Prof. Khalid Abdullahi Zaria a Ranar Hausa ta Duniya, 2023

    1. Duk Wanda Zai Rubuta Littafin Hausa, Ko Da Tarihin
    ANNABI MUHAMMADU Ne, Ya Tanaji KuÉ—in Bugawa, Don Duk Arewa Ba Mai Tallafa Masa!

    2. Duk Wanda Ya Rungumi Aikin Wallafa Littafan Hausa A Matsayin Sana'ar Da Zai Ɗauki Ɗawainiyar Iyalinsa, Sai Gidansa Ya Fi Ƙarfinsa!

    3. Ba Gwamna, Sanata Ko Minista Daga Arewa Da Ya San Wai Yau Ana Wani Bikin Ranar Hausa, Talakawa Ne Ke Barankadamarsu!

    4. 50-Page-English-Book Maras Ma'ana Wajen Sarakuna Da 'Yan Boko Da Matasan Arewa Ya Fi Littafin Hausa Mai Shafi 500 Komai Ma'anarsa!

    5. Sarakunan Arewa Da Na Haɗu Da Su, Ba Wanda Ya Taɓa Mutunta Littafan Hausa Da Nake Rubutawa, Sai Dai Su Tambaye Ni, Ina Na Turanci?

    6. Ban TaÉ“a Ganin Bahaushe Ya Ƙaddamar Da Littafin Hausa ₦10,000,000 Ba. Na Ga Hausawa 5 Sun Ƙaddamar Da Na Turanci ₦500,000,000.

    7. Yawaita Rubutu A Harshen Hausa Ne Laifin Da Mutum Zai Yi 'Yan Arewa Su Raina Shi Musamman Matasan Da Ke Bibiyar Social Media!

    8. Musulmin Arewa Ne Suka Fi Raina Hausa, Domin Ko Da ƘUR'ANI Aka Fassara Da Hausa A Rubuce, Ba Zai Sa Su Mutunta Marubucin Ba!
    Prof. Khalid Abdullahi Zaria a Ranar Hausa ta Duniya, 2023

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.