Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Na Amadu giwa
G/Waƙa:
Ƙane
mutun ko ya ƙi ka,
:
Baya ce maka raggo.
Jagora
: Kai mutun ko ya ƙi ka,
: Ba
ya ce maka raggo.
‘Y/ Amshi
: Tunda har yanzu ba ka tai,
: Biɗar dami ga mutun
ba.
:
Sannu da sauran haka na Amadu giwa,
:
Gogarman Tumba ya gwada masu noma.
Jagora: Haba maza ku yi noma.
‘Y/ Amshi: Ku zan aje mana gero,
:
Wanda bai aje gero ba,
: Ban
buga masa turu .
:
Sannu da saran haki na Amadu giwa,
:
Gogarman Tumba ya gwada masu noma.
Jagora : To ashe yaro.
‘Y/ Amshi: Baya citta baya mazuru,
:
Tunda bai saba kai duhu ba ga noma,
:
Sannu da saran haki na Amadu giwa,
:
Gogarman Tunba ya gwada masu noma.
Jagora: To ƙane
ya ce ran juma’a,
‘Y/ Amshi: Kana ta biɗa ta,
: To
Allah ya kai mu juma’ar ga mu gaisai.
Jagora: Ƙane mutun ko ya ƙi
ka.
‘Y/ Amshi: Baya ce maka raggo,
:
Tunda ba ka zo biɗar dame ga mutun
ba.
Jagora: Ƙane mutun ko ya ƙi
ka,
‘Y/ Amshi: Ba ya ce maka huntu,
:
Tunda ba ka je biɗar tuhwa[1]
ga mutun ba.
:
Sannu da saran haki na Amadu giwa,
:
Gogarman Tunba ka gwada masu noma.
2.5.11
Salau Ɗan Nanaya
G/Waƙa: Ya yi gargare[2]
inda noma,
:
Yana gaba Salau Ɗan Nanaya.
Jagora: Ka biya na mata na Salmo.
‘Y/ Amshi: Kar ka fasa noma na Garba.
Jagora: Sai dare na mata na Salmo.
‘Y/ Amshi: Kar ka hwasa noma na Garba,
: Ya
yi gargare inda noma,
:
Yana gaba Salau Ɗan Nanaya.
Jagora: Ɗan amale ya zan
amale,x2
‘Y/ Amshi: Shirya Salau ka gado
Nanaya,x2
: Ya
yi gargare inda noma,
:
Yana gaba Salau Ɗan Nanaya.
Jagora: Ɗan yaƙubu.
‘Y/ Amshi: Yana inda noma,
: Bai
kula da rana ba daji.
Jagora: Ɗan amadu,
‘Y/ Amshi: Yana inda noma,
: Bai
kula da rana ba daji.
: Ya
yi gargare inda noma,
:
Yana gaba Salau Ɗan Nanaya.
.
Jagora: Tun ba a daɗe ba,
: Ba
a jinjima ba,
‘Y/
Amshi:
Ba a jinjima[3]
ba,
:
Zuwa guda Salau ya yi doki.x2
Jagora: Ɗan Nanaya.
‘Y/ Amshi: Ya bamu doki,
: Daɗa a bamu tauna ta dokin.
Jagora: Yaƙubu
yana taimaka man.
‘Y/ Amshi: Saboda kai Salau ya biyani.
Jagora: Abubakar yana taimaka min.
‘Y/ Amshi: Saboda kai salau ya biya ni.
: Ya
yi gargare inda noma,
:
Yana gaba Salau Ɗan Nanaya.
Jagora: Ka biya ni mata na Salmo,
‘Y/ Amshi: Kar ka hwasa noma na Garba,
: Ya
yi gargare inda noma,
Jagora: Sai dare na mata na Salmo,
‘Y/ Amshi: Kar ka hwasa noma na Garba,
: Ya
yi gargare inda noma,
:
Yana gaba Salau Ɗan Nanaya.
Jagora: Ɗan amale ya zan
amale,x2
‘Y/ Amshi: Shirya Salau ka gado
Nanaya,x2
: Ya
yi gargare inda noma,
:
Yana gaba Salau Ɗan Nanaya.
Jagora: Na naya na yaba maid a girma,x2
‘Y/ Amshi: Saboda kai salau ya biya
ni,x2
: Ya
yi gargare inda noma,
:
Yana gaba Salau Ɗan Nanaya.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.