Ticker

Mamman Kanen Mani

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Mamman Ƙanen Mani

G/Waƙa: Koma daji masarin burburwa[1]

: Mammn zarin Mani.

 

Jagora: Koma daji ƙanen Mani.

‘Y/ Amshi: Koma gona tsare noma.

 

  Jagora: Mamman Gojen waɗan Mahwara.

‘Y/ Amshi: Mamman Ganɗon mutan Mahwara.

 

Jagora: Mamman Zakin mutan Mahwara.

‘Y/ Amshi: Mamman Ganɗon mutanen Jangebe

: Ganɗon mutan Rini.

: Koma daji masarin burburwa

: Mammn zarin Mani.

 

Jagora: Ɗan Baraya nagode ya kyauta,

‘Y/ Amshi: Shi ma ban rena kyauta ba

: Wada duk aka yi yana yo ma Daudu.

.: Yaw a Karo komi.

 

Jagora: Wada duk aka yi….

‘Y/ Amshi: Aka yi yana yo ma Daudu,

: Ya wa Karo komi.

Jagora: Mani mai sumak kashin kuɗɗi.

‘Y/ Amshi: Mani ban rena kyauta tai,

: Shi ma ban rena kyauta ba

: Wada duk aka yi yana yo ma Daudu.

.: Yaw a Karo komi.

 

Jagora: Mai ƙasumba Mani na gode.,

‘Y/ Amshi: Shi ma ban rena kyauta ba

: Shi ma yaw a Karo komi,

: Wada duk aka yi yana yo ma Daudu.

.: Yawa Karo komi.

 

Jagora: Mamman Gojen waɗan Mahwara,x2

‘Y/ Amshi: Mamman Ganɗon mutanen Jangebe

: Ganɗon waɗan Rini.x2

: Ga noma ba a ce ma ɗanyaro,

: Komi duhu yai yi.

.

Jagora: Tahi gona gazayen Mani.

‘Y/ Amshi: Tahi wa aiki irin noman dole,

: Ka gama da sayyunai.

.

Jagora: Tahi gona ginshiƙin Mani

‘Y/ Amshi: Tahi wa aiki irin noman dole,

: Ka gama da sayyunai.

 

Jagora: Ladan Gilbaɗi na halin girma

‘Y/ Amshi: Shi ma ban rena kyauta ba,

: Kuma ga taggon ga mai ƙwari,

: Don albarkar kiɗin noma yab ban.

: Ya wa Karo komi.

 

  Jagora: Kowac ce maka baya son noma,

: Hay yaz zama ba ka tsoronai,

‘Y/ Amshi: Ce mai wahala ga kainai taƙ ƙare.

: In ba ya tsoronai.

 

Jagora: Kowac ce ma zaya cin-rani,

: Hay yaz zama ba ka tsoronai,

‘Y/ Amshi: Ce mai wahala ga kainai taƙ ƙare.

: In ba ka tsoronai.

: Koma daji masarin burburwa,

: Mammn zarin Mani.

 

Jagora: Na gode maka Audu ja-gaba

‘Y/ Amshi: Ya kai gojen hwaɗi Iliya

: Shi gojen hwaɗi Iliya

: Shi yab bamu shinkahwa

 

Jagora: Na gode maka Audu ja-gaba.

‘Y/ Amshi: Shi ma ban rena kyauta ba,

: Shi ma ya ba kari daɗi

: Kuma ga janhwag ga mai ƙwari ya ban.

: Ban rena kyauta ba.

 

Jagora: Audu gajere nai muna alheri.

‘Y/ Amshi: Shi ma ban rena kyauta ba.

 

Jagora: Audu gajere nai muna alheri

‘Y/ Amshi: Shi ma ban rena kyauta ba,

: Wada duk aka yi yana yo ma Daudu.

: Ya wa karo komi.

 

Jagora: Na gode ma Rabbani,x2

‘Y/ Amshi: Da niz zaka nan kiɗin noma,

: In gaida irin masoyana Daudu,

: Mu ga masu ƙauna ta.x2

 

Jagora: Raggo ya sha baƙay yunwa

: Kuma babu kwabon kashi birni,

: Kuma ba tsabad daka birni,

: Sannan ya sami goranai,

: Sannan ya ɗauki sandatai,

‘Y/ Amshi: Mai ƙarhi na baran sauran yaro,

: Yunwag ga ba dama.x2

: Koma daji masarin burburwa

: Mammn zarin Mani.

 

Jagora: Koma gona biɗo gero

‘Y/ Amshi: Mamman barka da saran burburwa,

: Mammn zarin Mani.



[1]  Wata ciyawa ce wadda manoma kan sare ta wajen noma don su gyara shukarsu.

Post a Comment

0 Comments