Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali Sububu. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Mai Gidan Nasara (Ta farko)
Ana kiransa da suna Muhammadu Sani, wasu suna kiransa Autan
Yaya, amma an fi ce masa Noma, saboda shahararsa ga noma. Abokin wasan
(taubashin) Amali ne, mutumen garin Kuzi ne da ke cikin mazaɓar Faru da
ke cikin ƙaramar hukumar Maradun.
G/Waƙa : Ka yi sunan noma,
: Mu gaisai da
aiki,
: Mai gidan Nasara,
: Ɗan da yat
tara damma.
Jagora: A
jinjina[1] a
aje,
: Ba shi komi da hwata,x2
: Tunkuɗa[2]
yaro,
: Ba ta komi da dutsi.
‘Y/Amshi:
Noma jan zaki,
: Mai wa yaro
kujera[3].
: Ka yi sunan
noma,
: Mu gaisai da
aiki,
: Mai gidan
Nasara,
: Ɗan da yat
tara damma.
Jagora: Gajere abun da yawa,
: Inda baƙon Habibu,
: Ina gida wani
bin,
: Hankalina ka tashi,
: Ga ni can wani
bin,
: Zuciyata ta yo nan,
: In biyo hanya,
: In taho in da Mamman,
: Ko da niz zaka.
‘Y/Amshi:
Sai hankali na ya kwanta,
: Ka yi sunan
noma,
: Mu gaisai da
aiki,
: Mai gidan
Nasara,
: Ɗan da yat
tara damma.
Jagora: Sai hankali na ya kwanta,
: Ka yi sunan
noma,
: Mu gaisai da
aiki,
: Mai gidan
Nasara,
: Ɗan da yat
tara damma.
Jagora: Dut
inda niz zaka[4],
‘Y/Amshi:
Sai hankali na ya kwanta,
Jagora: Yanzu kam Mamman,
: Sai ka hausan
ga doki,
: Wanda za ni gwada[5] wa,
: Gida can ga
dangi,
: In yi mai
turke,
: Masu sona su
duba,
: Gashi dai
nauna ba,
: Giri babu
mashi,
: Ko na hwan huɗu ne.
‘Y/Amshi:
Noma na so ka bani,
: Ka yi sunan
noma,
: Mu gaisai da
aiki,
: Mai gidan
Nasara,
: Ɗan da yat tara damma,
Jagora: Kuma in akwai hali,
: Ba matcewa ga
dokin,
: Ko jiran ka
nikai,
: Hak ka dubo Talata,
: Kasuwam Mahwara.
‘Y/Amshi:
Mai dawaki da shawa.
: Ka yi sunan noma,
: Mu gaisai da aiki,
: Mai gidan Nasara,
: Ɗan da ya tara
damma.
Jagora: Noma wa nane dum,
: Nu ɗauko ta
tushe,
: Ɗan uwana ne,
: Wanda yak kai
jimilla,
: Lissahin da
nikai,
: Tamu kaka
halima,
: Mai biɗaj jikan
gona.
‘Y/Amshi:
Ku za ya dibi,
: Ka yi sunan
noma,
: Mu gaisai da
aiki,
: Mai gidan Nasara,
: Ɗan da yat
tara damma,
Jagora: Wanga ko wajje,
: Noma Jikan Salau ne,
: Irin gidan
Abdu,
: Jan kada dama gurbi[6],
: Taƙamad da nikai,
‘Y/Amshi:
Taka ce don kaji ta,
: Ka yi sunan
noma,
: Mu gaisai da
aiki,
: Mai gidan
nasra,
: Ɗan da ya
tara damma.
Jagora: Duniya
da yawa bani,
: Roƙon bahili,
: Ina ganin
zaure,
: Ba ni
kwana ga hanya,
: Na gano
shigihwa,
: Ba ni kwana ga
bukka,
: Na gano ɗaki,
‘Y/Amshi:
Ba ni kwana ga zaure,
: Ka yi sunan
noma,
: Mu gaisai da
aiki,
: Mai gidan
Nasara Ɗan da,
: Ya tara damma,
Jagora: Yawan hwarauta,
: Mai tsunke Gyado[7] ga
daji,
: Shi da ba rame,
: Ba wurin molaƙewa,
: Sai ya dunga
gudu,
: Har a cimmai
akame,
: Shi na iyaka
yi nai,
‘Y/Amshi:
A ci mai mutunci.
: Ka yi sunan
noma,
: Mu gaisai da
aiki,
: Mai gidan
Nasara,
: Ɗan da yat tara damma,
Jagora: Mai kwaɗan nama,
: Sai ya dawo ga
tuji,
: Don ganin
suturar,
: Mujiya gat ta jaka,
: Ina ganin
gashin mujiya,
: Manya-manya,
: Koda nit tona.
‘Y/Amshi:
Mujiya babu nama,
Jagora: Amali na gane mujiya,
‘Y/Amshi:‘Yak
kaɗan ta.
: Ka yi sunan
noma,
: Mu gaisai da
aiki,
: Mai gidan
Nasara,
: Ɗan da yat tara damma[8].
[1] A ɗauki
abu don a ji kwatancin nauyinsa.
[2] Turawa.
[3] A zaunar da mutum saboda ya kasa ko an tsare
masa.
[4] Zowa/tahowa
[5] Nunawa
[6] Inda ruwa ke kwantawa a rafi ko tafki da
sauransu.
[7] Wata dabba mai haƙora gaye-gaye,
wanda ke tono rame das u ya shige.
[8] Ɗaure-ɗauren gero ko dawa
ko wani abu.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.