Maigidan Nasara (Ta biyu)

    Citation: BunguÉ—u, U.H. (2022). WaÆ™oÆ™in Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Amali  Sububu

    Maigidan Nasara (Ta biyu)

    Noma Autan Yaya shi ne sunan Maigidan Nasara, taubashin Amali ne (abokin wasansa), mutumen  garin Kuzi ne na mazaÉ“ar Faru da ke cikin Æ™aramar hukumar Maradun a jihar Zamfara. Shi ma manomi ne wanda yake noma amfanin gona, hakan ya sa Amali ya yi masa waÆ™a. Na sami wannan waÆ™ar ne bayan na taÉ“a samun wata wadda na kawo a sama, sai na ga akwai wasu ‘yan bambance-bambance, bayan na yi shawara da malamina sai muka ga cewa a sa su duka su biyun.

     

     G/WaÆ™a : Ya yi sunan noma,

       : Mu gaisai da aiki,

       : Mai gidan Nasara,

    : ÆŠan da yat tara damma.

     

        Jagora: A jinjina a aje,

    : Ba shi Komi da hwata, x2

    : TunkuÉ—ay yaro,

    : Ba ta Komi da dutci,

    : Noma jan zaki ,

        ‘Y/Amshi: Mai wa yaro kujera[1].

    : Ka yi sunan noma,

       : Mu gaisai da aiki,

       : Mai gidan Nasara,

    : ÆŠan da yat tara damma.

     

        Jagora: Mijin Rahammu,

    : Na ‘Ya’inna,

    : Baban Habibu,

    : Ina gida wani bi,

    : Hankalina ka tashi,

    : Ga ni can wani bi,

    : Zuciyata ta yo nan,

    : In biyo hanya,

    : In taho inda Mamman,

        ‘Y/Amshi: Ko da nig ga ka sai,

    : Hankalina ya kwanta.

    : Ya yi sunan noma,

       : Mu gaisai da aiki,

       : Mai gidan Nasara,

    : ÆŠan da yat tara damma.

     

        Jagora: Duk inda nig gaka sai,

    : Hankalina ya kwanta,

       ‘Y/Amshi: Sai hankalina ya kwanta,

    : Ya yi sunan noma,

       : Mu gaisai da aiki,

       : Mai gidan Nasara,

    : ÆŠan da yat tara damma.

     

        Jagora: Yanzu kau Mamman,

    : Sai ka hausan[2] ga doki,

    : Wanda  za ni gwada,

    : Wa gida can ga dangi,

    : In yi mai turke,

    : Masu sona su diba,

    : Ga shi dai nau ne,

    : Ba biri babu mashi,

       ‘Y/Amshi: Ko na hwan huÉ—u ne,

    : Noma na so ka ba ni,

    : Ya yi sunan noma,

       : Mu gaisai da aiki,

       : Mai gidan Nasara,

    : ÆŠan da yat tara damma.

         

              Jagora: Kuma in akwai halin,

    : Ba matcewa ga dokin,

    : Ko jiranka nikai,

    : Hak ka dibo Talata, 

           ‘Y/Amshi: Kasuwam Mahwara,

    : Mai dawaki da shawa.

    : Ka yi sunan noma,

       : Mu gaisai da aiki,

       : Mai gidan Nasara,

    : ÆŠan da yat tara damma.

     

        Jagora: Noma wana ne,

    : Don mu É—auko ta tushe,

    : ÆŠan’uwana ne,

    : Wanda yak kai jimilla,

    : Lissafin da nikai,

    : Tamu kaka Halima,

    : Mai biÉ—aj jikan,

    : Gona Buda ya bini,

        ‘Y/Amshi: Jikan gona Buda ya bini.

    : Ya yi sunan noma,

       : Mu gaisai da aiki,

       : Mai gidan Nasara,

    : ÆŠan da yat tara damma.

     

        Jagora: Wanga kau wajjen,

    : Noma jikan Salau ne,

    : Irin gidan Abdu,

    : Jan kada dama gurbi,

    : Taƙamar da nikai,

    : Taka ce ÆŠan Tahida.

        ‘Y/Amshi: Ya yi sunan noma,

       : Mu gaisai da aiki,

       : Mai gidan Nasara,

    : ÆŠan da yat tara damma.

     

        Jagora: Duniya da yawa,

    : Ba ni roƙun Bahili,

    : Ina ganin zaure,

    : Ba ni kwana ga hanya,

    : Na gano shigihwa[3],

    : Ba ni kwana ga bukka,

    : Na gano É—aki,

    : Ba ni kwana ga zaure.

        ‘Y/Amshi: Ya yi sunan noma,

       : Mu gaisai da aiki,

       : Mai gidan Nasara,

    : ÆŠan da yat tara damma.

     

        Jagora: Yawan hwarauta mai,

    : Tsunke gyado ga daji,

    : Shi da ba rame,

    : Ba wurin molaƙewa,

    : Sai ya dunga gudu,

    : Har a cimmai a kame,

    : Yana iyakay yi,

    : Nai a ci mai mutunci.

        ‘Y/Amshi: Ya yi sunan noma,

       : Mu gaisai da aiki,

       : Mai gidan Nasara,

    : ÆŠan da yat tara damma.

     

        Jagora: Mai kwaÉ—an nama,

    : Ce ya dawo ga tuji,

    : Don ganin suturar,

    : Mujiya kay ya ja ka,

    : Ina ganin gashin,

    : Mujiya manya-manya,

    : Ko da nit tona,

    : Mujiya ‘yak kaÉ—an ce.

        ‘Y/Amshi: Mujiya ‘yak kaÉ—an ce,

     

        Jagora: Amali na gane,

    : Mujiya yak kaÉ—an ce,

        ‘Y/Amshi: Mujiya yak kaÉ—an ce,

    : Ya yi sunan noma,

       : Mu gaisai da aiki,

       : Mai gidan Nasara,

    : ÆŠan da yat tara damma.

     

        Jagora: Ya yi sunan noma,

       : Mu gaisai da aiki,

       : Mai gidan Nasara,

    : ÆŠan da yat tara damma.

         ‘Y/Amshi: Ya yi sunan noma,

       : Mu gaisai da aiki,

       : Mai gidan Nasara,

    : ÆŠan da yat tara damma.



    [1]  A zaunar da mutum saboda ya kasa ko an tsare masa.

    [2]  Saya man.

    [3]  Shigifa

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.