Ticker

Na Kama Mijina Yana Wasan Banza Da Ƙanwata Ƙarama.

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam, tambaya ta ita ce: Mace ce da mijinta ta taɓa kama shi yana ‘wasanni’ da ƙanwarta yarinya ƙarama a shekarun baya. A kan haka har aurensu ya kusa mutuwa, amma ta yi haƙuri saboda ya ce, ya tuba kuma ba zai ƙara ba. Don haka ita ma ba ta gaya wa kowa ba. To, a yan watannin baya kuma sai ta lura yana zuwa shimfiɗar yaranta idan ta farka da dare, yana cewa wai ya je gyara musu kwanciya ne! Ya ki yarda su tattauna maganar duk da ta nemi hakan, kuma ba ta ga alamar nadama a tare da shi ba tun daga karon-farko. Sannan kuma ya ki yarda ya shiga makaranta inda zai riƙa jin waazi. A gaskiya in ban da wannan matsalar yana da kyawawan halaye: Yana kulawa da zumunci, da kulawa da iyali da bayar da taimako gwargwado. Shawara ta ke nema, me ya kamata ta yi? Ko za a taimaka mata da laccocin da suke bayani a kan irin laifinsa? Allaah ya saka wa malam da alkhairi.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Allaah ya saka mana gaba-ɗaya.

1. Da farko: Gyara wa yaran kwanciya ya ce yake yi, kuma ba ki kama shi da ‘wasanni’ ba, irin na farko.

2. Kin tabbatar da cewa yana da kyawawan halaye da ɗabi’u, in ban da abin da ya auku a baya.

3. Ƙin yarda ku tattauna maganar ba dalili ne mai nuna cewa ya yarda ya aikata wasanni da yaranki ba.

4. Rashin ganin alamun nadama daga gare shi tun karon farko bai nuna cewa bai yi nadamar ba.

A ƙarƙashin wannan, ina ga matakan da suka kamata ta ɗauka, a babin shawara su ne:

1. Dole ki yi taka-tsantsan, kar ki bai wa shaiɗan dama ya shigo ya ɓata muku zamantakewa a tsakaninki da mijinki ‘mai kyawawan ɗabi’u’, kuma mahaifin ’ya’yanki.

2. Ki yawaita yin addu’a da neman ƙarin shiriya da kariya gare ki da shi kansa da sauran yaranki.

3. Ki ƙara sa ido da ɗaukar matakan kariya don tsare lafiyar ke kanki da yaranki.

4. Ki yawaita yi masa nasiha da jaddada buƙatar ya shiga makaranta, wataƙila daga baya ya yarda.

5. Ki kyautata zato gare shi bayan ya tuba, kar ki riƙa leƙen sirrinsa don gano ko tuban da gaske ne ko kuwa?! Yawanci, hakan ba ya gyara mai laifi, in ban da ma kangarar da shi yake yi.

Maganar leccocin Malamai a kan irin wannan laifin da ya yi kuwa, ina ganin amfaninsa a nan kaɗan ne ƙwarai. Ai babu wanda bai san cewa ‘wasannin banza’ da yara ƙanana wani mummunan laifi ne ba. Don haka, sanya masa kaset na lacca ko waazin wani malami a kan maganar zai zama kamar ƙoƙarin ƙure shi ne, da neman tona masa asiri kawai, wanda kuma hakan kan iya kai shi ga kangarewa.

Allaah ya kiyaye, kuma Allaah ya ƙara mana shiriya baki-ɗaya.

WALLAHU A'ALAM

Shaikh Muhammad Abdullah Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IƙsWWSpUkwk6b8hWJ6vXOO

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments