Ticker

6/recent/ticker-posts

Kokari Dogo Bajinin Bawa

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Ƙoƙari Dogo Bajinin  Bawa

 

G/Waƙa: Ya ci gazama ,

: Sannu da rana Bajinin  Bawa.

 

Jagora: Wuce maza na Amadu,

: Dogo ka isa an bar ka.

 ‘Y/ Amshi: Ya wuce maza,

: Sannu da rana BajininBawa.

 

 Jagora: Wuce maza na Amadu,x2

 ‘Y/ Amshi: Dogo ka isa an bar ka.x2

: Ya wuce maza,

: Sannu da rana BajininBawa.

 

Jagora: Ko yau da kai da Dango,

‘Y/ Amshi: A yi kallonka cikin daji.

 

 Jagora: Ko yau da kai da Dango,

 

‘Y/ Amshi: A yi kallonka cikin daji.

: Ya ci gazama,

: Sannu da rana Bajinin Bawa.

  Jagora: Na  Bawa in hwaɗa ma,

: Bari noma da ɗiyan rumji,

‘Y/ Amshi: Kas su zo su ɓata ka,

: Da wari da ruwan nama,

  Jagora: Na  Bawa in hwaɗa ma,

: Bari noma da ɗiyan rumji,

‘Y/ Amshi: Kas su zo su ɓata ka,

: Da wari da ruwan nama,

: Ya ci gazama,

: Sannu da rana Bajinin  Bawa.

 

  Jagora: Ko yau da kai da Dango,

‘Y/ Amshi: A yi kallon ku cikin daji.

: Ya ci gazama,

: Sannu da rana Bajinin  Bawa,

 

Jagora: Ƙoƙari ya ci gazama,x2

 ‘Y/ Amshi: Sannu da rana Bajinin  Bawa,

: Ya ci gazama,

: Sannu da rana Bajinin  Bawa,

 

  Jagora: Koko da ni da kai babu giri,

: Babu munahicci,x2

‘Y/ Amshi: Don akwai amanammu,

: Da tsohimmu da tsohinka.x2

: Ya ci gazama,

: Sannu da rana Bajinin  Bawa,

 

Jagora: Wuce maza na Amadu dogo,x2

‘Y/ Amshi: Ka isa an barka.x2

 

  Jagora: Ko yau da kai da Dango,

‘Y/ Amshi: A yi kallonka cikin daji.

 

  Jagora: Ko yau da kai da Dango,

‘Y/ Amshi: A yi kallonka cikin daji.

: Ya ci gazama,

: Sannu da rana Bajinin  Bawa,

Post a Comment

0 Comments