Ticker

Noma Tushen Arziki

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Noma Tushen Arziki

G/Waƙa: Noma tushen arziki

: A yi noma yaƙin cigaba

Jagora: Noma tushen arziki,

: A yi noma yaƙin cigaba.

 

‘Y/Amshi : Noma tushen arziki,

: A yi noma yaƙin cigaba.x2

 

  Jagora: Yara da mun waƙa in mun gama

: Mu tai arewa mu ja jiki

: Mu kama noma tushen arziki

: Gar kuga waƙa ta aure mu tsaf

: Yara duk waƙar da nake muku

: Ban kamar Shata ba uban Hajo

: Ya riƙe noma tushen arziki

‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

: A yi noma yaƙin cigaba.x2

 

Jagora: Gaisheku

 ‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

: A yi noma yaƙin cigaba.

 

  Jagora: Kai kunga malam Garba Abubakar

: Ɗan Ammani Garba na Huntuwa

: Ya riƙe noma tushen arziki

Y/Amshi: Noma tushen arziki,

: A yi noma yaƙin cigaba.x2

 

  Jagora: A lokacin da aka isko ni a a zariya,

: Baba dan Adaraka Uban Ali Tunda,

: Ka rike noman zamani to ni,

: Mai kiɗanka da ɓotata riƙe.

‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

: A yi noma yaƙin cigaba.x2

 

  Jagora: Kai na fada maku noma zamuyi,

: Wanda bai noma duniya don ko,

: Riƙon aure zai mai wuya.

‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

: A yi noma yaƙin cigaba.x2

 

  Jagora: Masu kiɗa na Shehu ina kira,

: Ku gyara hannu daidai da ku,

: Ku shirya hannu daidai da ku,

: Don kiɗan noma ne za a yi,

: A kama noma tushen arziki.

‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

: A yi noma yaƙin cigaba.x2

 

  Jagora: Masu kiɗana ku sake kiɗa,

: Wannan ganga ta babba ce,

: Wadda ya yi ma Audu Gwamnan Kano,

: Ya zama turabi[1] ya tafi,

: Ya Rabbana gafartan ya Haliƙu.

‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

: A yi noma yaƙin cigaba.x2

 

  Jagora: Kai ku tuna da farko da Najeriya,

: Da tana noman gida mun taba,

: Noman auduga mun yi noman koko,

: Duniya kwana ake tashi ake kullum,

: Sai ga man fetur ya fito,

: To mun rikiɗe mun yad da su,

: Sai ga man fetur ya tafi.

 

‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

: A yi noma yaƙin cigaba.x2

 

  Jagora: Tunda man fetur bana yai ƙasa,

: Mu ɗauki noma kowa yai waje.

‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

: A yi noma yaƙin cigaba.x2

 

  Jagora: Yara dare ya fara ya raba,

: Ina kiɗanku na noman zamani.

‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

: A yi noma yaƙin cigaba.x2

 

  Jagora: Kai kaji waƙa ta tai sama,

: Kiɗan na noma tushen arziki.

‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

: A yi noma yaƙin cigaba.x2

 

  Jagora: Kai ku tuna da Shata Baba Uban Hajo,

: Gonatai tai eka dubu,

: In ya yi waƙar gona zai tafi.

‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

: A yi noma yaƙin[2] cigaba.x2

 

  Jagora: Yara waƙar noman zamani,

: In mun yi noma yau duniya,

: Mun samu kuɗinmu mu adana,

: Ku zo gida mu kasa ukku,

: Kashe ɗaya mu fachanchana,

: Kashi ɗaya banki zamu kai,

: Kashi gudan mu yi noman zamani.

‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

: A yi noma yaƙin cigaba.x2

 

  Jagora: Yara kun ga kuɗi in sun zo,

: Mu riƙe kar mu sanya ido,

: Mu riƙe duka wata rana ba wata,

: Rana ba ce yau bare kuma,

: Wasan damuna in aka labta[3],

: Ruwa mi zamu ci.

‘Y/Amshi: Noma tushen arziki,

: A yi noma yaƙin cigaba.x2

 

  Jagora: Yara ku ƙara kiɗa daidai dani,

: Saboda waƙar noman zamani,



[1]  Mutuwa yake nufi.

[2]  Wata tanyar da ake bi don samun cigaba.

[3]  Yin ruwan sama mai nauyi/yawa.

Post a Comment

0 Comments