak Kashin Haki Isah

 

G/Waƙa: Ya yi an gani,

: Mai galmak kashin haki Isah.

 

Jagora: Ya yi an gani,

: Mai galmak kashin haki Isah.

 ‘Y/ Amshi: Ya yi an gani,

: Mai galmak kashin haki Isah.

 

 Jagora: Gidan Hamma za ni na.

‘Y/ Amshi: In kwance takaici ban rammai,

: Ya yi an gani,

: Mai galmak kashin haki Isah.

 

 Jagora: Yaro gahwarakka ga

 ‘Y/ Amshi: Manya

: Ya yi an gani,

: Mai galmak kashin haki Isah.

 

  Jagora: Ni dole in yi ma kiɗi,

‘Y/ Amshi: Ai shikka a zan tar da gero.

 

Jagora: Tilas in yi maka kiɗi

 ‘Y/ Amshi: Don ko ya bi baya jin rana.

 

  Jagora: Wandara ka biya kiɗi,x2

‘Y/ Amshi: Wata’ala ya ƙara mai girma.x2

 

Jagora: Abul azizu ka biya,

 ‘Y/ Amshi: Wata’ala ya ƙara mai girma

 

  Jagora: Gidan Hamma za ni na,

‘Y/ Amshi: Domin su ka son kiɗin noma.

: Ya yi an gani,

: Mai galmak kashin haki Isah.

 

Jagora: Ni dai abin da nig gani,

 ‘Y/ Amshi: Kyan Ɗanɗa ya gadi babanaix2.

 

  Jagora: Kowag gadi arziki,

‘Y/ Amshi: Sai ya yi shi duniya daidai.

 

Jagora: Gero na gidanka Isah,

 ‘Y/ Amshi: Yau kowat taho yana cisai.

 

  Jagora: Dawa na gidanka Isah,

‘Y/ Amshi: Yau kowat taho yana cisai.

 

  Jagora: Maiwa na gidanka Isah,

‘Y/ Amshi: Yau kowat taho yana cisai.

 

  Jagora: Masara na gidanka Isah,

‘Y/ Amshi: Yau kowat taho yana cisai.

 

Jagora: Shinkahwa na gidanka Isah,

‘Y/ Amshi: Yau kowat taho yana cisai.

 

Jagora: Wake na gidanka Isah,

‘Y/ Amshi: Yau kowat taho yana cisai.

 

 Jagora: Gujiya na gidanka Isah,

‘Y/ Amshi: Yau kowat taho yana cisai.

 

 Jagora: Kuɗɗi gas u nan ga Isah,

‘Y/ Amshi: Yau kowat taho yana cisai.

 

Jagora: Abul azizu ya biya,x2

‘Y/ Amshi: Wata’ala ya ƙara mai girma,x2

 

Jagora: Na gode ma Madugu,

 ‘Y/ Amshi: Wata’ala ya ƙara mai girma

: Ya yi an gani,

: Mai galmak kashin haki Isah.

 

 Jagora: Wandara ka biya kiɗi,

 ‘Y/ Amshi: Wata’ala ya ƙara mai girma,x2

 Jagora: Kun ga Magaji sarki na,

 ‘Y/ Amshi: Wata’ala ya ƙara mai girma,x2

 

 Jagora: Gidan Hamma ba Bahili,

 ‘Y/ Amshi: Yau kowat taho suna cisai.

 

  Jagora: Kwatarmawa akwai maza,

‘Y/ Amshi: Yau kowat taho suna cisai.

Post a Comment

0 Comments