Mai Girma Sarkin Yaƙin Katsina

Mai Girma Sarkin Yaƙin Katsina

Alhaji Mamman Ifo Allahu ya taimake ka... 
Inji Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun a faifan sa na Marigayi Mai Girma Ciroman Katsina, Janaral Hassan Usman Katsina mai amshi " Mai ban tsoro sadauki, Hassan ɗan Shehu Malan". 
Yana nufin Marigayi Sarkin Yaƙin Katsina, Alhaji Mamman Ifo. A wannan hoton kuma Mai Girma Sarkin Yaƙin Katsina na yanzu ne, kuma Ɗan Marigayi Sarkin Yaƙin Katsina, Alhaji Mamman Ifo, watau Alhaji Bello Mamman Ifo. Allah ya jiƙan Magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.

Daga Taskar

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments