Malan Shekarau Na Girnace

    Citation: BunguÉ—u, U.H. (2022). WaÆ™oÆ™in Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Amali  Sububu

    Malan Shekarau Na Girnace

    Malam Shekarau a garin Girnace yake na yankin Isa ta jihar Sakkwato. Yana aikin gona sosai, hakan ya sa Amali ya yi masa waƙarsa.

     

       G/WaÆ™a : Koma gona ga haki Malan,

    : Masu kai dare gona.

     

    Jagora: Malam Shekarau na Girnace,

     ‘Y/Amshi: Malan Shekarau na Girnace,

    : Wahala ba ta biyo gidanai ba.

     

    Jagora: Niyya ÆŠan  Sa’idu,

    : Sa ma haki wahala,

       ‘Y/Amshi: Niyya ÆŠan  Sa’idu,

    : Sa ma haki wahala,

    : Mu ga ka ci ƙarhi nai.

     

      Jagora: Ni yau Girnace nikai da kiÉ—i,

        ‘Y/Amshi: Ni yau Girnace nikai da kiÉ—in aiki.

    : In gano mazan hwama[1].

     

       Jagora: Mamman Girnace nikai da kiÉ—i.

        ‘Y/Amshi: Ni yau Girnace nikai da kiÉ—in aiki,

    : In gano mazan hwama.

    : Koma gona ga haki Malan,

    : Masu kai dare gona.

     

        Jagora: Malan ya kira ni,

    : Ya yi biyan doki.x2

             ‘Y/Amshi: Malan ya kira ni,

    : Ya yi biyan doki.

    : Yanzu niy yi zama[2] tai.x2

     

       Jagora: Amma Hushe ta kyauta,

       ‘Y/Amshi: Ta ban sirdi

    : Na ji ta yi mai kawu.

     

       Jagora: ‘Yakkware ta kyauta,

        ‘Y/Amshi: Ta ban sirdi.

    : Na ji ta yi ma kawu,

       : Koma gona ga haki Malan,

    : Masu kai dare gona.

     

        Jagora: Malan Shekarau na Girnace,

         ‘Y/Amshi: Malan Shekarau na Girnace wahala,

    : Bata biyo gidanai ba.

    : Koma gona ga haki Malan,

    : Masu kai dare gona.

      Jagora: Goje duk kag ganai yana,

    : Kwan nan-kwan nan,

    : Ya zama mahelheci,

    : Ya zan sha-ka bani,

    : Ya zama tunhwaya, 

       ‘Y/Amshi: Ya zama tunhwaya[3] ,

    : Ban iya yi mai hira.

     

       Jagora: Ƙato duk kag ga yana,

    : Yawon iska,

    : Ya zama duman rani,

    : Wannan ya É“akita,

    : Ya zama tunhwaya,

    : Ya zama duman rani.

        ‘Y/Amshi: Ya zama duman rani,

    : Koma gona ga haki Malan,

    : Masu kai dare gona.

     

       Jagora: Niyya ÆŠan Sa’idu,

    : Sa ma haki wahala,x2

       ‘Y/Amshi: Niyya ÆŠsn Sa’idu,

    : Sa ma haki wahala,

    : Mu ga ka ci ƙarhinai.x2

    : Koma gona ga haki Malan,

    : Masu kai dare gona.



    [1]  Manyan manoma.

    [2]  Sukuwa da doki don nuna gwaninta.

    [3]  Ciko, wato idan wani mazubi bai cika ba sai a tunhwaye.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.