Ticker

Noma Babbas Sana’a

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Noma Babbas Sana’a

Ita wannan waƙa ya yi ta don noma nei, ya yi kira ga jama’a don su dawo ga sana’ar noma, an lura cewa a lokacin da ya yi waƙar mutane sun fara kauce wa sana’ar noma ne suna yin wasu sana’o’i, kamar hada-hadar man fetur da kwangiloli da saurnsu, sai Gwamnati ta umurci mawaƙa a lokacin da su juyo da hankulan jama’a wajen sana’ar noma, nan ne fa sai gogan naka ya yi wannan waƙar.

G/Waƙa: Noma babbar sana’a,

: Koway yi ta ya bar rasawa.

 

  Jagora: Kowa tsare noma daidai ne,

: Kowa aje gero da dawa,

: Wannan ya ɗebe takaici.

‘Y/ Amshi: Noma babbar sana’a,

: Kowa ya yi yabar rasawa.

 

  Jagora: Ka taimaki bayinka Allah,

: Allah shi ne mai iyawa,

: Ka taimaki bayin Allah,

: Allah shi ne mai iyawa.

‘Y/ Amshi: Noma babbar sana’a,

: Kowa ya yi ta ya bar rasawa.

 

  Jagora: Can dori Nijeriya ƙasarmu,

: Allah ya bada arzikin noma,

: Mu noma gero mu noma dawa,

: Ga shinkafa ga gyaɗa,

: Ga auduga muna noma,

: Ga masara kuma ga shinkafa,

: Ga acca kuma ga alkama muna noma,

: Arzikin man fetur ya motsa,

: Kasuwar man fetur ta katce,

: Munka watsar da noma,

: Munka koma a kan kwangiloli,

: Ga shi arzikin fetur ya ƙare ƙasar nan,

: Can ƙasashen da muke kaiwa,

: Kasuwar mai ta faɗi!

: To ‘yan Nageiriya yanzu me zamu komawa,

: Ƙara mu koma kan noma,

: Ƙara mu koma kan noma,

: Mu tara abinci kasarmu,

: Mu samu abinci da zamu ci,

: Mu samu abinci sutura kana mu,

: Nemi kuɗi mu kare mutuncin na kanmu,

: Mu kare mutuncin ƙasar ga,

‘Y/ Amshi: Mu kare mutunci na kanmu,

: Mu kare mutuncin ƙasar ga.

 

  Jagora: Kun san gero da dawa,

: Da sauran abunda za mu ci,

: Shi muka ci Najeriya, amma

: Auduga da gyaɗa to ita ce zamu ɗauka,

: Mu kai ta can ƙasashen waje,

: Mu sayar mu samo kuɗɗi,

‘Y/ Amshi: Mu kare mutuncin ƙasar ga

 

  Jagora: In mun samo kuɗi masu amfani,

: Kana mu gina masu amfani,

: Kayan amfanin gona ko’ina a kai,

: Mu kare mutuncin na kammu,

‘Y/ Amshi: Mu kare mutuncin ƙasarga

: Indai mun samu kuɗi da yawa,

: Ƙara mu je mu nemi ilimi,

: Mu kai ‘ya’yanmu su smu ilimi,

: Mu kare mutuncinmu na kanmu,

 

  Jagora: Mu kare mutuncin ƙasarga,

: Kowa ya kare mutuncin na ƙasarga.

: Ya ƙare mutuncin na kainai,

: Ya kare mutuncin ƙasarga,

: Noma babbar sana’a,

  Jagora: Wadaduk nikaso Najeriya,

: Mutane dun na hore ku,

: Manyan garuruwanmu,

: Kowane gari kazo,

: Kai hangi dala ta gyaɗa,

: Ka hangi dala ta auduga,

: Kowane gaya mun tara,

: Indai mun miƙa mun yi ƙwazo,

‘Y/ Amshi: Mun kare mutuncin ƙasarga.

 

  Jagora: Mun kare mutunci na kanmu,

‘Y/ Amshi: Mun kare mutuncin ƙasarga.

 

  Jagora: Darajar naira mu da ta faɗi,

‘Y/ Amshi: To kuma sannan zata dawo.

 

  Jagora: Darajar naira mu data ta faɗi,

‘Y/ Amshi: To kuma sannan zata dawo.

 

  Jagora: To kuma sannan ku ma’aikatan Najeriya,

: To ku tsaya a kan gaskiya,

: Kowa ya tsaya Allah,

: Kai ta tsaya ga naka aiki,

: Ni in tsaya ga nawa aiki,

: In mun yi hakan mu taimaki kanmu,

: Kar mu tsaya muna yin ƙeta,

: Muna cutar kanmu da kanmu,

: Kai babba ka shirga ɓarna,

: Sannan ka ce yaronka bai yi,

: Kowa duk ya tsaya ya dage,

: Mu kare mutuncinmu zak kyau,

‘Y/ Amshi: Mu kare mutuncin mu kaz kyau,

: Mu kare mutuncin ƙasarga,

: Noma babbar sana’a rasa ba,

: Kowa yita ya bar rasawa.

 

  Jagora: Kai/ku jama’a Najeriya,

: Talakawa da sarakuna,

: Da ku ma’aikatan gwamnati,

: Alhji Musa Ɗan kwairo,

: Shi ma ya yi horon jama’a kowa,

: Ya kama noma da gaskiya,

: Ni ma Alhaji Musa Ɗankwairo,

: Bayan na aje kotsonnina,

: Na je Sakkwato can gidana,

: Ni ma zan koma gona,

: In kama noma ƙwarai da gaske,

: Ina tara gero, in tara dawa,

‘Y/ Amshi: In nemi abinci na kaina,

: In nemi abinci na kaina.

 

  Jagora: Na kare mutuncin na kaina,

‘Y/ Amshi: Na kare mutuncin kasarga.

: Noma babbar sana’a,

 

  Jagora: Kowa ya tsaya ya yi aiki,

‘Y/ Amshi: Yawon banza ba’ason nai.

: Noma babba sana’a,

 

 Jagora: Da ku ma’aikatan gwanmen,

: Da manya-manyan sarakunanmu,

: Kowa ya bada goyon baya,

: Mu taru mu ceto ƙasar ga.

‘Y/ Amshi: Mutaru mu ceto ƙasar ga,

:Jama’a mu taru mu ceto ƙasar ga.

: Noma babba sana’a,

 

  Jagora: Kowa ya kama aikin daji,

: Kowa naz zan baida aiki,

: Ya zo ya ɗauki fartanya,

: In yay yi hakan ya yi dai-dai.

‘Y/ Amshi: In yay yi hakanga ya yi dai-dai,

: In yay yi hakanga ya yi dai-dai.

 

  Jagora: Kowa naz zan baida aiki,

: Yana yawo ga titi ga banza, 

: Irinsu ka yan sace-sace.

‘Y/ Amshi: Irinsu ka yan sace-sace,

: Noma babbar sana’a,

: Kowa ya yi ta yabar rasawa.

 

  Jagora: Ka taimaki bayinka Allah,

‘Y/ Amshi: Allah kai am mai iyawa.

: Noma babba sana’a.

 

  Jagora: Manyan sojojin Najeriya,

: Sun ce kowa ya koma noma,

: In kun yi hakan kun yi…

‘Y/ Amshi: In kun yi hakan kun yi dai-dai.

 

  Jagora: Manyan ‘yan sanda Nijeriya,

: Kowa ya koma noma Ƙwairo,

: In kun yi hakan kun yi dai-dai.

‘Y/ Amshi: In kun yi hakan kun yi dai dai.

 

  Jagora: Manyan kwastam na Najeriya,

: Kowa ya koma noma Ƙwairo,

: In kun yi hakan kun yi dai-dai.

‘Y/ Amshi: In kun yi hakan kun yi dai-dai.

 

  Jagora: Imagireshin da N.S.O ,

: Kowa ya kama noma nai,

: In kun yi hakan kun yi dai-dai.

‘Y/ Amshi: In kun yi hakan kun yi dai-dai.

 

  Jagora: Sarakunanmu na najeriya,

: Kowa ya kama noma nai Ƙwairo,

‘Y/ Amshi: In kun yi hakan kun yi dai-dai.

 

  Jagora: ‘Yan kasuwa na najeriya,

: Kowa ya kama noma Musa,

‘Y/ Amshi: In kun yi hakan kun yi dai-dai.

: Noma babbar san’a,

 

  Jakora: In kun yi hakan kun yi dai-dai,

: Noma babbar sana’a,

: Sai mun aje gero mun aje dawa,

: Ga masara ga alkama,

: Ga Shinkafa ga masara, 

: Idan abinci ya taru,

‘Y/ Amshi: Sannan darajar naira za ta dawo,

: Sannan darajar naira zata gyaru,

: Noma babbar sana’a.

 

  Jagora: Mun shirya muntara aiki,

: Ga ya nan ya barmu jibje,

: To ku yan najiriya ƙara,

: Mu motsa mu miƙe,

: Mu kare mutuncinmu ya fi.

‘Y/ Amshi: Mu kare mutuncin ƙasarga,

 

  Jagora: Kaɗa da abincin ƙasarmu,

: Mun san mun samu komai,

: Allah ya albarkato ƙasar,

: Najeriya da arziki sai in,

: Mun ƙi yin biɗa in mun miƙe,

: Mun nemi na kanmu,

: Allah za ya taimake mu,

: Kowa kan nemi taimako,

: Gun Allah sai ya yi mai,

: Diba min faɗin Najeriya,

: Ko’ina akwai magurzayye,

: Na gurzar auduga,

: Sannan Najeriya akwai dala ta gyaɗa,

: Sannan akwai dalan auduga,

: To diba yanzu babu ko guda,

: Kama aiki Mu kare mutuncin ƙasarmu,

‘Y/ Amshi: Mu kare mutuncin na kanmu.

 

  Jagora: In mun yi hakan,

‘Y/ Amshi: Mun yi dai-dai,

 

  Jagora: Yawon banza ba a so nai,

‘Y/ Amshi: Yawon banza ba a so nai,

 

  Jagora: Aiki a yi domin Allah,

: Ba na bari domin Allah,

‘Y/ Amshi: In mun yi hakan dai-dai,

 

  Jagora: A kama hanyoyin sana’a,

: Sannan shara’a a kan gaskiya,

: In dai mutum na nashi aiki,

: To ka bar shi da na shi aiki,

: Ke ma ki bari in yi nawa,

‘Y/ Amshi: Ke ma ki bari in yi nawa,

 

  Jagora: Ko’ina ka bari in yi nawa ,

: In mun yi hakan mun yi dai-dai,

: In mun yi hakan mun yi dai-dai,

‘Y/ Amshi: Noma babbar sana’a,

 

  Jagora: Abin da a kyawo garemu,

: Mu daina shawar kayan waɗansu,

: Mu daina shawar kayan waɗansu,

: Mun dinga shawar kayan ƙasarmu,

: In mun hakan.

‘Y/ Amshi: Mun yi dai-dai.

: In mun hakan mun yi dai-dai.

 

  Jagora: Abin da ak kyawo garemu mu daina,

: Shawar kayan waɗansu,

: Mu dinga shawar kayan ƙasarmu,

: In mun yi hakan,

‘Y/ Amshi: Mun yi dai-dai.

 

  Jagora: Jama’a in mun yi hakan.

‘Y/ Amshi: Mun yi dai-dai,

: Noma babbar sana’a.

 

  Jagora: Malam ka ce gyara ka kai,

: Wai kai dan kona da mulki,

: Koko don kana da arziki,

: Ka je ka sawo,

: Kayan ƙasashen waje,

: Don ka sayar, a ƙi sayen,

: Wa gidanka ka/kai kuɗi ka kai su,

: Can waje, kabar gida ba komi,

: To wai kai don ka waye, to shiko,

: Talakawa in sun zo sai ku ce sun yi,

: Laifi sai in kun kare mutuncin ku,

: Sai su ma sun yi ƙi yi,

: Su kare mutuncin ƙasar ga.

‘Y/ Amshi: Su kare mutuncin ƙasar ga.

: Noma babbar sana’a koway yi ta,

: Noma babbar sana’a koway yi ta,

 

  Jagora: Koway yi gyara ya hi ɓanna[1],

: Gwamnati na horon jama’a,

: Kowa ya kama aiki da gaske,

: Kowa naz zan Bai da aiki,

: Wannan ya cuci ƙasa,

: Sannan kuma ya cuci kainai,

‘Y/ Amshi: Sannan kuma ya cuci kainai,

: Noma babbar sana’a,

: Koway yi ta ya bar rasawa.

 

  Jagora: Dan ƙwairo na sha dariya,

: Na iske Bahillace daji,

: Yana ta kiwon Shanu nai,

: An ba shi hurar gero ya sha,

: Dan nan sai yac ce “miyetti”[2],

: Garɗi ne yar ratci kainai,

‘Y/ Amshi: Garɗi ne ya ratci kainai,

: Noma babbar sana’a,

: Kowa yi ta ya bar rasawa.

 

  Jagora: Ka taimaki bayinka Allah.

‘Y/ Amshi: Allah kai am mai iyawa,

: Noma babbas sana’a,

: Koway yi ta ya bar rasawa.



[1]  Shi yana ganin gyara shi ne mutum ya kama aikin gona wato noma, barinsa ɓarna ne.

[2]  Kalma c eta Fulatanci wadda take nufin godiya.

Post a Comment

0 Comments