Mai Girma Sardaunan Sakkwato, Alhaji Sir Abubakar Alhaji

    Mai Girma Sardaunan Sakkwato, Alhaji Sir Abubakar Alhaji

    Mai Girma Sardaunan Sakkwato, Alhaji Sir Abubakar Alhaji Ɗan Sarkin Shanun Sakkwato Alhaji Muhammadu da aka fi sani da Sarkin Shanu Alhaji Ɗan Malam Haliru Ɗan Malam Bara'u Ɗan Malam Muhammadu Buhari Ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi. An fara sarautar Sardauna a Sakkwato a lokacin mulkin Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman (1817-1837), wanda ya fara naɗawa shi ne Malam Halilu Ɗan Malam Hassan Ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio ya kuma bashi Hakimcin Garin Marnona. Allah ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.

    Daga Taskar

    Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
    ÆŠanmadamin Birnin Magaji
    Imel: birninbagaji4040@gmail.com
    Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.