Mutuntarwa

     Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Bara da wasu waÆ™oÆ™in bara a Æ™asar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    Mutuntarwa

    Mutuntarwa tana nufin MawaÆ™i ya É—auki wata halayya ko É—abi’a ta mutum ya saka wa wani abu da ba mutum ba kamar dabba ko tsauni ko Æ™waro da sauransu, kuma ya kasance wannan halayyayr ko É—abi’ar mutum ne kawainaka san shi da ita. To amma wani lokacin abin yakan zama akasin haka, ÆŠangambo (2007:45). Misali:

     “Kura ta ga É—an bara É—an almajiri,

    Bari in bi ka É—an bara ko in san gari,

    Tafiyata da taki ba ta zama É—ai da É—ai,

    Ke ƙwace kikai ga mata ba su ba ki ba,

    Ni roÆ™o nikai ga mata ‘yan arziki,

    (Ya Tabaraka ya Rabbana)

    A layi na biyu na waÆ™ar da ta gabata an nuna almajiri yana zance da kura, ya faÉ—i ta faÉ—i. Ta ce za ta bi shi su shiga gari amma ya ce a’a, ya kuma gaya mata dalilansa na Æ™iyawa. A nan an nuna kura na magana tamkar yadda mutum ke yi kuma tana fahimta maganar mutum idan ya yi. Yin magana da fahimtar ma’anar da ke Æ™unshe cikin zance duka É—abi’u da halaye ne na mutum amma aka É—ora su ga kura wadda take dabba. To a nan an mutuntar da kura, wato an saka mata halaye da É—abi’u irin na mutum.

    A wani misalin daga wata waƙar cewa ake:

    Kogon kura na shiga,

    Ko na damisa na shiga,

    Sai tat taso man tsaye,

    Sai nic ce wa zaki ci,

    Sai tac ce mai magani,

    Sai na baÉ—e ta da magani,

    Kahin a jima ban gan ta ba.

    (Karatun Magani)

    A wannan waƙar mai suna karatun magani da almajiran ke bara da ita akwai mutuntarwa. An nuna mai shiga kogo ya haɗu da damisa har sun yi sa-in sa da juna. Wannan ka ce- na ce da ya shiga tsakani damisa da mai ɗibar magani halayya ce da aka san mutane da ita, amma sai ga shi ga damisa. To ke nan an mutuntar da damisa an ce tana magana yadda mutum yake yi.

    Duk da yake salon jinsantarwa kashi uku ne kamar yadda bayani ya gabata, kashi ɗaya ne kawi aka iya samo misalansa daga cikin waƙoƙin bara da na sami kaiwa gare su. Sauran kasusuwan biyu, wato dabbantarwa da abantarwa ba a sami misalansu ba.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.