Ƙilu ta Ja Bau - Uku
Kukurukuuuu! Zakaran gidan ɗaya tilo ya yi cara da asubahin fari babu wanda ya motsa. Can ya sake yi iya karfinsa ya ji shiru. Ba da daɗewa ba ya daddage ya kuma tsallara ihu amma a banza. Sai ya koma cikin akurkinsa ya kwanta ya ce "Ni dai na fita wAllahi."
Jim kaɗan
Maigidan ya fito daga ɗakinsa
ashe ya tashi. Ya ɗauki
butarsa ya ji fayau babu ruwa. Har ya juya ya kalli ɗakin da ya fito zai kama faɗa sai ya lura har yanzu
gari bai waye ba ya ja bakinsa ya yi shiru. Kar ya manta Baaba tana ɗaki kar ya tashe ta.
Ya je jikin randa ya sa kofi don debo ruwa sai nan ma ya
karci ƙasar
randar babu ko ɗigo.
Ya mike a fusace ya yi tsaki ya wurga kofin cikin randar yana huci. Ya juya zai
je ya tashi matarsa je nan sai ya ga mahaifiyarsa ta fito daga ɗakinta ita ma da buta a
hannu.
Kafin ta yi magana ya yi sauri ya rusuna ya gaisheta cikin
murya tattausa ta amsa masa ba gaba ɗaya
ba don ba su yi sallah ba. Ta wuce shi ta shiga banɗakin gidan da kowa ke amfani da shi. Kafin ta
fito ya ɗauki guga ya
jawo ruwa a rijiya ya zuba a butarsa.
Da babarsa ta fito ya kar6i butarta ya cika mata shi da ruwa
cikin girmamawa ta kar6a a zaune kan wata kujera a bakin makwarara ta kama
alwala. Shi kuma ya shiga ban ɗakin
yana takatsantsan kar ya saki tusa uwar ta ji. Ya yi ɗahara ya fito.
Da ya fito ya ga Baaba ta gama alwala har ta koma ɗaki
shi ma sai y zauna inda ta tashi ya ɗaura
tasa alwalar. Yana cikin haka Ladanin masallacinsu ya kama kiran sallah da shaƙaƙƙiyar
muryarsa. AlhamdulilLaah ya dai fi dubu da suke ƙudundune a cikin bargonsu.
Bacin ya kammala alwalar ya shiga ɗaki ya lalubo hula ya sa ya ce "Na tafi
masallaci. Tashi ki zo zaure ki rufo kofar saboda tsaro" Matarsa ta yi
wani juyi ta gyara kwànciya ta ce "Na ji." Amma shi gurnani kawai ya
ji kafin ya fita ya ce "Kar fa in dawo ba ki tashi ba."
Wajen ƙarfe 6:30 na safe gari ya gama washewa Maigidan ya dawo zai ƙwanƙwasa
kofar ke nan a zo a buɗe
masa sai ya samu kofar yadda ya barta wato ba a rufe ba. Nan take ya fusata ya
banki kofar cikin gaggawa ya kutsa ta zauren ya shiga gidan.
Nan ma zai soma faɗa
a tsakar gida ke nan ya tuna cewa Baabarsa fa na nan. Ya yi sauri ya yiwa
fushinsa linzami ya wuce ɗakin
tsohuwar ya tsaya baƙin kofa ya yi sallama "Assalam alaikum Baaba in
shigo?" cikin ladabi da sassauta murya. Ta ce masa "Wa alaik assalam
e shigo."
Ya shiga a durƙushe ya zube a gabanta kansa a duƙe
"Baaba ina kwana?" Ba ta amsa masa kai tsaye ba sai da ta ida
addu'o'inta ta shafa ta ajiye carbinta sannan ta ce da shi "Nabaaba lafiya
lau." ya bi ta da "Ina gajiya? Ya jiki jikinki naki?" Ta ce da
shi "AlhamdulilLaahi."
Suka dai gaisa har suka shiga hira yana me take so ya sayo
mata na magunguna tunda ta ce bayanta na yi mata ciwo. Ko dai ya kaita asibiti
ne ko ya kira mata Dakta Halliru ɗan
wansa da ya karanci aikin likita yana aiki a Asibitin Aminu Kano? Ta ce da shi
a'a ya bar shi.
Bacin ya gama gaida babarsa ya tashi ya fito daga wajenta
tana shi masa albarka sai ya shiga ɗakinsa
nan ma da sallamarsa "Assalam alaikum." Ya ji kamar an amsa masa amma
fa a cikiciki. Ya nemi waje ya zauna ya ajiye hularsa a gefensa matarsa na
kwance akan gado.
Bayanta na juye ko ta juyo ta kalle shi. Ya ce da ita
"Wai ba ki tashi kin yi sallah ba ne? Ba na ce kar in dawo in same ki a
kwance ba?" Ya saurari ya ji amsa ba ta ce da shi ufan ba. Sai ya ɗora zance a kai "Sannan na ce ki bi ni ki rufo
mana kofar gidan nan, nan ma haka na dawo na samu ba ki rufo ta ba. Ko me
yasa?"
Ta ce "Na rufo ta mana sake komawa na yi na buɗe ta da na gama
sàllah." Ya yi shiru bayan ta gama magana. Bai san sanda ya ɗaga muryarsa cikin bacin
rai ya ce "Kin ga kar ki kawo mun rainin wayo kin ji ko wannan kofar ba ki
rufe ta ba malama!" Ta ce "Na rufo ta."
"To shike nan kin rufo. Kin ce kin yi sallah ko? Wai me
yasa na tashi butata babu ruwa ko na ɗahara
ba ma na alwala ba? Ban ce ki daina bar mun ita haka ba?" Su ka yi shiru
na ‘yan daƙiƙoƙi ta
buɗa baki za ta yi
magana ya ce "Ga shi ko gaishe ni ma ba ki yi ba!"
Ta yi masa wani irin kallon reni kai ka ce wani ne wanda bai
isheta kallon biyu ahu ba. "Yau wajen kwana biyar ke nan kullum na shigo
ni ne zan ce miki ina kwana? Wato kin fi ƙarfin ki fara gaishe ni ke nan ko me kike
nufi?" "To menene don ka fara gaishe ni? Ni ba matarka ba ce?"
Ta kada baki ta tambaye shi.
Ya ɗauke
wuta na wani ɗan
lokaci don tsananin mamaki! "Me kika ce?! Sake faɗa in ji ki da kyau tukunna! Ni kike cewa
menene don na fara gaishe ki? Wato don ƙarfin hali har tambayata kike ke ba
matata ba ce? Ikon Allaah." Ya faɗa
cikin kogin tunani ya yi shiru.
Shin anya kin san ko ni waye kuwa? Kin San matsayinsu a
rayuwarki kuwa? Ni fa ni ne mijinki wanda Allaah SWT Ya yi ki don ni! Ashe wata
sa6uwar fitsara kika tsinto ban sani ba? Wato ni mijinki nine zan dinga gaishe
ki duk wayewar garin Allaah? Yau zan ga rashin kunya! Kai!" ya tashi tsaye
yana kallonta.
"Ai Sunnah ce! Sunnar Annabi ce miji ya fara gaida
matarsa kuma ya gaishe ta safe da rana da yamma. Kai ka fi Annabi ne?" Ya
ji wani irin surrr daga wuyansa ya yi ƙasa. Can ya buɗe bakinsa ya ce da ita "Da kyau. Lallai
ban fi Annabi SAWS. Ke ko ubana bai kai darajar takalminsa ba wAllahi."
"Kuma kin yi gaskiya kam Manzo SAWS shi ne yake bibiyar
ɗakunan matansa tara
(9) kowacce ya je su gaisa ya tambayi lafiyarsu damuwarsu buƙatunsu
da dai sauransu. Ni kuwa don Allaah in tambaye ki mana; Matana nawa ne?"
Ya jira ta ba shi amsa amma ya ji shiru. "Ba ki da amsa ne? Na ce ku nawa ne?!"
Nan ma said ya sake ɗora
mata amsa ya ce "To alhamdulilLaah. Tunda abinda kike so in dinga yi ke
nan wato shiga ɗakunan
matana ina gaishe su to in sha Allahu abindaa zai fara faruwa ke nan
kwanakwanan nan. Zan tabbatar miki da kasancewar hakan! Buri ki zai cika
taf"
Ai kan ka ce kwabo matar nan ta dirgo daga kan gado ta durƙusa a
gaban mijin ta kama ba shi haƙuri tana ta tuba tana neman gafararsa.
Hawaye shar6e-shar6e tana ce da shi "Malam don Allaah don Annabi na tuba!
wAllaahi ba abinda nake nufi ba ke nan." Ya yi gum yana kallonta da wani
murmushin ƙeta
a fuskarsa.
Ta ba shi haƙurin duniyar nan amma ina! Dama ya daɗe yana son ya ƙara
aure amma saboda zaman lafiya, so da ƙauna da suke ga iyayenta mutanen kirki ya
rasa ta inda zai 6ullo mata sai ga shi bagatatan ya tsinci dami a kala. Ai kuwa
bai 6ata lokaci ba yanzu matansa hudu (4)
Da yake yana Allaah Ya yi masa arziƙi Dan kasuwa ne Yana samu
akai akai nan da Nan ya same aka gina masa mai bangare hudu ya auri wasu Mata
uku a gufi a gufi. Kuma kowacce ya kama zuwa gidanta don ya dinga gaisheta. Ma
sha Allaah.
Daga baya ma aka ce ita matarsa ta fari ta yi yaji akan ko mene ne ma... Yauwa wai in ya je bangarenta ba ya tsayawa ya daɗe yana hira kamar yadda ta samu labarin yana yi a wajen sauran mata. Ya ji tsoron Allaah ya dinga kwatanta aldalci fa. Yanzu dai ko ta dawo shi ne ba a sani ba.
Daga Taskar
Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
Imel: mmtijjani@gmail.com
Lambar Waya: +234 806 706 2960
A Kiyayi Haƙƙin Mallaka
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.