Ticker

6/recent/ticker-posts

Muhamman Dan Korau

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Muhamman Ɗan Korau

 

G/Waƙa: Wuce maza Ɗan Mantai,

: Muhamman Ɗan Korau,

: Sai mu ba shi tahwashenshi,

: Dogo Ɗan Kwaima.

 

  Jagora: Na Audu ko da rani,

: Bai saba kwana bedi ba,

 ‘Y/ Amshi: Kaga ya saɓi kwashenshi,

:  gonatai zaya.

: Wuce maza Ɗan Mantai,

: Muhamman Ɗan Korau,

: Sai mu ba shi tahwashenshi,

: Dogo Ɗan Kwaima.

 

  Jagora: Yaro bai saba ba.

 ‘Y/ Amshi: Bai saba aiki ba,

: Koda munka kwarare shi,

: Sai ya lallace.

 

 Jagora: Yaro bai saba ba,

 ‘Y/ Amshi: Bai saba aiki ba,

: Koda munka kwarare shi,

: Sai ya lallace.

: Wuce maza Ɗan Mantai,

: Muhamman Ɗan Korau,

: Sai mu ba shi tahwashenshi,

: Dogo Ɗan Kwaima.

 

 Jagora: Yau na taho da kiɗi inda,

‘Y/ Amshi: Inda dogo Ɗan Kwaima,

: Abin da munka bukata,

: Muhamman shi zai bai.

 

Jagora: Yau na taho da kiɗi inda,

  ‘Y/ Amshi: Inda dogo Ɗan Kwaima,

: Abin da munka bukata,

: Muhamman shi zai bai.

 

Jagora: Mamman na gode mai,

‘Y/ Amshi: Allah anfana,

: Sai mu ƙara yaba mai,

: Zaman ya kyauta man,

 

 Jagora: Abdu na gode mai.

 ‘Y/ Amshi: Allah anfana,

: Sai mu ƙara yaba mai,

: Zaman[1] ya kyauta man. 

 

 Jagora: Garba na gode mai.

‘Y/ Amshi: Allah anfana,

: Sai mu ƙara yaba mai,

: Zaman ya kyauta man, 

: Wuce maza Ɗan Mantai,

: Muhamman Ɗan Korau,

: Sai mu ba shi tahwashenshi,

: Dogo Ɗan Kwaima.

 

Jagora: Yaro bai saba ba,

  ‘Y/ Amshi: Bai saba aiki ba,

: Koda munka kwarare shi,

: Sai ya lallace.

 

 Jagora: Yaro bai saba ba,

‘Y/ Amshi: Bai saba aiki ba,

: Koda munka kwarare shi,

: Sai ya lallace.

: Wuce maza Ɗan Mantai,

: Muhamman Ɗan Korau,

: Sai mu ba shi tahwashenshi,

: Dogo Ɗan Kwaima.

 

 Jagora: Na taho da kiɗi inda,

‘Y/ Amshi: Inda dogo Ɗan Kwaima,

: Abin da munka bukata,

: Muhamman shi zai bai.

 

 Jagora: Na taho da kiɗi inda,

‘Y/ Amshi: Inda dogo Ɗan Kwaima,

: Abin da munka bukata,

: Muhamman shi zai bai.

: Wuce maza Ɗan Mantai,

: Muhamman Ɗan Korau,

: Sai mu ba shi tahwashen[2]shi,

: Dogo Ɗan Kwaima.



[1]  Saboda/domin/don

[2]  Kiɗa musamman na manoma.

Post a Comment

0 Comments